Ticker

6/recent/ticker-posts

Lakabin Sunayen Tsuntsaye Da Bishiyoyi a Sunayen Kanuri (Barebari)

Daga

Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng

Da

Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736

Laƙabi da Sunayen Tsuntsaye

Tsuntsu halitta ce mai rai da ke da ƙafa biyu da fukafukai. Yakan haihu ta hanyar nasa (saka) ƙwai tare da ƙyanƙyashe shi cikin yardar Ubangiji. Su ma tsuntsayen sun kasu kashi biyu, akwai na gida da na daji.

Kamar sauran al’umomi, Kanuri su ma sukan laƙaba wa ‘ya’yansu sunayen tsuntsaye. Daga cikin irin sunayen sukan zaɓo ne daga na tsuntsaye maɗaukaka su laƙaba wa ‘ya’yan nasu. Irin waɗannan sunayen sun haɗa da:

Jad. na 13: Laƙabin Tsuntsaye a Sunayen Kanuri

 

Suna

Ma’ana

1.       

Danga

Shirwa

2.       

Kadau

Shaho

3.       

Kwuui

Kaza

 Laƙabi da Sunayen Bishiya

Bishiya itaciya ce da kan tsiro cikin sarautar Allah, ta girma ko a daji ko a gari. A wasu lokutan kuwa akan dasa su ne. Suna da muhimmanci a rayuwar al’umma, wannan ne ya sa akan yi amfani da sunayensu a laƙaba wa ɗan’adam. Al’ummomi da dama kan yi amfani da sunayen su laƙaba wa ‘ya’yansu, ciki kuwa har da al’ummar Kanuri. Misalai daga ckin irin waɗannan sunaye sun haɗa da:

Jad. na 14: Laƙabin Bishiyoyi a Sunayen Kanuri

 

Suna

Ma’ana

1.       

Tomsu

Tsamiya

2.       

Kawui

Bagaruwa/Gabaruwa

Tushen Bayani: Waziri, (2000 p. 35)

Sunayen Hausawa

Manazarta

Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083

Post a Comment

0 Comments