Ticker

6/recent/ticker-posts

Tasbihi Da ‘Yan Yatsu

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mlm ina tmby ne akan yin tasbihi da yan yantsu to mlm ni na kasance ina amfani da charbi duk lokacin da zanyi azkhar na safiya da maraice saboda idan ina yi da hannu sai lissafin yake kwace min shin ya hallata na yi anfani da charbi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To baiwar Allah Abinda ya tabbata a sunnah shine mutum yayi tasbihi da ýan yatsunsa babu shakka lissafa tasbihi da ýan yatsu shine abinda manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yayi umarni dashi a cikin hadisin Yusayrah mahaifiyar Yasir (RA) kamar yadda Abi Dawud ya rawaito a hadisi mai lamba ta 1501.

Kenan idan kina son lissafin tasbihinki ya dace da koyarwar manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da umarninsa to kawai hakuri zakiyi ki lazimci lissafin tasbihi da ýan yatsunki daman ita sunnah sai anyi hakuri an jure ake iya aikata ta. sabida haka ki dinga tattara hankalinki yayin tasbihin, kuma kamar yadda kikace lissafin yana kwace miki to a gaskiya inaga hankalinki ne baya kan tasbihin a lokacin zikirin safiya da yamman domin lissafin tasbihi guda ɗari ba abune me wahala ba. wannan yasa Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace mu dinga lissafin da ýan yatsunmu kuma nasan kema kinyi imani cewa Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) bazai koyar damu aikata duk wani abu me wahala ba domin shi mai tausayine a garemu duk wani abu da zai sa mu takura baya umartanmu dashi, sabida haka inaga zaifi kyau ki dinga tattara hankalinki yayin da kike tasbihin, Amma idan shekarunki sun ja ma'ana girma ya fara cin miki ta yadda har kina iya saurin mance lissafi to kina iya amfani da charbin a babin larura.

Amma kuma shi carbin da kike magana akansa kamar yadda kike tambayar halaccin amfani da shi, Hakika akwai saɓanin malamai game da amfani da carbin yayin lissafa tasbihin. Wani ɓangare na malamai sun karhanta yin amfani da carbin Sabida rashin asalinsa a cikin addini Amma Wasu malaman suna ganin halaccin amfani da carbin abisa sharadin idan har shi mai jan carbin be ɗauki jan carbin a matsayin wani aikin ibada me cin gashin kansa ba to yana iya amfani da carbin. Sabida haka Idan kin ɗauki carbin kawai a matsayin abun lissafin tasbihi ba tare da kin bashi wani matsayi a cikin addini ba, to babu laifi kina iya lissafa tasbihi da shi yayin tasbihin. Amma duk da haka Abinda yafi dacewa a gareki shine ki lassafa tasbihin da ýan yatsunki domin lissafa tasbihi da ýan yatsu shine Abinda ya kasance manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana yi kuma da ýan yatsun yayi mana umarni mu dinga lissafa tasbihin.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Zaku iya samun shafinmu ta wannan hanyar...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments