Daga
Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng
Da
Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
Laƙabi da Abin Mallaka
Haka kuma, al’ummar Barebari sukan yi wa mutum laƙabi da wani abu da ya mallaka ko ya mulka, musamman sarakuna. Irin waɗannan laƙubba suna faruwa ne sakamakon alkunya da sanya jin nauyin faɗar sunan mutum na yanka. Misalai daga cikinsu su ne:
Jad. na 19: Laƙabin Mallaka a Sunayen Kanuri
|
|
Suna |
Ma’ana |
|
1. |
Kali
Ngarmaram |
Mai
farin ingarma[1] |
|
2. |
Dal
Karema |
Mai
doki baƙi[2] |
|
3. |
Baa
Farra |
Mai
doki |
|
4. |
Baa
Fema/Yafea |
Maishanu |
|
5. |
Kaka
Kanyia |
Mai’awaki |
|
6. |
Dunyama |
Maiduniya |
Tushen Bayani: Waziri, (2000 p. 35)
Laƙubban Dangantaka
Su ne laƙubban da ake yi waɗanda ake ayyana nau’in ‘yan’uwantaka ta jini ko ta aure. Hakan yakan sa a sakaya sunan yanka, a dinga faɗar laƙabin
da yake nuna matsayin mai magana
da wanda ake magana
da shi ko a kansa. Al’ummar Kanuri suna amfani da irin waɗannan nau’o’in laƙubba wajen ambaton danginsu
a harkokinsu na yau-da-kullum. Misalansu sun haɗa
da:
Jad. na 20: Laƙabin Dangantaka a Sunayen Kanuri
|
|
Suna |
Ma’ana |
|
1. |
Ba |
Baba
(uba ko mahaifi) |
|
2. |
Bawa |
Baba
(uba ko mahaifi) |
|
3. |
Ya |
Mama
(uwa ko mahaifiya) |
|
4. |
Bakura |
Baban gida (baffa wan mahaifi) |
|
5. |
Baba
Gana/Awana |
Baba ƙarami
(baffa ƙanin mahaifi) |
|
6. |
Yana/Bawa |
Gwaggo
(ya ko ƙanwar mahaifi) |
|
7. |
Rawa |
Kawu
(wa ko ƙanin mahaifiya) |
|
8. |
Yakura |
Inna
(yar mahaifiya) |
|
9. |
Ina |
Inna
(ƙanwar mahaifiya) |
|
10. |
Ya |
Wa ko
ya |
Tushen Bayani: Modu, Muhammada da Bello, (2017 p. 410)
Ta la’akari da waɗannan laƙubban da suka shafi dangantakar jini da auratayya. Za a fahimci cewa, al’ummar Barebari mutane ne masu kunya, wanda hakan ya haifar da kawaici a tsakaninsu ta rashin ambaton ainihin sunayen dangin iyayensu.
[1]Laƙabi ne da ake yi wa shahararriyar sarauniyar Barno mai
suna Aisa.
[2]Laƙabi ne da ake yi wa Yariman Borno
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.