Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Jinin Haihuwa Idan Ya Dauke Kafin Kwana 40

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum. Malan Dan Allah ya halatta macen da ta haihu kwana biyar Sai jinin ya ɗauke ya halatta tayi wanka tayi sallah ko bai halattaba?

HUKUNCIN JININ HAIHUWA IDAN YA ƊAUKE KAFIN KWANA 40

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

Idan jinin haihuwa (biki) ya ɗauke bayan kwanaki biyar, mace za ta yi wankan tsarki kuma ta cigaba da sallah da azumi kuma Mijinta zai iya saduwa da ita.

A bisa koyarwar addinin Musulunci ba sai ta jira ta cika kwanaki arba'in (40) ba za ta fara sallah. Idan alamomin tsarki sun bayyana ko da kuwa a rana ta farko ne ko ta biyar, wanka ya wajaba a kanta. Idan har jinin ya sake dawowa a cikin kwanaki arba'in ɗin, a lokacin ne za ta sake dainawa ta koma hukuncin mai jego.

Akwai kuskure da mata da yawa ke yi, suna zaton cewa Nifasi dole sai an yi kwana 40. A'a, kwana 40 shi ne Iyaka mafi yawa (Maximum), ba iyaka mafi kankanta ba.

Idan jinin ya ɗauke ko da bayan kwana biyar ne, ko sati biyu, matukar kin ga alamar tsarki (Bushewa ko Farin Ruwa), to kin gama Nifasi. Wanka ya hau kanki, Sallah ta hau kanki, Azumi ya hau kanki. Sai dai idan jinin ya sake dawowa kafin kwana 40 ɗin su cika, to sai ki daina sallah (ki koma hukuncin Nifasi).

Ummu Salama (R.A) ta ce: "Masu biki (Nifasi) sun kasance suna zama kwanaki 40 a zamanin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam)." (Sunan Abu Dawud & Tirmidhi)

Babban Malami Imam Tirmidhi yana cewa bayan ya kawo hadisin: "Masana daga cikin Sahabbai da Tabi'ai sun yi Ijma'i (Haduwa) akan cewa mai biki za ta bar sallah kwana 40 ne, sai dai idan ta ga tsarki kafin nan, to za tayi wanka tayi sallah."

A takaice idan Jini ya dauke kafin kwanakin 40 sai kiyi Wankan tsarki Sannan kiyi Sallah. Idan kuma Jini ya wuce kwanaki 40 sai kiyi Wankan tsarki, kiyi Sallah (ko da jinin bai ɗauke ba, wannan ya zama Istihada/Ciwo).

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Za ku iya samun shafinmu ta wannan hanyar...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments