𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, malam ya kokari, tambayace gare ni, na yi wata biyu ban ga al'ada ba, sai yanzu ta rinka zuwa tana Daukewa, na zo asibiti sun ce juna biyu ne, to in ya zo min da safe shikenan sai ya Ɗauke sai kuma gobe da safe, sai in ya Ɗauke inyi wanka in cigaba da sallah, malam ko ya halatta hakan?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuh.
To yar'uwa wannan
jinin da kika gani mutukar yana kama da jinin hailar da kaki saba gani, to zai
hana sallah, kuma zai Ɗauki dukkan hukunce-hukuncen jinin haila, saboda asali
duk jinin da ya zowa mace ana Ɗaukarsa a jinin haila, in dai ba akwai
wani sababi da zai hana shi ya zama haila ba, kuma babu wani dalili a Alƙur’ani
ko a sunna da zai hana shi ya zama haila.
A zance mafi inganci
mai ciki tana iya yin haila, don haka duk yinin da ki ga jini to yana Ɗaukar hukuncin jinin
haila ne, haka ma tsarki yana Ɗaukar hukunce-hukuncen tsarki, ta
yadda za ki yi wanka duk yinin da ba ki ga jini ba, Saidai idan yana yayyankewa
kusa-kusa, to kina iya jinkirta wankan, sai ki haɗa sallolin da ba ki ga jini ba a
lokutansu kamar azahar da la’asar ko magrib da isha, saboda yin wanka a kowanne
lokaci akwai wahala a ciki, kuma Allah yana cewa:
وَمَا
جَعَلَ عَلَيۡكُمۡ فِى الدِّيۡنِ
"Bai sanya muku
Kunci a cikin addini ba" (Suratu Hajj 78).
Don neman Karin
bayani duba: Almugni na Ibnu Khudaamah 1\214 da Dima’uddabi’iyya shafi na 11.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Zaku iya samun shafinmu ta wannan hanyar...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.