Daga
Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi
Talla a kan intanet tana nufin tallata haja ko ra’ayi ko aƙidar wani ko waɗansu domin samun kuɗi. Kusan wannan nau’in talla ba a samun ta a duniyar zahiri – duk da akan samu makamantanta da ake gudanarwa a gidajen talabijin da na rediyo da kuma cikin finafinai. A yau Hausawa da dama sun yi nisa a wannan harkar kasuwanci. Ana gudanar da tallar kan intanet ta fuskoki daban-daban da suka haɗa da:
a. Talla a kafafen intanet (website and blogs)
b. Talla a shafuka da zaurukan kafafen intanet
c. Talla ta hanyar raba liƙau
A - Talla a Kan Kafafen
Intanet (Websites and Blogs)
Duk wanda yake da kafar intanet wadda ta gawurta, yana da damar ɗora tallace-tallace a kai. Tallan yana iya kasancewa ta fuskoki guda biyu, ko dai Adsense ko kuma keɓantattun tallace-tallace. Adsense nau’in
talla ne inda ake rajista da kamfanin Google. Kamfanin na Google ne zai riƙa karɓar tallace-tallace sannan ya ɗora waɗanda suka dace a kafar wanda ya yi
rajistar (ta la’akari da nau’o’in mutanen da suke ziyartar kafar tasa).
Keɓantattun tallace-tallace kuwa su ne waɗanda
ake karɓa daga ɗaiɗaikun mutane ko kamfanoni ko ƙungiyoyi ko gwamnatoci,
da makamantansu. Kai-tsaye akan yi ciniki da yarjejeniyar yadda tallar za ta
kasance (kamar abin da ya shafi farashi, da shafukan da za a ɗora su da tsawon lokacin da za su ɗauka kafin a sauƙe su). A duba misalan da
aka kawo a ƙasa:
Hoto Na 1.6: Talla a
kafar intanet
Madogara: An ɗauko
daga https://www.isyaku.com/search/label/FADAKARWA
A hoto na 1.6 da aka kawo a sama, za a ga yadda aka ɗora talla a kafar Isyaku. Mamallakin
wannan kafa Bahaushe ne ɗan
jahar Kebbi, mai suna Isyaku Garba.
B. Talla a Shafuka Da
Zaurukan Kafafen Intanet
Waɗanda suke da zauruka a kafafen intanet suna da damar da
za su iya amfani da su wajen tallace-tallace. Wannan ya danganta da ƙa’idoji da kuma yanayin amfani da zauren. Bugu da ƙari, ya danganta da yawan adadin mutanen da suke bibiyar
zuren.
Hausawa da dama suna samun kuɗi a
YouTube da Facebook da Instagram da TikTok a dalilin irin wannan nau’in tallar.
Mawaƙan Hausa na zamani da ‘yan barkwanci Hausawa masu yawa suna cin gajiyar
wannan dama. Tuni masu tsara finafinan Hausa ma suka rungumi wannan hanyar
neman kuɗi inda
suke sakin finafinansu a kan YouTube tare da ɗora tallace-tallace domin samun kuɗin shiga. Fitattun finafinan Hausa masu
dogon zango da ake sakewa a kan YouTube sun haɗa da Labarina da Izzar So da
Amaryar TikTok da Asin da Asin da makamantansu.
Daga cikin ‘yan barkwancin Hausa kuwa da suka shahara da kafafen YouTube da
TikTok (waɗanda
suke ɗora
tallace-tallace a kan tashoshi ko shafukansu) akwai Abubakar Sadauki da aka fi
sani da Abis_Fulani. Akwai kuma Mu'azu Muhammad da aka fi sani da Bushkido.
Sannan akwai Ali Muhammad Idris da aka fi sani da Maɗagwal da
sauransu.
C. Talla Ta Hanyar Raba Liƙau
Wannan hanya ce ta neman kuɗi a kan
intanet wadda ta shafi tura saƙonnin talla na wani kamfani a kafafen sada zumunta
ta sigar liƙau.[1] Mai wannan kasuwancin yana ɗaukar liƙau da za a riƙa ba
shi a kowace rana (ko wani lokacin da aka ƙayyade) sannan ya raba a
kafafen sada zumunta irin su Facebook, TikTok, WhatsApp, da sauransu.
Duk da kuɗin da ake samu a ire-iren waɗannan
hanyoyin neman kuɗi, dole ne mutum ya yi takatsantsan gudun faɗa
wa tarkon ‘yan damfara. Fahimtar yadda suke gudanar da shi zai sa a rarrabe
tsakanin aya da tsakuwa, sannan a guje wa yi musu kuɗin
goro gaba ɗaya a matsayin caca ko damfara.
[1] A waɗansu lokuta yakan kasance bidiyo ko hoto.
Manazarta:
Sani, A-U., Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.