Daga
Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani
Surukai jam’i ne na kalmar ‘suruki’ ko ‘suruka’ (siriki da sirika a wani karin harshe). Suruki kuwa yana nufin, mutumin da ya auri ‘yar wani ko mutumin da ya aurar da ‘yarsa ga wani, (CNHN, 2006 sh. 403). Surukai su ne waɗanda suka aurar da ‘yarsu ga wani, ko ta auri ɗansu, surukai sun haɗa da uban ɗiya, uwarta, gwaggwanninta da sauran ‘yan gidansu, haka shi ma mijin iyayansa da yayyensa da sauran yan gidansu.
1. Dakau aikin surukai, in ba za
ka iya ba, ba su ‘yarsu
2. Dalili, mai sa a kama gindin
suruka
3. Hankali ka rabon dawo, har a
manta uwar miji
4. Jirbo aikin surukai, a guda da
kunya, a tsaya a sha wuya
5. Kada ka kula da son suruka,
kai dai yardar matarka
6. Ku taya ni figa, uwar miji ta
zama zakara
7. Mai karɓa surukin mai kyauta
8. Mutuwar sarakuwa, gajarta
tafiya ce
9. Rashin ta faɗi, tusa gidan suruki
10. Sa kai a uku, takabar suruki
11. Samun wuri, amarya da aron
‘yan kunnen uwar miji
12. Tsautsayi, takabar suruki
13. Wasa ya ɓaci, an taɓi kuiɓin sarakuwa
14. Wasa, wasa ne, ban da
tsikarar uwar miji da taɓarya
15. Wuya, mai sa a kwana ɗakin suruka
16. Ya yi auki, uwar miji ta ƙi cin
tuwo
Al’adar Hausawa, dangantaka
tsakanin matar ɗa da
uwar miji wani muhimmin lamari ne kuma babban ɓangare
ne daga cikin zamantakewar aure, sai dai kash! A mafi yawan lokuta mu’amalar su
da cuɗanyar su ba ta
cika yin kyau ba, musamman a wannan zamani da ake zaman doya da manja a
tsakaninsu, saboda suna kallon junansu a matsayin abokan hamayya game da shi
mai gidan, domin wasu dalilai da sukan bijiro a cikin lamuran rayuwar yau da
kullum.
Ga wasu daga cikin karin maganan
Hausa waɗanda suke ƙunshe
da wasu halaye da ɗabi’un
mata da surukansu.
1. Wasa, wasa ne, ban da tsikarar
uwar miji da taɓarya
A al’ada mutum yana wasa ne da
sa’ansa ko abokin wasansa. Wannan karin maganar tana nuna cewa, raini ya fara
shiga tsakanin matar ɗa
da uwar miji inda har ake ba matar shawara cewa ko da za ta yi wasa da ita, to
kar ta wuce wuri. Bisa ga al’ada uwar miji ba abokiyar wasar matar ɗa ba ce. Idan kuwa aka ga
alamun hakan, to ba wasa ba ne, reni ne ya shiga tsakani. Haka kuma, ana nufin
lugudan da ake yi ya yin daka da taɓarya
a turmi wanda yake sautinsa yana tare da wasu maganganu masu ma’ana to idan ana
yin lugudan, ana iya sadarwa tsakanin mai dakan da abokan zamanta kishiyoyi ko
uwar mijin. A nan ana lurar da matar ɗa
cewa, ko za ta yi irin wannan, ta kula cewa uwar miji ba abokiyar wasanta ba
ce.
Ana amfani da wannan karin magana
ne a wurin gargaɗin
mutum da ya tsaya daidai matsayarsa, kar ya wuce wuri ya yi abin da al’ada za
ta zarge shi.
2. Wasa ya ɓaci an taɓi kuiɓin sarakuwa
Wannan karin maganar na nuna irin
yadda raini ya shiga sosai tsakaninsu, har matar ɗa
ta kai ga jikin uwar miji. Ana amfani da ita a nuna cewa mutum ya wuce wuri ya
yi abin da bai dace ba, a mahangar al’ada da zamantakewa.
3. Dalili mai sa a kama gindin
suruka.
Wannan karin maganar tana bayyana
muna cewa, halin jinya ne kaɗai
ke sa suruka ta kama gindin uwar miji, ko lalura ce kawai ke sa mace ta kai ga
jikin suruka, saboda kunya da girmamawa, kamar yanayin jinya da makamantansa.
4. Hankali ka rabon dawo har a
manta da uwar miji
Wannan karin magana tana ɗauke da habaici ko gugar
zana ga matar ɗa wadda
ake ganin saboda tsananin rashin jituwar dake tsakaninta da uwar miji
hankalinta ya rufe ta raba abin da ba ta ba uwar miji ba. AƘamusun
Hausa (CNHN, 2006 sh. 101) an bayyana ‘dawo
da cewa’ dunƙulen
fura.’ Ma’ana dawo na nufin
curarriyar fura. Fura kuwa abin sha ce mai daraja a al’adar Bahaushe.
Ana amfani da ita a yi shaguɓe ga wani mutum da ya bar
wani abu mai muhammanci, ya ɓuge
ga aikata wani abu wanda bai kai muhammancin wancan ba.
5. Ya yi auki, uwar miji ta ƙi cin
tuwo
Wannan karin magana tana nuna
muna zurfin hamayya tsakanin matar ɗa
da uwar miji, ta yadda aka bayyana rashin nuna damuwa game da rashin cin
abincin uwar miji ta yi, da kuma bayyana farin ciki cewa abincin ma ya yi auki
da ba ta ci ba.
A ƙamusun Hausa (CNHN, 2006 sh. 448) an
bayyana ‘tuwo da cewa;
abincin da ake yi da garin dawa ko gero ko masara ko kuma aka yi da shinkafa
aka tuƙa
da tafasasshen ruwa, aka kwashe. Ana ci da miyar kuɓewa ko kuka ko kuma yakuwa da sauransu. Tuwo,
abinci ne mai matuƙar daraja ga al’adar
Bahaushe.
6. Ku taya ni figa, uwar miji ta
zama zakara
Wannan karin magana ya ƙara
bayyana zurfin hamayyar da ke gudana tsakanin matar ɗa da uwar miji, zaman doya da manja tsakanin
uwar miji da surukai, inda aka nuna cewa wani aibu ya sami uwar miji, amma
maimakon matar ɗa ta
tausaya tare da taimaka mata don ganin ta fita cikin mummunan yanayi, sai aka
ji tana neman waɗanda
za su taya ta a iyar da halaka uwar mijin.
Ana amfani da shi wajan nuna cewa
dama ta samu a kan abokin jayayya lokacin da wata musiba ta same shi.
7. Mutuwar sarakuwa gajarta
tafiya ce
Wannan karin magana tana ƙunshe
ne da saƙon
ƙololuwar
kishi da hamayya, inda aka bayyana cewa, ita matar ɗa tana nuna farin cikinta game da mutuwar uwar
mijinta da tunanin cewa, mutuwar za ta sauƙaƙa mata tafiyar da lamuran rayuwar gidan
mijinta.
Ana amfani da ita a nuna cewa
wani da ya ke shiga ƙunci ko damuwa saboda wani abu, ya huta daga ci gaba da zama
cikin wannan yanayi, sanadiyar rabuwa da abin da yake sa masa tarnaƙi.
Karin magana ta taskace muna cewa, a mahangar al’adar Hausawa, tun zamani mai tsawo, ana samun saɓani nan da can tsakanin
mata da uwar miji, sai dai a wannan zamani abun ya fi ɓaci.
Manazarta
Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.