Ticker

6/recent/ticker-posts

Farillan Sallah Da Sunnoninta

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Ina so a yi min karin bayani akan farillan Sallah da Sunnoninta da kuma abubuwan da ke ba ta Sallah

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To sudai Farillan-Sallah sun kasune gida-2, akwai Sharuɗɗan-Sallah Sannan kuma akwai Rukunan-Sallah. Kuma akwai Bam-Bamci tsakanin Sharaɗi da kuma Rukuni: Sharaɗi ana samunsa ne kafin ashiga cikin ibada, shi kuma Rukuni ana samunsa ne a cikin ita ibadar kanta, kuma dole sai kowanne yasamu sannan ibada take cika.

SHARUƊƊAN-SALLAH (8)

1. Balaga.

2. Hankali.

3. Muslunci.

4. Tsarkin-Kari.

5. Tsarkin-Dauɗa.

6. Suturce-Al'aura.

7. Shigowar-Lokaci.

8. Fuskantar-Alƙibla.

Kuma gaba ɗayan Malamai sun yi Ijma'i akansu, sai dai Malamai sun yi Saɓani akan cewa Shin Ƙulla-Niyya da kuma Kabbarar-Harama, suma Sharaɗine ko kuma ba Sharaɗi ba ne?

RUKUNAN SALLAH (4)

1. Ruku'i.

2. Sujjada.

3. Tsayuwa.

4. Zaman-Ƙarshe.

Wannan ma gaba ɗayan Malamai sun yi Ijma'i akansu, Sai dai Mazhabin Shafi'yya sunƙara da waɗansu abubuwa kamar haka:

1. Sallama.

2. Tahiyar ƙarshe.

3. Daidaituwa a cikin Rukū'i.

4. Salati ga Annabi ().

5. Zaman da'ake yi tsakanin sujjada.

FARILLAN SALLAH 15

1. Niyya.

2. Rukū'i.

3. Sujjada.

4. Sallama.

5. Nutsuwa.

6. Daidaituwa.

7. Karatun-Fatiha.

8. Tsayuwa dominsa.

9. Kabbarar harama.

10. Tsayuwa dominta.

11. Dagowa daga Rukū'i.

12. Ɗagowa daga Sujjada.

13. Jeranta tsakanin farillai.

14. Ƙulla niyyar koyi da liman.

15. Zaman ƙarshe wanda za a yi sallama a cikinsa.

SUNNONIN SALLAH 8

1. Karatun-Sūra.

2. Ɓoye karatu.

3. Bayyana karatu.

4. Zaman tahiya nafarko.

5. Sami'Allahu liman hamidahu.

6. Ƙarin addu'a azaman tahiya na 2.

7. Kowacce kabbara inbanda tafarko.

8. Sanya sutura agaban mai sallah.

Sai dai kuma Malamai sun yi Saɓani dangane da zaman tahiya, akwai Malaman da suka ce zaman tahiya dukkansa farillane, to amma mafi rinjayen Malamai suntafine akan cewa zaman tahiya nafarko Sunnane, amma zama nabiyu Farillah ne.

ABUBUWAN DA KE ƁATA SALLAH, 11

1. Rashin yin niyya.

2. Warwarewar alwala.

3. Yin dariya a cikin Sallah.

4. Wasa maiyawa a cikin Sallah.

5. Barin wata farilla dagangan.

6. Cin wani abu ko shansa.

7. Yin magana dagangan wacce ba ta shafi sallah ba.

8. Bayyana tsiraici dagangan.

9. Yin amai dagangan.

10. Juyawa alƙibla baya dagangan.

11. Karin raka'a ko sujjada dagangan

ωαηαη sнιηε gωαяgωαdoη ɗαη αвιηdα ιʟιмιη мυ dαкυмα вιηcιкεηмυ үαкαι zυωα gαяεsнι, dαηнαкα ιdαη αηgα ωαηι кυsкυяε αcιкιη αвιηdα мυкα яυвυтα тo αηα'ιүα ғαɗαкαя dαмυ мυgүαяα, тαяεdα кαωo нυננα мαι ƙαяғι.

Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα:↓↓↓

"شـرح الـمـمـتـع" (3/225)

"الموسوعة الفقهية" (12/39)

шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ.

 AMSAWA

 Mυѕтαρнα Uѕмαи

 08032531505

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments