Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Dole Ne Mace Ta Kwance Kitsonta Domin Yin Wankan Janaba?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam, ina da kitso a kaina kuma gashin yana da yawa, ga shi an daure shi sosai. Shin idan na yi Janaba (bayan saduwa), dole sai na kwance kitson nan duka kafin in yi wanka, ko kuwa zan iya wanka a haka?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

A'a, ba dole ba ne ki kwance kitsonki domin wankan Janaba. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya saukaka wa mata a wannan ɓangaren saboda wahalar da ke cikin yawan kwancewa da daurewa. Abin da ake bukata kawai shi ne ki tabbatar ruwa ya shiga har Gindin Gashin (fatarkai), sannan ki kwarara ruwa a saman kitson.

Ummu Salamah (Allah Ya kara mata yarda) ta tambayi Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) game da wannan matsalar, ta ce: "Ya Manzon Allah! (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ni mace ce mai yawan gashi kuma ina yin kitso (ina daure shi). Shin zan dinga kwance shi idan zan yi wankan Janaba?"

Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce mata:

(لاَ، إِنَّمَا يَكْفِيكِ أَنْ تَحْثِي عَلَى رَأْسِكِ ثَلاَثَ حَثَيَاتٍ ثُمَّ تُفِيضِينَ عَلَيْكِ الْمَاءَ فَتَطْهُرِينَ)

"A'a (kada ki kwance). Ya wadatar a gareki ki kwarara ruwa a kan ki sau uku (tare da tura ruwan a gindin gashin ya yin da kike wankan janaba), sannan ki zuba ruwa a dukkan jikinki, shikenan kin yi tsarki." (Sahih Muslim: 330).

IMAM AN-NAWAWI (Rahimahullah) Yana cewa:

"Wannan hadisin na Ummu Salamah hujja ne karara cewa ba wajibi ba ne mace ta kwance kitsonta domin wankan Janaba... Matukar ruwa ya samu damar shiga har zuwa gindin gashin (fatarkai) da kuma saman kitson." (Duba: Sharh Sahih Muslim)

SHEIKH IBN UTHAYMIN (Rahimahullah) Yana cewa: "A wankan Janaba, ba a shar'anta wa mace ta kwance gashinta ba, saboda yawan maimaituwar Janaba (saduwa tana yawan faruwa), don haka aka saukaka mata. Amma a Wankan Haila (Gama Al'ada), wasu malaman sun ce ya fi kyau ta kwance saboda Haila sau ɗaya take zuwa a wata, kuma ana son tsarkin ya fi karfi." (Duba: Majmu' Fatawa Ibn Uthaymin)

Tunda ba sai kin kwance ba, ga yadda ake yi: Ki debo ruwa a tafin hannunki, ki zuba a kan. Ki yi amfani da yatsunki ki Tura Ruwan sosai har sai kin ji fatar kanki ta jike (wato gindin gashin ya samu ruwa). Ki sake zuba ruwa a saman kitson gaba ɗaya (ba sai kin warware shi don wanke cikinsa ba, matukar ruwa ya bi ta samansa da gindinsa). Sai ki wanke sauran jikinki.

'Yar uwa, wannan sauki ne daga Allah. Kada wahalar kitso ta sa ki dinga gujewa mijinki, ko kuma ki yi wanka shaho-shaho (babu tura ruwa a gindi). Dole ne ruwa ya taɓa fatar kai, amma kitso ba sai an kwance shi ba.

Allah Ya sa mu dace.

(Ku tura wa 'yan uwa mata don su samu sauki a ibadarsu).

WALLAHU A'ALAM

Abdullahi S. Boza ✍️

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Za ku iya samun shafinmu ta wannan hanyar...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments