Ticker

6/recent/ticker-posts

Nayi Kokarin Kashe Maciji A Mafarki

TAMBAYA (29)

Assalamu alaikum malam inada tambaya nataba mafarkin maciji amma karami inata kokarin kashe shi amma sai ya gudu nayi mafarkin nan sau biyu sai bayan watanni nasake wani mafarkin Shi ma dai na macijin ne amma wannan yanada girma kuma Shi ma ba baki bane daf dani ina yana kallo na sai na ji tsoro na fara addu'ar kawai sai naga ya ba ce da na farka sai nakunna Suratul bakara tau tun daga lokacin dai ban sake mafarkin ba.

Shi ne nace don Allah me hakan yake nufi. Allah ya kara ilimi mai amfani amin ya hayyu ya qayyum

AMSA

Mafarkin maciji yana nufin: maqiyi, yan bidi'ah, iko, mugun shugaba, mace

Mafarkin maciji na nufin qiyayya tsakanin surukai ko kuma yaya ko kuma gaba tsakanin makota. Idan ka yi mafarkin kana sanye da fatar maciji hakan na nufin zai bayyana qiyayya ga mutane

Kashe maciji da kuma ganin jininsa a hannu na nufin ganin bayan maqiyi. Mafarkin karamin maciji na nufin karamin yaro. Bakin maciji na nufin mugun maqiyi, farin maciji na nufin sassauqan maqiyi. Idan maciji ya hadiye mutum a mafarki na nufin zai samu wani babban matsayi. Fitowar maciji daga rami na nufin samun da namiji. Kashe maciji na nufin aure. Gwazarma da macizan ciki na nufin yan uwa da yayansu. Ganin maciji na cin abinci a teburin mutum na nufin rabuwar abokai. Ganin macizai a sahara na nufin haduwa da yan fashin hanya

SHARHI: Da farko dai dukkan godiya ta tabbata ga Allah SWT wanda cikin ikonSa ya sa baki kara mafarki makamancin hakan ba. Hakan ya farune silar qira'ar can da kika saka na Suratul Baqara wanda daman Abu Hurairah RTA ya karbo hadisi daga Annabi SAW ya ce "Shaidanu ba sa shiga gidan da ake karanta Suratul Baqara"

Sunan Abu Dawud lambata 526

A shawarce ki dinga aiki da wannan hadisin na karatun Suratul Baqara kada ki gaza domin neman kariya daga sharrin mahassada, yan bidi'ah da sauransu

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments