Daga
Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani
Miji (Mijìi)
Miji wani mutum ne magidanci mai iyali wanda yake da mata ɗaya ko fiye da ɗaya, kuma suna ƙarƙashin ikonsa da mallakarsa. Miji a nan yana nufin duk wani namiji magidanci, wato wanda yake da aure. Yana da bambanci da namiji da aka tattauna a babi na biyu. Namiji ya zo ne a ƙarƙashin bayanin jinsi - ɗaya daga cikin jinsu biyu da suke auren juna (jinsin maza da jinsin mata). A wannan bagire kuwa, ana magana ne game da namiji a matsayin magidanci. A ƙasa an kawo misalan kare-karen magana da suka shafi miji:
1. A haihu, ina miji?
2. Ba haka aka so ba, ƙanen
miji ya fi miji kyau.
3. Ɓalangandi, bikin dangin miji.
4. Gantali, bikin dangin miji.
5. ƙirmisisi, tusa gaban miji.
6. Muna ga Rasulu, ɗiyar boka ta rasa miji.
Mata (Màataa)
Mata wata mace ce mai aure wadda
take a ƙarƙashin
kulawar mijinta tare da bin umurninsa, domin yin ibadar aure. Mata ita ce
abokiyar zaman miji a gidan aure, a cikin zamantakewar aure. Kalmar mata a nan
tana da bambance da kalmar mace da aka tattauna a babi na biyu. Ita mace ta zo
ne a ƙarkashin
bayanin jinsin ma’aurata
bisa al’ada da addinin
Hausawa. Mata kuwa kalma ce da take nufin wadda ta yi aure. A ƙasa an
kawo misalan kare-karen magana da suke ɗauke
da ƙunshiyar
mata:
1. A hana ka mata, a gane ka da
goyo.
2. Ballagaza, matar banza.
3. Ɗaya matar yaro.
4. Kowa yana son mata, sai in
aljihunsa ba wuri.
5. Mata, ba a ba da aron ki.
6. Matar mutum abin zargin sa.
7. Matar mutum kabarinsa.
8. Matar wani ba ta wani ba.
9. Sauna, matar ‘yan ci-rani.
Miji Da Mata (Mijìi Da Màataa)
Miji da mata mutane ne waɗanda zamantakewar aure ta
haɗa su a bisa turba ɗaya, wato zaman aure. Miji
shi ne mai yin kowace irin hidima da lalura ga matarsa domin ɗauke nauyin da ya rataya
bisa kansa a matsayin wanda ya ɗauko
alƙawari
a lokacin ɗaurin aure
tare da kare mata mutuncinta da kuma biya mata buƙatunta gwargwadon hali. A bangaren matar
kuwa, tana bakin ƙoƙari wajen gudanar da ayyukan gida da tarbiyantar da yara.
Zaman miji da mata, zama ne na haƙuri da
kau da kai ga wasu abubuwa da yiwa juna uzuri a tsakanin su, saboda kowa ya ce “zo mu zauna, ya ce zo mu saɓa”. Hausawa na cewa miji da
mata sai Allah. Akwai kare-karen magana da suke ɗauke
da ƙunshiyar
miji da mata sakamakon alaƙarsu. Misalai sun haɗa
da:
1. Boɗaɗuwa,
mata a kan miji
2. Kai ma can, mata ta raina miji
3. Maganin mace, mijinta
4. Munafuki, mijin mace biyu
Manazarta
Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.