Daga
Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani
Ango
Ango shi ne mutumin da ya yi sabon aure kamar yadda aka bayyana a cikin CNHN (2006 sh. 17). Auren da aka ɗaura masa yana iya kasancewa na farko ko na biyu ko na uku ko ma na huɗu. Ko dai yaya abin ya kasance, sunansa ango kasancewar ya yi sabon aure. Kare-karen magana da suke ɗauke da ƙunshiyar ango sun haɗa da:
1. A kwana a tashi, wata rana
jariri ango ne.
2. Abin al’ajabi, ango ya kwana ƙunzugu.
3. Ba laifi, ango ya kwana da
durwa.
4. Da sannu, yaro ango ne.
5. Hamburki, Ango ba ƙoshi.
6. Izgili, angwaye bakin rijiya.
7. Kowa da al’adar garinsa, ango
ya rufe kai da turmi.
8. Sharri takin masoya, inji
sabon ango.
Amarya
Matar da ta yi sabon aure, ita
ake kira amarya. Wannan aure ba dole sai ga budurwa ba. Matar tana iya
kasancewa bazawara. Bugu da ƙari, ba dole ne sai ta je gidan mijin a
matsayin matar farko ba. Tana iya zuwa a matsayin mata ta biyu ko ta uku ko ma
ta huɗu. Da zarar
auren sabo ne, to sunanta amarya. Akwai kare-karen magana masu yawa da suke ɗauke da ƙunshiyar
amarya a cikinsu. Misali:
1. Abin tsana, amarya a bayan
kare.
2. Amarya ba kya laifi, ko kin
karya ɗan masu gida.
3. Amarya in ba ta hau doki ba,
ba za a ɗora mata kaya
ba.
4. Amarya mai daɗin tuwo.
5. Ba laifi, amarya bisa jaki.
6. Ba zama, maye ya yi amarya.
7. Ilin, amarya ta ci ƙanen
miji.
8. Ka ji rabo? Amarya da tsohon
ciki.
9. Ƙauyancin amarya, hawa gado da zani.
10. Kome wayon amarya sai an sha
manta.
11. Kurum baka, amarya ta ci ɗan masu gida.
12. Kwana nawa ne, maye ya yi
amarya.
13. Sabuwar amarya, ba kasafai
takan yi aibu ba.
14. Sai ci, maye ya yi amarya.
15. Samun wuri, amarya da aron
‘yan kunnen uwar miji.
16. Shirun amarya ba tsoro ba,
hankalin mutanen gida take dubi
17. Tun ana marmari, amarya kan
yi goshi.
Ango da Amarya
Kamar yadda idan ka ga wata, za
ka ga Zara, haka ma ango da amarya suke kasancewa a tare bisa mahangar falsafar
al’ada. Wannan ne ya sa aka samu wasu karin magana na Hausa waɗanda suke ɗauke da ƙunshiyar
gambizar ango da amarya. Daga cikinsu akwai:
1. Abin da ke ga amarya, shi take
ba ango.
2. Ango mijin amarya, kada ka sha
mai ya ruɗe ka.
3. Da sanin ango, an yi wa ‘yan
buki duka an karya ƙafar uwar amarya.
4. ƙwalisa, amarya ta ga ango ba riga.
5. Sabo da yi, amarya ta haye
ango.
6. Zagwaɗi, ango shiga ɗakin
amarya.
7. Zaƙin mazallaƙo,
ango da amarya a daren farko.
Manazarta
Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.