'Yan Pi Network

    Waƙa mai taken *Yan Pi Netwok* na ƙunshe da fasaha da barkwanci tare da gargaɗi. Da ma masu hikima sun ce: "Da wasa ake faɗa wa wawa gaskiya." Yana da kyau a lura cewa, sha'irin ba wai yana inkari game da kuɗin intanet ko Pi Network ba ne, yana dai faɗakarwa ne game da yadda matasa ke ƙwallafa rai da ɗora buri da sakankancewa sama da ƙima ga al'amura makamanta wannan.

     'Yan Pi Network
    1.

    Ya ake ciki ne abinmu?
    Ya kuke gayun garinmu?
    Ya batun aure da mota?

    2.

    Ga shi har an cinye rabi,
    Kwanakin aure da hubbi,
    Ba halamun kai sadaki.

    3.

    Ya batun tafiya Amurka?
    A biyo Dubai da Makka?
    A yi Hajji a yo É—awafi?

    4.

    Ya batun auren Baturai?
    Ya batun tafiya ko Turai?
    Tun da nan an kasa seti?

    5.

    Ya batun kyautar karatu?
    Ai Arewa akwai buƙatu,
    Na talauci har da yunwa.

    6.

    Ya batun bene da jirgi?
    Ga shi har an fara zargi,
    Kan fashewa ta Disamba.

    7.

    Kun yi alƙawura gare mu,
    Kuka ce ai za ku sa mu,
    Arziki a watan Disamba.

    8.

    Ga shi kun sa na ci bashi,
    Kun saka na daina dashi,
    Don zatona za ta fashe.

    9.

    Na ciyo bashin mai koko,
    Ga shi A'isha na da anko,
    Zan biya a wata ta sallah.

    10.

    Na yi alƙawura ga Ummu,
    Zana rushe rabin gidanmu,
    Zan gina a watan Disamba.

    11.

    Yanzu wai shin ya ya zan yi?
    Wagga alƙawura da nai yi,
    Ga yawan bashuka gare ni.

    12.

    Rabbana kai ke wa bawa,
    Na tawo ka sakani inuwa,
    Ka raban kwaÉ—ayi da buri.

    13.

    Ka cire mini son na banza,
    Ka saka ni na zama gwaza,
    Gun halak ka raban da buri.

    14.

    Shirya masu jiran ta fashe,
    Sa su zama a kodayaushe,
    Masu ƙwazo da bin halali.

    15.

    Nai salatai gun gwanina,
    ÆŠan Amina abin nufina,
    Shugaban duka mai wafati.

    Haƙƙi mallaka:
    ©Muhammad Bala Garba.

    1 comment:

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.