Daga
Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng
Da
Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
Laƙubban Isharar Matsayin Dangantaka
Laƙubba ne da ke fayyace matsayin alaƙar da ke tsakanin rukunin al’umma. Akan fahimci matsayin mutum da ke cikin rukunin iyalansu ta hanyar amfani da wasu keɓaɓɓantun lafuzza a yayin da ake gudanar da hulɗar sadarwa a harkokin yau-da-kulmun. Wannan lamarin abu ne da ya kasance ruwan dare game duniya, da ya shafi kusan kowace al’umma. Al’ummar Fulani na ɗaya daga cikin wadda lamarin ya shafa. Kasancewar suna da irin waɗannan laƙubban da suke amfani da su a yayin gudanar da hulɗar sadarwa da take wanzuwa a tsakanin dangi. Misalai daga ciki sun haɗa da:
Jad. na 39: Sunayen Matsayin Dangantaka na Fulani
|
|
Suna |
Dangantaka |
|
1. |
Baaba |
Uba
(mahaifi)
|
|
2. |
Dada |
Uwa (mahaifiya) |
|
3. |
Bappa |
Wan
ko ƙanen mahaifi |
|
4. |
Goggo |
Yar
ko ƙanwar uba (mahaifi) |
|
5. |
Kaawu |
Wa ko
ƙanen uwa
(mahaifiya) |
|
6. |
Penndo |
Inna
(yar
ko ƙanwar uwa) mahaifiya |
|
7. |
Abba,
Bobbo, Iya |
Wa
(yaya namiji) |
|
8. |
Nenne,
Diddi, Dadda |
Ya
(yaya mace) |
|
9. |
Adda |
‘Yar
fari mace da aka fara haihuwa
a gida |
Tushen Bayani: Modu da wasu, (2017 p. 410).
Yayin da aka duba waɗannan laƙubban
da suka shafi dangantaka
ta jinni da ke nuna matsayin mai magana da wanda ake
magana da shi
ko a kansa. Hakan ya nuna za a
tarar da cewa, mafi yawan al’ummomi na da irin waɗannan laƙubban isharar nau’in zumuntar da take tsakanin mai magana
da wanda ake magana
da shi ko a kansa.
Samar da Laƙubba Daga Sunan Mahaifi ko Kaka
Al’ummar Fulani kan samar da laƙabi daga sunan mahaifi ko kaka namiji. Misali, a al’adar Fulani idan
aka raɗa wa abin haihuwa sunan iyaye ko kakanni maza, akan yi
masa laƙabi da ɗaya daga cikin waɗannan laƙubban:
Jad. na 40: Laƙubba Daga Sunan
Mahaifi ko Kaka
|
|
Suna |
Ma’ana |
|
1. |
Baamanga |
Baba
babba |
|
2. |
Baapeetel |
Baba ƙaramin |
|
3. |
Baaba
Iyaali |
Babangida |
|
4. |
Baaba
‘adda |
Babangida |
|
5. |
Baaba
diddi |
Babangida |
|
6. |
Bappaaji |
Baba
(na sashen uba) |
|
7. |
Goggooji |
Kawu
(wa ko ƙanin uwa) |
|
8. |
Hammaaji |
Wa |
|
9. |
Addaaji |
Ya |
|
10. |
Abbaaji |
Ya |
|
11. |
Baabaaji |
Ya |
Tushen Bayani: Modu da wasu (2017 p. 411)
Laƙubban Sunayen Yanka
Bayan bayyanar Addinin Musulunci
da yadda al’ummar Fulani suka karɓe shi, ya sa
sun yi ƙoƙarin samar
da wasu keɓantattun laƙubba ga sunayen yanka domin girmama masu sunayen na asali. Sukan yi haka ne a sakamakon jin nauyin faɗar sunan ko kuma wasu dalilai na musamman. Misalai daga cikin irin waɗannan sunaye sun haɗa
da:
Jad. na 41: Laƙubban Sunayen Yanka na Fulani
|
|
Suna |
Laƙabi |
Ma’ana |
|
1. |
Muhammadu |
a.
Giɗaɗo b.
Ballo c.
Cuɓaaɗo |
|
|
2. |
Usmanu |
a.
Shehu b.
Biiri |
Malami |
|
3. |
Aliyu |
Garga |
|
|
4. |
Ibrahim |
Jaalo |
|
|
5. |
Nafisatu |
Demmo |
|
|
6. |
Maryam |
Daaso |
|
|
7. |
A’ishatu |
Dikko |
|
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.