Ticker

6/recent/ticker-posts

Lakabin Sunayen Abubuwa Da Na Abinci Da Abin Sha a Sunayen Kanuri (Barebari)

Daga

Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng

Da

Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736

Laƙabi da Sunayen Abubuwa

Akwai daskararrun abubuwa da Allah Ya halitta domin amfanin ɗan’adam. Irin waɗannan abubuwa suna da ƙima da daraja ta musamman a tsakanin al’umma. Sakamakon darajar nan tasu ya sa akan samu al’ummomi da dama da sukan laƙaba wa ‘ya’yansu sunayensu. Al’ummar Kanuri suna ɗaya daga cikin al’ummomin da suke sanya wa ‘ya’yansu sunayen irin waɗannan abubuwan. Misalai daga cikinsu sun haɗa da:

Jad. na 15: Laƙabin Abubuwa a Sunayen Kanuri

 

Suna

Ma’ana

1.       

Dinar

Zinariya

2.       

Kau

Dutsi

3.       

Ƙari

DutsinWuya

Tushen Bayani: Waziri, (2000 p. 35)

Laƙabi da Sunayen Abinci ko Abin Sha

Abinci shi ne duk wani abu da ake ci don maganin yunwa ko saboda kwaɗayi ko kuma a dalilin marmari (domin sha’awa a ɗan ƙanƙanin lokaci).

Abin sha shi ne duk wani abu da ake kwankwaɗa mai ruwa-ruwa kamar fura, koko, kunu, da sauransu.

Sakamakon muhimmancin irin waɗannan abubuwa ga rayuwar ɗan’adam ne ya sa al’ummar Kanuri suke yi wa ‘ya’yansu laƙabi da sunayensu. Misalai daga cikinsu su ne:

Jad. na 16: Laƙabin Abinci a Sunayen Kanuri

 

Suna

Ma’ana

1.       

Buri

Abinci

2.       

Kalu

Miya

3.       

Bullum

Kunu

Tushen Bayani: Waziri, (2000 p. 35).

Sunayen Hausawa

Manazarta

Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083

Post a Comment

0 Comments