Ticker

6/recent/ticker-posts

Me Ake Nufi Da Janaba?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Dan Allah malam ina tmby. Me ake nufi da janaba? Taya mutum xai gane yanada janaba Sai kuma banbancin maziyyi da maniyyi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To bayin Allah a takaice abinda ake nufi da JANABA shine kasancewa a halin babbar najasa wacce take hana manyan ibadau har sai an gusar da ita ta hanyar wankan tsarki wannan shine ake kira da JANABA a takaice. Sannan kuma JANABA itama ana sanyanta cikin abubuwan da ake kira da Babban kari ko kuma babban hadasi su dangin waɗannan najasar basa tsarkakuwa dole sai ta hanyar wankan tsarki misali kamar samuwar jinin haila ko jinin Nifas/biki wannan duk ana kiransu manyan hadasi.

JANABA tana samuwa ta dayan abuwa guda biyu:

1. JIMA'I TSAKANIN MIJI DA MACE: Matukar an samu saduwa tsakanin miji da mace to janaba ta hau kansu kenan wankan janaba/tsarki ya wajaba akansu.

2. FITAR MANIYYI TA HANYAR MAFARKIN SADUWA KO KUMA FITAR MANIYYI IDO FARKE KAMAR TA HANYAR JIN DADI: Matukar maniyyi ya fita daga jikin namiji ko mace ta waɗannan hanyoyin to janaba ta hau kansu wankan janaba/tsarki ya wajaba akansu. Ta Waɗannan hanyoyin ne mutum zai gane cewa akwai janaba a tare dashi. wato kodai ta hanayar jima'i ko kuma ta hanyar mafarkin saduwa ko kuma ta hanyar fitar da maniyyi ido farke ta hanyar jin dadi.

Dangane da bambancin maniyyi, maziyyi da wadiyyi ga bayanin bambancinsu a takaice kamar haka:

MANIYYIN NAMIJI: Ruwa ne mai kauri fari wanda yake fitowa yayin babbar sha'awa kamar saduwa, ko wasa da farji. Sannan yana tunkudo juna lokacin da yake fitowa, kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino, ko damammen gari, Idan yabushe yana kamshin kwai.

MANIYYIN MACE: Ruwa ne tsinkakke, mai fatsi-fatsi, wani lokacin kuma yana zuwa fari, wanda yake fitowa yayin babbar sha'awa kamar saduwa, ko wasa da farji. Sannan yana tunkudo juna lokacin da yake fitowa, zataji tsananin sha'awa da daɗi lokacin fitowar sa. Kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino ko damammen gari, Idan ya bushe shima yana kamshin kwai. Sannan sha'awarta zata yanke bayan fitowarsa.

HUKUNCIN MANIYYI: Yana wajabta yin wanka. Idan mutum ya ganshi bayan ya tashi daga bacci (ko da bai tuna yin mafarki ba), wanka ya wajaba a kansa. Idan kuma ya fito saboda rashin lafiya ko sanyi (ba tare da sha'awa ba), ba ya wajabta wanka.

MAZIYYI: Ruwa ne tsinkakke dayake fitowa, yayin karamar sha'awa, kamar tunanin aure ko kuma tuna wacce kakeso, ko matarka, ko kallon matar ko namijin da kike sha'awa. Haka kuma yana fitowa yayin wasa tsakanin miji da mata, saidai shi baya tafiyar da sha'awa, kuma wani lokacin ba'a sanin ya fito. Malamai suna cewa: Maziyyi yafi fitowa mata, fiye da maza.

HUKUNCIN MAZIYYI: shi ne mutum zai wanke azakari ko farjinsa da duk inda ruwan ya taɓa a jiki ko tufa, sannan a sake alwala idan za a yi sallah. Baya halatta ayi sallah da tufifin da maziyyi ya taɓa har sai an gusar dashi ta hanyar yayyafa ruwa ko wankewa. Amma fitarsa baya wajabta wanka.

WADIYYI: Wani ruwa ne mai kauri da yake fitowa a karshen fitsari, ko kuma karshen bahaya ga wanda yajima baiyi jima'i ba, yana fitowa ga waɗanda basuda aure, ko waɗanda sukayi nisa da abokin rayuwarsu ta aure, ina nufin namiji ko mace.

HUKUNCIN WADIYYI: Yana ɗaukar hukunci irin na fitsari. Najasa ne kuma yana karya alwala. Mutum zai wanke gaban muddin ya fito, ya wanke inda ya taɓa, sannan ya yi alwala idan zaiyi sallah.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Zaku iya samun shafinmu ta wannan hanyar...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments