Ticker

6/recent/ticker-posts

Hoton Mummunar Zamantakewar Ma’aurata a Karin Magana

Daga

Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani

Aure a Kunshiyar Karin Magana

Kamar dai yadda aka samu karin magana masu nuna kyakkyawar zamantakewa, haka kuma akwai jerin karin magana waɗanda suke nuna mummunar zamantakewa tsakanin ma’aurata. Ga wasu daga cikinsu.

1. Ruwa ba ya tsami banza

Wannan karin magana ce da ta kasance gama-gari. Duk da haka, ana amfani da ita a bagiren aure. Asalin ruwa abin sha ne wanda ɗanɗanonsa yake da daɗi na musamman wanda ya bambanta da duk wani ɗanɗano. Saboda haka, da zaran aka ji ɗanɗanonsa ya canja zuwa mai tsami ko ɗaci, to ba shakka ya gauraya da wani abu. Wannan karin magana tana nuna cewa asalin zamantakewar mutane zamantakewa ce kyakkyawa, duk lokacin da aka ga wani canji, ba banza ta kawo shi ba.

2. Ƙeta mai ɓata zama

Kalmar ‘ƙeta’ na nufin, mugunta ko zalunci (CNHN, 2006 sh. 280). Wannan karin magana tana nuna cewa babbar matsalar da ke kawo taɓarɓarewar kyakkyawan zamantakewa ita ce, matsalar mugunta da zaluntar juna. Maganin matsalar kuwa shi ne, kyautatawa da yi wa juna adalci a duk harkokin yau da kullum. Domin kuwa ita rayuwa tana son mai kyautata mata, haka kuma tana ƙin mai munana ko muzguna mata. Matuƙar ana son ɗorewar kyakkyawan zamantakewa dole ne a samu daidaito, domin ita rayuwar duniya tana ginuwa ne a kan tubalin ba ni gishiri in ba ka manda.

3. Mun gaji da kyau, hali muke nema

Da kyau da hali abubuwa ne guda biyu waɗanda abokan zama suke buƙatar su ga juna, amma duk lokacin da hali ya munana, yakan ɓoye kyawun mai shi. Maza ne suka fi amfani da wannan karin maganar, idan matansu suka yi masu wani mummunan abu ta fuskar zamantakewa domin su nuna ɓacin ransu ga halayen macen, da kuma yin tir da kyakkyawar mace da ta rasa kyakkyawar ɗabi’a ko hali.

4. Mata! Mance su yi ma gayya

Kalmar ‘gayya’ na nufin ‘yin abu da gangan da niyyar ramuwa (CNHN, 2006:163). Wannan karin magana tana nuna cewa idan aka cutar da mata a zamantakewa ba kasafai suke aiwatar da ramuwa nan take ba, a mafi yawan lokuta sukan bari ne sai kura ta kwanta ko kuma har sai wanda ya munana masu ya manta sannan su yi shiri su mayar masa da martani idan ba su yafe ba. Kasancewar mata sun yi tarayyar wasu ɗabi’u da ƙananan yara da ma dabbobi, saboda haka, duk wanda ya samu kanshi a matsayin jagoransu, to sai ya yi tsayuwar daka wajen kwaɓa da lura da lamuransu, domin kuwa shi tamkar makiyayi ne, duk lokacin da ya yi sake da kulawa da su, to suna iya aiwatar da wata ɓarna wadda bai yi tsamanni ba, sanadiyar rashin kulawarsa ta a kai a kai.

Manazarta

Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449 

Post a Comment

0 Comments