Ticker

6/recent/ticker-posts

Mata a Karin Magana

Daga

Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani

Aure a Kunshiyar Karin Magana

Mata ma sun fito a ƙunshiyar kare-karen magana daban-daban. Wasu daga ciki suna nuni da halayensu na kirki da tasirinsu da muhimmancinsu a cikin alumma. Wasu kuwa suna nuni ne ga raunin da suke da shi. Yayin da aka nazarci ire-iren waɗannan kare-karen magana, za a fahimci abubuwa masu yawa game da yadda Hausawa suke kallon mata, musamman dangane da zamantakewar aure.

1. Mata suna suka tara, amma halinsu ya bambanta

Wannan karin magana tana nuna cewa mata sun yi tarayya ne kawai a wajen suna da ake kiran su da shi, wato mata, amma kowace mace tana da halaye da ɗabi’u daban da na wata mace. A irin wannan lamari, za a sami mata masu suna iri ɗaya waɗanda sun shahara da hali irin na kyautatawa da haƙuri da juriya a zaman aurensu, amma fa za a iya samun wata daga ciki mai irin sunansu ba ta da irin wannan siffa ta su, haka kuma a iya samun ƙabila masu wata siffa mai kyau wadda suka shahara da zaman aure, amma za a iya samun wasu daga cikin su waɗanda suka sha bambam da irin halinsu, irin wannan halayyar za a iya samun su a kowane irin gida, ko ƙabila ko zaman gari, amma kuma a samu bambamcin hali daga matan.

2. Mata haja ne, kowa da tayin da ya karɓe ta

Haja na nufin kayan sayarwa, musamman na tufafi ko kayan ado na mata. Wannan karin magana tana nuna cewa mata abu ne masu daraja da ake yin ado da su, kuma ake mallakar su ta hanyar yarjejeniya da ake ƙullawa, kuma kowace mace tana da ƙimarta daban domin darajojinsu da raayinsu ba daidai yake da juna ba.

3. Ƙarfin mace, sai yawan magana

 Wannan karin maganar tana nuna raunin mace a wajen zamantakewa da kuma husuma, sai dai an halicce su da ɗabi’a ta yawan magana da kaifin harshe, wanda shi ne yake ƙarfafa muradunsu a fagen jayayya, amma ba ƙarfin jiki ba. Wato, ba su cika jure wa aiki mai wahala na tsawon lokaci ba, amma suna iya ɗaukar lokaci mai tsawo suna yawan surutu da mita (jinini) (Yunusa, 1989:103-104). Ga al’ada, akan siffanta mace da raunin jiki da ƙarfi a wajen husuma, amma mai kaifin baki da salo da fasaha wajen kare kanta. Wannan yabo ne a gare ta domin shi zai keɓance ta da siffar jinsin mazaje wato dai, alada ta kalli mata a matsayin sojojin baka a ɗabi’arsu.

4. Kowa ya ci shinkafar mace, tasa ya ci

Wannan karin magana tana magana game da al’adar kula da iyali da Hausawa suka gada kaka da kakanni, inda ake danƙa wa maza haƙƙin ciyarwa. Cewa duk yadda namiji yake ganin yana more wa wasu abubuwa waɗanda mallakin mace ne, a mafi yawan lokuta jiɓin goshinsa ne yake ci ba tare da ya sani ba. Domin kome tsawon lokaci wata macen idan ta bayar da wani abu ga mutum da hannun dama, sai ta dawo daga baya ta amshi fiye da abin da ta bayar da hannun hagu (hauni).

5. Mata zuma ne sai da wuta

Wannan karin magana tana nufin mace fa sai da tsawatawa ake iya zama da ita. Ba a barin ta da tunaninta saboda rauni gare ta. Idan har ana son a more su, to tillas sai an tanƙwasa su. Zuma wani ƙwaro ne mai samar da abin sha mai daɗi, kuma wanda ake haɗa abin sha da abinci da shi daban-daban tare da samar da maganin cututtuka daban-daban da shi. To sai dai shi zuma ba yakan bari a tatsi wannan albarka tasa ba har sai ya ji zafin wuta kuma mai tatsar albarkar sai ya sha harbi. Haka dai wasu matan suke ta fuskar zamantakewa kamar dai yadda zuma yake, ga zaƙi kuma ga harbi.

6. ‘Na gaji’ mai hana wa mata lada

Mata sun shahara ƙwarai a aladar Hausawa wajen hidimar mazajensu da kuma sauran ayyukan gida, sai dai kash! Wata ɗabi’a wadda take ci masu tuwo a ƙwarya, kuma take hana su shan romon hidimar tasu shi ne, gajiyawa da rashin juriyar ɗorewa da hidimar iyali da maigida. Wannan rashin juriyar shi ya sa al’ada ta kalli mace a matsayin wadda za ta fara abu mai kyau a farkon lamari da gasken gaske, amma lokacin da tafiya ta yi tafiya kuma aka kama hanyar cin amfanin abun ko moriyarsa sai ta yi ragwan kaya ta yi kasala ko ma ta yi watsi da shi ta nuna kasawa da gajiyawa. sakamakon haka sai ta rasa cin moriyar shukar da ta yi, domin kuwa kowane lamari ba farkon shi ne mafi mahimanci ko abin lura ba, ƙarshen.

7. Mata in ba ku ba gida[1]

Wannan karin magana, yana nuna muhimmancin mata wajen kula da gida. A al’ada, mata sun keɓanta ga wasu ayukka na gida waɗanda suke da alhakin gudanar da su, kamar kaɗin zare da taɓin auduga da tawai na yara da girki da gyaran gado da sauransu, waɗannan ayukkan ba kasafai za a ga namiji ya zunduma yin su ba sai dai don wata lalura. Ana amfani da wannan karin magana wurin koɗa mata da gwarzanta su.

8. Riƙon gida a bar wa mata

Wannan karin magana kirari ne da ke nuna cewa riƙon gida a bar wa mata, domin su ne jinsin da suka fi taka rawa wajen kimtsin gidan Hausawa da tsaftace shi da kula da tarbiyyar yara da sauran abubuwan da suka shafi yau da kullum na zamantakewar aure.

9. Zaman gida sai mata

Wannan karin maganar tana nuna wata muhimmiyar ɗawainiya wadda mata suke tsayuwa da ita kusan kowace rana, wato hidimar gida da tsaronsa. A al’adar Hausawa da zamantakewar aure, mata su ne mazauna gida da tsaron sa da kula a tsawon yini da kuma wani yanki na dare.

Ana amfani da waɗannan karin magana a wurin nuna cewa, ba fa kowa ke iya yin abin da wani ke iya yi ba a bar kowa da layin da ya fi ƙwarewa ko ya fi iyawa.

Bisa ga al’adar Hausawa, matansu na kulle ne daga jiya zuwa yau. Don haka, maza su ke fita waje wurin nema, mata kuwa su zauna a gida. Ko a zamanin da, maguzawa suke zuwa gona da matansu, sai sun yi abinci suke tafiya, ko kuma idan rana ta yi a tashe su su koma gida domin yin abinci. Ke nan, zama a gida mata suka fi yin sa, su aka sani da shi a tsarin zamantakewar Hausawa.

10. Ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne

Wannan karin maganar yana nuni da cewa, akwai lalurori ko damuwowin mata waɗanda mata ‘yan’uwansu ne kawai za su iya fahimta. Wannan ne ya sa wasu sirrukan suke kasancewa a tsakaninsu kawai, ba tare da maza sun sani ba.

11. Mace wuƙar fawa ce, da yar uwarta ake wasa ta

Wannan karin magana yana nuni da yadda maza suke ɗaukar mataki game da halin rashin kirki da mata suke yi musu ta hanyar wasu matan na daban. Babban misali shi ne ɗaya daga cikin nau’ukan aure da aka yi bayani a babi na ɗaya, wato auren huce takaici. Idan ya kasance namiji ba ya jin daɗin zama da mace, yana iya ƙaro aure domin kawai ita ta gidan ta shiga taitayinta. A irin wannan yanayi, za ka ji ana zance makamancin wannan:

Audu: Wai ka ga yadda uwar gidan Malam Mudi ta koma mutumiyar arziki kamar ba ita ba?

Bala: Ai ta bi hanya tun bayan da ya yi mata amarya a sallar cika-ciki. Ka san mace wuƙar fawa ce, da yar uwarta ake wasa ta.



[1] Akan cike wannan karin maganar da cewa “... in kun yi yawa gida ya ɓaci.”

Manazarta

Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449 

Post a Comment

0 Comments