Ticker

6/recent/ticker-posts

Lakabin Dabi’un Mutum Da Na Siffar Jiki a Sunayen Kanuri (Barebari)

Daga

Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng

Da

Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736

Laƙabi da Ɗabi’un Mutum

Al’ummomi da dama sukan yi wa mutane laƙubba ta la’akari da halayensu ko al’adunsu. Kodayake irin waɗannan laƙubban akan yi wa mutane ne su bayan sun girma. Idan aka naƙalci halayensu sun tashi da su ne tun daga yarinta, hasali ma sun zama sababbin lamura gare su (abubuwan da suka saba da su). Ana kyautata zaton sakamakon haka ne ya wanzar da samuwar irin waɗannan laƙubba a tsakanin al’ummar Kanuri (Barebari). Misalai daga cikinsu sun haɗa da:

Jad. na 17: Laƙabi ta La’akari da Ɗabiun Mutum a Sunayen Kanuri

 

Suna

Ma’ana

1.       

Zau

Jarumi(mai ƙarfin zuciya)

2.       

Kaikai

Mai fitina (fitinanne/mai halin banza)

Tushen Bayani: Waziri, (2000 p. 35)

Laƙabi da Ƙirar Sifar Jiki

Ta wannan haujin, al’ummar Kanuri (Barebari) ba a bar su a baya ba, domin sukan yi wa ‘ya’yansu laƙabi ta la’akari da yanayin ƙirar sifar jikin mai karɓa sunan. Misalai daga cikin irin waɗannan laƙubban sun haɗa da:

Jad. na 18: Laƙabi ta La’akari da Ƙirar Sifar Jiki a Sunayen Kanuri

 

Suna

Ma’ana

1.       

Kime

Ja

2.       

Kori

Gajere

3.       

Sulum

Wankan darza (wankan tarwaɗa)

4.       

Dia

Mai furfura

5.       

Chilluwa

Ɗantsito (ɗan ƙanƙani)

Tushen Bayani: Waziri, (2000 p. 35)

Sunayen Hausawa

Manazarta

Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083

Post a Comment

0 Comments