Ticker

6/recent/ticker-posts

Kwaskwarimar Sunayen Musulunci Na Yanka a Sunayen Fulani

Daga

Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng

Da

Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736

Wani salo ne da al’ummomi da dama kan yi amfani da shi ta hanyar yi wa sunan yanka ƙari ko kuma a rage wani sashen kalmarsa ta ainahi. Wato yi wa kalmomin sunan yanka wani gyaran fuska na musamman domin yi musu ƙari ko a gutsure wasu ƙwayoyin sautin kalmar na asali. Irin wannan kan auku ne ta hanyar cire wata ƙwayar sauti daga farkon kalma ko tsakiya ko kuma ƙarshenta. Hakan kan haifar da sauyawar lafazin kalmar na asali. Sakamakon haka ne ke sa ba kowa ne ke iya fahimtar inda aka samo sunan ba, har a riya a zuci, a ɗauka sunan gargajiya ne.

Su ma al’ummar Fulani ba kanwar lasa ba ne ta wannan haujin, don sun yi wa sunayen yanka na Musulunci ‘yan gyare-gyare don su dace da tsarin ginin kalmominsu. Sau da yawa akan yi kwaskwarimar ne domin ɓad da kamar kalmar ta asali. Misalai daga cikinsu sun haɗa da:

Jad. na 42: Kwaskwarimar Sunayen Musulunci a Sunayen Fulani

 

Suna

Kwaskwarima

Tsokaci

1.       

Muhammadu

a.      Hammadu

b.     Hamma

An gutsure ƙwayar sautin mu na farkon kalmar ne. A nan kuwa sai aka gutsure ƙwayar sautin mu da take farkon kalmar tare kuma da shafe sautin ƙwayar du da take ƙarshen kalmar. Wannan ne ya haifar da al’umma ke riya cewa asalinsu sunaye ne na Fulani.

2.       

Abubakar

Bakari

A nan an shafe ƙwayoyin sauti biyu na farkon kalmar, wato A da bu, sai kuma aka yi ƙarin ƙwayar sauti ta wasalin I a gaɓar ƙarshen kalma, wato an yi ɗafa-ƙeya ke nan, wanda ya haifar da samun Bakari

3.       

Abubakar

Buba

A nan an cire gaɓar farkon kalmar sunan wato A

aka kuma shafe gaɓar ƙarshen kalmar wato, kar wannan ne ya sa aka sami Buba saboda gyare-gyaren da aka yi wa kalmar a farko da kuma ƙarshe.

4.       

Abubakar

Kari

A nan, cire gaɓoɓi uku na farkon sunan aka yi, aka bar buɗaɗɗiyar gaɓar ƙarshen sunan, sai aka yi mata ɗafa-ƙeya na wasalin i, ta koma rufaffiyar gaɓa da ake furtawa da “Kari”.

5.       

Usmanu

Manu

A nan an gutsure gaɓar farko ta kalmar watoUs. ”

6.       

Aliyu

Alim

A nan an yanke gaɓar ƙarshen kalmar ne, wato yu, aka yi ƙarin ƙwayar sautin m, sai ta koma Alim

7.       

Maryam

Mayri

A nan an yi musayar gurbi a gaɓar farko, aka ɗauri

sautin m a madadin sautin r, yayin da aka shafe

ƙwayar sautin m.

8.       

A’ishatu

Shatu

A nan share gaɓoɓi biyu na farko aka yi, wato “A”

da “i”suka rinƙa amfani da gaɓoɓi na ƙarshen kalmar, wato Shatu.

9.       

Habiiba

Biiba

An cire gaɓar farko ta kalmar sunan wato “Ha”,

sai ta koma Biiba.

10.   

Asmaa’u

Maa’u

A nan ma, gaɓar farko ta kalmar sunan, wato As aka gutsure, sai sunan ya koma Maa’u

11.   

Husaini

Seyni

Nan ma gaɓar farko ta kalmar sunan ne aka cire, tare da sauya auren wasalin“ai”zuwa wasali ne

da ya ɗauri rabin wasalin y.

Tushen Bayani: Modu, da wasu (2017 p. 416)

Sunayen Hausawa

Manazarta

Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083

Post a Comment

0 Comments