Ticker

6/recent/ticker-posts

Yadda Ake Dillanci a Kan Intanet Domin Samun Kudi

Daga

Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi

Damfara a Duniyar Intanet

Akwai manyan kamfanonin kasuwanci a duniya da suke da tsarin dillanci a kan intanet. Hausawa masu yawa suna cin gajiyar wannan tsari. Yana da sigogi daban-daban sannan ana iya samun bambancin sunaye da kamfanoni mabambanta suka yi masa. Duk da haka, a gama-gari an fi kiran sa da suna affiliate marketing, wanda a fassarar kai-tsaye zai kasance “kasuwancin ɗosane,” amma a haƙiƙanin yadda lamuran suke gudana, dillanci ne.

Kamfanoni da suka haɗa da masu sayar da littattafai da na’urori da ababen hawa da tufafi da abinci da sauransu, duk suna ba da damar dillanci. Dillali zai tallata kayan kamfani. Idan aka saya ta dalilin tallar da ya yi, to yana da kaso cikin ribar, wato dai la’ada (royalty). Akwai manyan nau’o’in dillancin kan intanet guda uku kamar haka:

a. Buɗe reshen kasuwanci

b. Ɗora liƙau da samfuran hajoji a kan kafar intanet ɗin dillali

c. Yaɗa liƙau da samfuran hajoji a kafafen sada zumunta

A duba misalai cikin hotunan da aka kawo a ƙasa:

Hoto Na 2.4: Dillanci Ta Hanyar Ɗora Liƙau a Kan Kafar Intanet

Madogara: An ɗauko daga kafar Amsoshi (www.amsoshi.com).

A hoto na 2.4 da aka kawo sama, za a ga misalin yadda aka ɗora liƙau da yake ɓoye cikin hoto a kan kafar intanet wadda ta kasance ta Hausawa. Yayin da masu ziyarar wannan kafa suka bi liƙau ɗin zuwa kafar masu kamfanin (kamfanin da ake yi wa talla) har suka yi hulɗayyar kasuwanci, to masu wannan kafa za su samu kamasho.

Hoto Na 2.5: Dillanci a Kan Kafar Paxful

Madogara: An ɗauko daga https://paxful.com/ha/buy-bitcoin-kiosk

Paxful babbar kafa ce ta hadahadar kasuwancin kuɗin intanet. Ita ma tana da tsarin dillanci. A hoto na 2.5 da aka kawo a sama, an ga yadda Paxful take ba da damar a buɗe abin da ta kira “shago” a kan kafarta. Wato zai zama tamkar wani ƙaramin shago wanda mai shi zai riƙa samun kayayyakin da zai yi dillanci daga asalin babban kantin Paxful. Fassara illahirin shafin zuwa Hausa na ƙara nuni da yadda Hausawa suke cikin wannan harkar dillanci.

Dangane da tura liƙau ta kafafen sada zumunta kuwa, Hausawa da yawa sun samu kuɗaɗe daga dillancin PalmPay da Kuda da Manhajar Abeg da Chipper Cash da makamantansu.

Manazarta: 

Sani, A-U.,  Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307

Post a Comment

0 Comments