Daga
Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani
Da yawa daga cikin karin maganar da suka shafi maza, kuma waɗanda suke alaƙa da aure, suna nuni ne game da halayen mazan a zamantakewa. Daga falsafar ƙwanƙwance su, ana iya hasashen cewa mafi yawansu sun fito ne daga bakin mata. Ko da ma dai, masana sun bayyana mata a matsayin waɗanda suke sahun gaba wajen samar da karin magana. A wannan ɓangare na littafin, an kawo wasu karin magana da suka shafi maza, musamman game da gurbinsu a zamantakewar aure.
1. Maza irin gujiya ne, sai an fasa akan san na ƙwarai
Wannan karin magana tana nuni ne da cewa ɗabi’un maza da halayensu ɓoyayyu ne, musamman a tunanin mata. Ba kasafai
ake iya gane su a fahimce su ba; har sai an mu’amalance su sannan za a iya
sanin su. An kwatanta maza da gujiya (gyaɗa) ne wadda ba a cika gane nagartarta ba har sai
an fasa kwasfarta/kwansonta ake gane ruɓaɓɓiya
da mai kyau. An kwatanta halayen namiji da ɗabi’unsa da cewa kamar barkono wanda ba za
a iya sanin zafin yajinsa ba har sai an tauna, haka shi ma namiji yake ta
fuskar halayyarsa, ba za a iya sanin haƙiƙanin yadda yake ba har sai an mu’amalance shi, saboda haka ne aka yi masa
kwatantawar kai tsaye da barkono.
Wannan karin magana yana ɗaya
daga cikin waɗanda
mata suke amfani da shi yayin jajanta wani lamarin kaico da ya faru da wata a
gidan aurenta – wanda kuma ya shafi rashin arziki daga ɓangaren mijin. Misali:
Talatu: Yanzu wa zai yi tunanin Audu zai aikata haka?
Larai: Tab! Ke dai bari! Ai maza irin gujiya ne, sai an fasa akan san na ƙwarai.
2. Namiji zabo ne, ba a shafuwar bayansa
A nan an kwatanta namiji da zabo ne saboda komai kyawun shi ba a iya
matsawa wurinsa don a shafi bayansa, saboda tashi zai yi. A tunanin wannan
karin magana, haka namiji yake. Duk yadda ake ganin sa, ba a sanin halinsa, sai
an zauna da shi. A kan kwatanta namiji da zabo ne saboda wayo. Kama zabo har a
shafa bayansa ba ƙaramin aiki ba ne. Kamar haka ne ake ganin cewa
maza sun fi mata wayo. Sun fu yaudarar su da kalaman soyayya tare da yi musu
wayo a zamantakewar aure.
3. Namiji zakara, ba da ƙwaya ka ci tsakuwa
Wannan karin magana yana nuna matsayin hidimar da namiji yake tsayuwa da
ita a wajen kulawa da ɗaukar
nauyin iyalansa ba tare da damuwa da sai shi ya ji daɗi ba. Dalilin haka ne aka kwatanta shi kai
tsaye da zakara wanda yake ba da ƙwayar abinci mai amfani ga jiki, shi kuma ya ci
tsakuwa wadda ba ta da wani amfani ga jiki. Wasu kuma cewa suke yi ‘Namiji zakara
ne ba da tsaba ka ci tsakuwa', domin ƙara matsayin hidimar da namiji yake
tsayuwa da ita wajen ɗaukar
nauyin iyalansa. Bambancin lafazi ne kawai ake samu tsakanin kalmar ‘ƙwaya’ da ‘tsaba’, amma
ma’ana da saƙonnin
karin- maganan duk ɗaya
ne.
4. Namiji kwaɗo ne mai share tsakar gida
Wannan karin maganar tana nuna yadda hidimar namiji ta game lamuran gida
duka, inda karin maganar ta bayyana cewa yana tsayuwa da ayyukan kyautatawar
gida da mutanen gida gaba ɗayansu.
5. Samnanci, namiji da taron buki
Kalmar samnanci na nufin shashanci ko sakarci da rashin sanin abin da ya
kamata a yi, idan har namiji ya ɓuge da
shirya taron buki ko kuma ya yi kane-kane ya shiga dumu-dumu a lamuran taron
buki. A al’adar Hausawa ana ganin cewa buki na mata ne ba maza ba.
6. Haɓaka, namiji da niƙa
Haɓaka
kalma ce mai nuna faɗaɗa ko ƙaruwa dai dai da kalmar
bunƙasa. Niƙa kuwa, kalmace da take bayyana dabarar sarrafa ƙwayoyin tsaba daga nau’o’in hatsin da sauran dangin kayan abinci ta hanar amfani da dutsi babba mai
faɗi da ƙarami
mulmulalle a mayar da ƙwayoyin zuwa gari domin samar da ire-iren abinci
kamar tuwo da fura da sauransu.
Al’adar Hausawa ta gargajiya, sanannen abu ne cewa, niƙa wani aiki ne da ya keɓanta ga jinsin mata a mafi yawan lokuta,
saboda haka ne, al’adar Hausawa ta taskace wannan al’adar a cikin adabi da
manufar nuna cewa, yana daga cikin bunƙasar sauyawar lamura, da kuma juyawar
zamani kasancewar ba a saba ganin namiji yana niƙa ba.. Ana amfani da
duwatsu (guda biyu) babba da karami a wajen niƙa.
7. Lamari sabo, namiji da surfe
Surfe na nufin daka jiƙaƙƙen hatsi domin a fitar da dusa (CNHN, 2006:403)
shi ma a al’adar
Bahaushe aiki ne na mata ba maza ba. Don haka a mahangar al’ada, sabon lamari ne a ga namiji ya ɗauki taɓarya yana surfa hatsi a cikin turmi.
8. Sabon salo, namiji da gazal
‘Gazal’ wani baƙin fensir ne mai maiƙo da mata kan goga a kan
girarsu yayin yin kwalliya. Kasancewar wannan wani nau’in kwalliya ne na mata,
to da zaran an ga namiji ya yi amfani da ita ba shakka ya zo da wani baƙon abu
a mahangar al’ada.
9. Maigida takobin daga
Wannan kirari ne wanda yake nuni tare da bayyana yadda al’adar Hausawa take kallon namiji magidanci a matsayin wata kariya da garkuwa wanda yake tsaye ƙyam koyaushe wajen ganin ya kare martabar gida ta hanyar aiwatar da hidimomin da suka wajaba garesu, da kuma sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.
Manazarta
Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.