Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Fidda'u (Saukewa Mamaci Alkur'ani)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Wai Malam Meye Hukuncin Saukewa Mamaci Al-ƙur'ani bayan ya mutu?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalamu To malamai sun yi saɓani akan wannan mas'ala zuwa maganganu guda uku:

1. Bai halatta ba, saboda ba'a samu wani nassi da yake nuni zuwa haka ba, kuma ita ibada ba'a yinta sai da nassi na musamman, Allah Yana cewa:

وَاَنۡ لَّيۡسَ لِلۡاِنۡسَانِ اِلَّا مَا سَعٰىۙ‏

Kuma mutum bã shi da kõme fãce abin da ya aikata. (An-Najm, Ayat: 39).

Mutum ba shi da wani abu sai aikinsa, kamar yadda wannan aya take nuni zuwa haka, tun da ba'a samu ba, yin hakan zai zama bidi'a, wannan ita ce Shafi'i.

2. Ya halatta a yi, saboda hadisan da suke nuna cewa mamacin yana iya amfana da abin da mai rai zai masa, kamar hadisan da suka yi umarni da yi masa sallah da nema masa gafara bayan ya mutu, da yi masa sadaka, wannan shi ne maganar mafi yawan malamai, har wasu marubuta ma sun hakaito ijma'i akan haka, saboda mutane sun jima suna yi kuma malamai ba su yi musu inkari ba.

3. Akwai wadanda suka tafi akan cewa idan ɗansa na cikinsa ya yi masa, to ladan zai same shi, amma wanda ba ɗansa ba, ba zai yi masa ba, saboda faɗin Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) "Ɗan mutum yana daga cikin aikinsa" Abudawud ya rawaito shi kuma Albani ya inganta shi a sahihu sunani-Abi-Dawud hadisi mai lamba ta: 2528.

Sai dai wasu malaman, suna rinjayar da magana ta uku, saboda faɗin Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) : "Idan ɗan-adam ya rasu ayyukansa sukan yanke sai dayan abubuwa guda uku: sadaka mai gudana, ko ilimin da ake amfana da shi, ko ɗa nagari da yake masa addu'a" kamar yadda Tirmizi ya rawaito shi kuma ya inganta shi a hadisi mai lamba ta:1376.

Wadancan hadisan kuwa da masu Magana ta biyu suka kafa hujja da su, to za a yi amfani da su ne a iya inda suka zo, amma ba za a yi kiyasin karatun ƙur'ani akan su ba.

Don neman Karin bayani, a duba Majmu'ul fataawa:24\366 da Nailul Audaar 4\112 da Ahakamul jana'iz shafi na: 171.

Allah ne ma fi sani.

Amsawa: DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Zaku iya samun shafinmu ta wannan hanyar...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments