Ticker

6/recent/ticker-posts

Kishiya a Madubin Karin Magana

Daga

Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani

Aure a Kunshiyar Karin Magana

Kishiya ita ce ɗaya daga cikin matan da suke auren mutum guda. “Kishiya ba haushi ta goje” mace ce wadda ta auri miji mai mata fiye da ɗaya a ƙarƙashin maigidansu bisa kulawarsa da umurninsa na zamantakewar aure.

Wasu daga cikin karin maganar da suka shafi kishiya sun haɗa da:

1. Aiki inda kishiya ba ya gudu.

2. Allah suturu buƙui, inji kishiyar mai doro.

3. Azarangaɗi, muguwar kishiya.

4. Ba zafi, barkonon taro a idon kishiya.

5. Ban ce a mutu ba, ban ce a warke ba, ciwon kishiya a yi ta lalacewa kan gado.

6. Cin tuwon kishiya, ranko.

7. Da alheri, kishiya ta hau kura da dare.

8. Da alheri, kishiya ta taɓi kishiya da bakin wuta.

9. Da me zan ji, ga mutuwar uwa, an yo min kishiya.

10. Da zaman banza gara aikin kishiya.

11. Dabara ƙafa, inji kishiyar gurguwa.

12. Haka ratata, inji kishiyar mai ‘ya’ya tara.

13. Haka tara, inji kishiyar mai mageduwa.

14. Ikon gwatse, kishiya hana kishiya amsa waƙar miji.

15. Kishin kishiya ba ya hana namiji aure.

16. Kishiya mai ban haushi, ana ganin ki akan zagi miji.

17. Kishiya sai naki, mai gida duba min.

18. Komai daɗinki da kishiya, inji babbar ƙawar amarya

19. Kowa da kiwon da ya karɓe shi, kishiyar mai akuya ta sayi kura.

20. Magana ba mai ƙarewa ba, an sai da akuyar kishiya an sai wa amarya zane.

21. Mai kishiya ba ta mutuwar Allah.

22. Me na iya da abin da ya gagari wuta? inji kishiyar ƙonanniya.

23. Mulkin mallaka, biyan bashi da ɗakin kishiya

24. Na ga abin da ya ishe ni, kishiya tara rana ɗaya

25. Rashin aiki, ta da kishiya daga barci

26. Tallar kai, sata ɗakin kishiya

27. Wada da wadaƙa, ta da kai da kishiya

28. Zama da kishiya tilas ne, ba don dukan su sun so ba

29. Zama da kishiya tilas ne, ba don uwar gida na so ba

30. Zuƙui, doron kishiya

Waɗannan karin magana guda 30, suna magana a kan irin yadda Hausawa suke kallon kishi da kishiya a cikin al’umma.

Manazarta

Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449 

Post a Comment

0 Comments