Daga
Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi
Kuɗin intanet (crypto currency) nau’i ne na kuɗin baɗini ko kuɗin ɓoye wanda ake samu a duniyar intanet. Buhari,3 (2021 p. 1) ya bayyana shi a matsayin “kuɗi da ake amfani da su a cikin kwamfuta wanda za a iya saye da saidawa/sayarwa da su a cikin hanya mai sauƙi.” Wani abin burgewa shi ne, ana iya sayen kuɗin intanet ta amfani da kuɗin zahiri, ana kuma iya sayen su ta amfani da wani nau’in kuɗin intanet na daban. Ƙididdigar Tripple A (2023 p. 1) ta nuna cewa, ya zuwa 2022, kashi goma da ɗigo talatin da huɗu (10.34%) na ‘yan Nijeriya sun mallaki kuɗin intanet.
Binciken Batey, (n.d.) ya tabbatar da cewa, kuɗin
intanet na farko shi ne Bitcoin wanda aka samar tun a shekarar 2008 sannan aka
fara amfani da shi a shekarar 2009. Wanda ya samar da Bitcoin ya bayyana
sunansa a matsayin Satoshi Nakamoto. Sai dai har yanzu ba a san mai wannan
sunan ba. Ba a ma san mutum guda ne ko ƙungiya ce ba.
Ya zuwa yau akwai nau’o’in kuɗaɗen
intanet daban-daban waɗanda kuma kullum suke ƙara yawa saboda sababbi da ake samarwa. Pi yana ɗaya
daga cikin waɗanda suka fi ƙaurin
suna a tsakanin Hausawa, inda har aka samu waƙoƙi[1] da
maganganun malamai da masana daban-daban game da shi. Bayan haka, har fim
sukutum aka yi game da Pi, mai suna ‘Yan Pi Network.
Akwai hanyoyi da dabarun gudanar da
kasuwancin kuɗin intanet masu yawa. Wannan littafin ya kawo guda biyu a
taƙaice. Na farkonsu shi ne trading wanda
a nan aka fassara shi a matsayin cinikayya. Na biyun kuwa shi ne holding,
wanda aka fassara shi da riƙewa.
A – Cinikayya
Shi ne tsarin da ake saye da sayar da
kuɗin intanet nan take domin samun ƙaramar riba. Wannan yana buƙatar lissafi da kyakkyawan hasashe. Mutum zai sayi wani
nau’in kuɗin intanet bayan yin lissafin cewa darajarsa za ta ƙaru bayan ɗan wani lokaci ko ‘yan kwanaki kaɗan,
domin ya sayar ya samu riba. Haka kuma, mutum yana iya saya a wurin ɗan
kasuwa mai sauƙin farashi,
sannan ya sayar wa ɗan kasuwa mai farashin da ya fi inda ya saya domin samun
riba. Bugu da ƙari, ana
iya saya daga wata kasuwar kan intanet mai sauƙin farashi sannan a sayar a wata kasuwa ta daban.
A taƙaice tsarin kasuwancin kuɗin
intanet yana kama da na kasuwancin kayayyaki a duniyar zahiri. Wani abu mai
muhimmanci shi ne, dole ne wanda yake gudanar da irin wannan kasuwanci ya
kasance yana bibiyar bayanai dangane da hadahadar kuɗaɗen
intanet a duniya. Hakan ne zai ba shi damar kauce wa yin hasara.
B – Riƙewa
Shi ne tsarin da mutum zai sayi kuɗin
intanet sannan ya ajiye shi na tsawon lokaci. Ana yin haka ne domin bin babbar
riba. Akan saya a lokacin da ake kira red market (jar kasuwa – wato
lokacin da darajar kuɗaɗen intanet ta faɗi) sannan a
sayar a lokacin da ake kira green market (koriyar kasuwa – wato lokacin
da darajar kuɗaɗen intanet ta tashi).
Daga cikin manyan kafofin hadahadar kuɗaɗen
intanet akwai:
Binance - https://www.binance.com/
Gate - https://www.gate.io/
Crypto - https://crypto.com/
OKX - https://www.okx.com/
KUCOIN - https://www.kucoin.com/
Paxful - https://www.paxful.com
[1] A duba
https://www.amsoshi.com/2021/12/yan-pi-network.html
Manazarta:
Sani, A-U., Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.