Ticker

6/recent/ticker-posts

Hoton Kishi a Karin Magana

Daga

Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani

Aure a Kunshiyar Karin Magana

Kamar yadda bayani ya gabata, wani lokaci miji yakan ƙaro wa mata abokiyar zama (kishiya) wanda a alada da mafi rinjayen addinin Hausawa, kishiya takan kasance daga ɗaya zuwa biyu har zuwa uku, watau mata huɗu ke nan. Kishi wani abu ne da yake a zuciya, watau ɗabi’a ce wadda kusan babu wanda bai da shi, sai dai kishin na wani ya sha bamban da na wani. An fi samun kishi a tsakanin mata, misali ta wajen auratayya, kamar in namiji ya auri mata biyu ko uku zuwa huɗu, to dole ne za a samu kishi tsakaninsu na jin ƙyashi da kuma tserereniya da juna wajen ɗauke hankali da jawo ra’ayin miji. Wani kishin yana da tsafta domin ba a faɗa, wani kuma kishin yakan yi muni, kamar yadda Muhammad (2020 sh. 139) ya bayyana.

Bugu da ƙari, bisa al’ada, iyalin Hausawa ba kurum sun ƙunshi matansa da ‘ya’yansa ba ne. A bayanin Malumfashi (2000 sh. 64), sun haɗa da har ma duk wani wanda yake a ƙarƙashin ikonsa ko kulawar sa, ko sun haɗa dangantaka ta jini kamar ‘yan’uwansa, ko kuma ba su haɗa ba, kamar agola da sauran yaran gida, kasancewar tsarin iyalin Hausawa tsari ne mai yaɗo.

Wannan binciken ya yi yunƙurin nazari da kuma tattauna yanayin kishi da ke gudana tsakanin mazauna gidan Hausawa, ta hanyar amfani da wasu karin magana masu saƙon kishi a cikinsu.

Kishi Tsakanin Kishiyoyi a Karin Magana

Zama tsakanin mace da kishiyarta waɗanda ake kira abokan zaman aure ko kuma kishiyoyi a al’adar Hausawa, zama ne wanda yake cike da hamayya da ƙyashi da saɓani da rashin jituwa, saboda mafi yawan mutane suna da ra’ayin cewa, kishi shi ne gishirin zaman mata fiye da ɗaya a rayuwar gidan aure. Wannan shi ne abin da ya ke gudana a bakunan Hausawa kaka da kakanni.

A ƙamusun Hausa (CNHN, 2006 sh. 247), an bayyana ma’anar kishi da cewa: 'Rashin jituwa da nuna ƙyashi irin wanda matan da ke auren mutum ɗaya ke yi wa juna”. Aka kuma bayyana ‘kishiya’ da cewa 'ɗaya daga cikin matan da suke auren mutum guda’.

A ra’ayi wannan littafi, kishi wani abu ne da yake a zuciya, kuma kusan babu wanda bai da shi, sai dai kuma na wani ya sha bamban da wani. An fi samun nuna kishi ga mata. Misali ta wajen auratayya, kamar in namiji ya auri mata biyu ko uku ko huɗu, to dole ne za a samu kishi a tsakaninsu, Kodayake akan yi kishi mai tsafta, wanda ba a faɗa, sai dai yin tsere da juyayya wajen kyautata wa miji. Wani kishi kuwa ba shi da kyau, domin ban da fitina da tsokana da faɗace-faɗace da tashin hankali da hana miji zama lafiya, babu abin da ke cikinsa na madalla ko sambarka. Don haka ne ake yi wa kishiya kirari da cewar; kishiya ba haushi” watau, ga al’adar Bahaushe, kishiya na jin haushin kishiyarta. Dalilin kishin ne masana da dama suka bayyana cewa, ɗabi’ar ‘yan ubanci ta samo tushe ne, watau daga kishin da yake gudana tsakanin kishiya da kishiya.

Bisa taƙaitawa ga abin da ya gabata, a nan, kishi na nufin nuna ƙyashi a kan wani saboda wani abu da ya mallaka ko ake tarayya a kansa ko kuma wata dama ta ɗaukakar rayuwa da ya samu. Hausawa suna amfani da kalmar kishi a wurare da dama cikin karin maganansu don nuna irin yadda kalmar take da muhimmanci da tasiri ga rayuwar Hausawa musamman mata, da irin yadda wannan kalmar ta kishi ta jawo wani ɓangare na wasu karin magana da suka shafi kishiya da uwar kishiya da ‘ya’yan kishiya har da uwar miji, kamar yadda Koko (2011 sh. 25) ta zayyana.

A wannan gaɓar, an yi nazarin mace da halayyarta da yanayin ɗabi’arta da ayyukanta a matsayinta na kishiya ta hanyar amfani da wasu jerin karin magana. Wannan nazarin ya yi dubi ne ga yadda al’ummar Hausawa suka bayyana ra’ayinsu game da halayen kishiya masu kyau da maras kyau kamar haka:

1. Mai koda ba ta son mai koda

Wannan karin magana tana nuna muna cewa irin yadda mutum ba ya son abokin gogayya ko jayayya ko hamayya a fagen aikinsa ko sana’arsa ko fasaharsa, saboda ɗabi’ar kishi da aka halitta shi a kanta. A ɗabi’ar mutum yana son ya yi fice ko shahara a wani fage na baiwa ko wata hikima ko ma wani abu, kuma ba ya son wani ya yi tarayya da shi a wannan baiwar, musamman kafaɗa da kafaɗa, face ya nuna rashin jin daɗinsa ga wannan mutum, har ma tana iya kai ga ya ɗaura ɗamarar yaƙar sa ta hanyar kawar da shi domin kuwa yana kallonsa ne a matsayin abokin gaba, haka ma kishiya take ganin cewa ‘yar uwarta kishiyar ta zamar mata tarnaƙi a gidan mijinta.

A Ƙamusun Hausa (CNHN, 2005 sh. 248) an bayyana kalmar ‘koda’ da cewa ‘sana’ar dakau ko niƙau, daidai da aikatau’. Saboda haka, kusan kowa ba ya son kishiya, amma kishin mata shi ne ya fi fitowa a fili.

Ana amfani da wannan karin magana a bayyana cewa mutum ba ya son kishiya a cikin lamuransa na yau da kullum. Ga al’ada, me ya sa mata suke da yawan kishi? Amsar ita ce:

2. Kishi kumallon mata, in ya motsa sai an haras

Wannan karin magana tana bayyana cewa, mata ba su iya ɓoye rashin son su ga haɗa miji da wata mace, komai kirkinta da halin nagartarta. Duk lokacin da kishi ya motsa tsakanin kishiyoyi sukan koma kamar mahaukata, su yi ta yin abin da bai dace ba. Sau da yawa sukan sami sauƙin zafin kishi idan sun yi amfani da jefa wa junansu kare-karen magana (Usman, 2005 sh. 120).

Kishi yakan dami waɗansu mata ainun. To, amma suna yin ƙoƙari suna ɓoye shi suna nuna kamar bai dame su ba, su mai da komai ba komai ba ne, sai ranar da wutar kishin ta ruru, sai gida ya kacame, da rigingimu, maigida ya kasa tsaye ya kasa zaune ganin wutar rikicin ta mutu. (Yunusa, 1989 sh. 22).

A ƙamusun Hausa (CNHN, 2006 sh. 252) an bayyana kalmar ‘kumallo da amai mai launin rawaya wanda akan yi don rashin lafiya ko rashin cin abinci da safe’. Haka kuma, an bayyana kalmar ‘haras’ da; amaye abin da aka ci ko aka sha’. Daga waɗannan bayanai an fahimci cewa, kishi wata ɗabi’a ce ta halitta wadda idan wata damuwa ta shige ta ko ta rasa cimma wani guri na rayuwa dole ɗabi’ar sai ta bayyana a fili kowa ya gane ta kuma ya ji ta. Al’ada ta gudana a kan cewa mace ba ta maraba da auren kishiya, saboda ire-iren waɗannan karin magana:

3. Zama da kishiya tilas ne, ba don uwar gida na so ba

Hausawa suna da al’adar auren mace fiye da ɗaya, tun kafin zuwan addinin Musulunci. Karin maganar tana bayyana irin yadda matar farko (uwargida) take ƙyamar shigowar wata mace a gidan aurenta a matsayin kishiyarta wadda za su riƙa yin kafaɗa da kafaɗa da ita wajen mu’amala da miji (Usman, 2005 sh. 121-122).

Fahimtar wannan littafin ya fi karkata ne ga karin maganar da ke cewa; zama da kishiya tilas ne, ba don dukansu (uwargida da amarya) suna so ba. Wannan shi ya fi zama daidai da ɗabi’ar mata, domin kuwa kamar yadda uwar gida ba ta son amarya ta shigo mata, haka ita ma amarya ba ta ƙaunar ta isko uwargida. Dukkansu ba mai son ya haɗa miji da wani, kasancewar ba su da tabbacin irin zamantakewar da za su yi da junansu a wajen mu’amalantar miji. Miji shi ne babban jigo wanda ake kishi kansa, saboda kuwa, su mata waɗanda suke kallon kansu a matsayin kishiyoyin juna, kishin su ya ginu ne sanadiyar tarayya da musayar mu’amala irin ta zamantakewa da suke yi da wannan miji a tsakanin su, hakan yana zame masu wata babbar damuwa da kowacen su take ganin cewa bai dace ba ta zama tana da abokan tarayya wajen hulɗar ta da miji, kuma take fatar cewa ina ma ace ita kaɗai ce mata a gare shi.

4. Kishin kishiya ba ya hana namiji aure

Wannan karin magana tana nuna cewa duk tsananin kishin nan na mata da aka bayyana, ba ya hana miji ƙara aure, matuƙar ya ƙudurci hakan. Da mata za su iya, da sun daina wannan kishi, amma ina! Ba za su iya ba kasancewarsa ɗabi’a ce wadda aka halitta su da ita, kuma ta gauraya da jini tare da tsokar jikinsu, kamar yadda za a ga tasirin kishi a ƙunshiyar jerin karin maganan Hausa kamar haka.

5. Mai kishiya ba ta mutuwar Allah

Wannan karin magana tana nuna irin yadda kishi yake cike da zargi tun daga rayuwar zaman aure har zuwa mutuwar ɗayansu. Karin Maganar ta taskace wata al’ada wadda take bayyana cewa duk wani abu maras kyau da ya samu mace mai kishiya, akan danganta shi ga kishiya, ko da rashin lafiya kishiya ta yi ta mutu, sai ka ji ana ƙoƙarin danganta mutuwar da wani aikin da kishiyarta ta yi a kanta. Hausawa suna da wannan tunani ne, saboda tsananin ƙiyayya da yawan zargi da ke tsakanin kishiyoyi, da kuma sanin halin da mata ke iya aikatawa ga kishiya.

6. Na shiga zunɗe, kishi da maras hankali

Wannan karin magana tana nuna irin tasirin da kishi ya yi a wajen zamantakewar matan aure da rashin ƙaunar kishiya, inda aka ga cewa duk da maras hankali, watau mahaukaciya idan miji ya auro ta a matsayin kishiya, babu wani sassauci da za ta samu ga wadda ta isko a gidan, domin kuwa ita ma za a fafata da ita a fagen kishi.

Ana amfani da karin maganar ne domin yin shaguɓe ga kishiya ko kuma tsokanar faɗa.

7. Zugurnugu![1] Kishi da masu iyaye

Idan aka yi dubi da tsanaki ga ma’anar wannan kalma ta ‘zugurnugu’ sannan aka yi nazarinta da kyau, za a fahimci cewa; mata suna tsoro ko fargaba da yin kishi da masu iyaye, kasancewar masu iyaye iyayensu za su riƙa ba su gudunmawa da kuma wani taimako da suke buƙata wajen ƙara masu ƙarfi da nau’o’in kayan faɗan da za su ci gaba da yaƙar kishiyarsu ta kowane hali.

8. Kishiya mai ban haushi, ana ganin ki akan zagi miji!

Duk da yake mata suna ƙyashi kuma suna ƙyamar kishiya, amma ba yadda suka iya. Dole ne uwargida ta miƙa wuya ga hakan, idan har aka yo mata kishiya. Wasu lokutan miji yakan auro kishiya ne domin kawai ya muzguna wa uwargida, saboda haka ake jin haushin ta sosai, kuma kusan duk lokacin da aka haɗu da ita ko aka gan ta, hakan yakan haifar da a zagi miji saboda haushin da take ba abokiyar zamanta. (Usman, 2005 sh. 121).

Ga al’ada irin ta kishi tsakanin kishiyoyi, duk yanayin da aka ga kishiya a cikin sa, akan danganta shige shi ne sanadiyar mijinta, hakan kuwa yakan faru ne, saboda yawan zargi da ƙyashi da ke tsakanin su, don haka idan kishiya ta ga kishiya tana cikin farin ciki hakan yana iya zama dalilin zagin miji ko kuma ta ga ta sami wani cigaba ga rayuwa ta hanya daban-daban, wannan ma yana kawo zagi ga miji.

9. Da me zan ji? Ga mutuwar uwa an yo min kishiya

Wannan karin magana ya daidaita tsakanin raɗaɗin shigowar kishiya gida da raɗaɗin da ake ji idan uwa ta mutu. A nan, mace tana juyayin cewa cikin matsalolin biyu wace matsala ta fi ɗaci? Da a ce uwar tana raye da za ta taimaka wajen sauƙaƙa damuwar da yarta za ta shiga lokacin shagulgulan bikin kishiyarta. Uwar za ta ba da shawara, kuma ta ɗora ta a kan hanyar da ta dace, amma ga shi uwar ba ta nan, hakan ya haifar da katafaren giɓi. Babu yadda za ta yi ban da ta amince da abin da al’umma ta tasirantu da shi na auren mata fiye da ɗaya (Usman, 2005:122-123). Ana amfani da wannan karin magana ne a lokacin da aka shiga halin tsaka mai wuya.

 Wannan karin magana, mace ce take juyayi tare da nuna damuwarta a kan rasa wani ginshiƙi, kuma tudun dafawa a gareta, a wurin cimma wasu buƙatocinta na rayuwa, kuma kwatsam sai ga shi a lokacin ɗaya wani abu da take ganin matsala ce babba da kuma barazana ga rayuwarta ya same ta a rana ɗaya, a kan haka ne take nazarin auna waɗannan musibu guda biyu da suka same ta da cewa shin wai da wane za ta ji, domin ana kukan targaɗe sai ga karaya ta zo.

10. Na ga abin da ya ishe ni, kishiya tara rana ɗaya

Wannan karin maganar ta fitar muna fili, ɓaro-ɓaro a bayyane yadda mata suke tsananin ƙin shigowar kishiya a gida, musamman idan kishiyoyi suka yawaita rigingimu da rikita-rikita za su yawaita kasancewar kishi yakan fi tsananta gwargwadon yawan kishiyoyin da suke tarayya ga miji ɗaya. Ba mamaki wannan karin magana tun na lokacin Maguzanci ne domin Hausawa, ba sa wuce auren mata huɗu, a lokaci guda, kasancewar addinin Musulunci ya haɗiye kaso mai yawa na al’adarsu. Saboda haka, cewar da aka yi kishiya tara, an yi amfani da salon kambamawa ne kawai, ga kishiyar da take tsananin tsoron sharrinta.

Ana amfani da wannan karin magana idan ana son a bayyana cewa wasu abubuwa marasa daɗi sun afka wa mutum a lokaci ɗaya.

11. Azarangaɗi, muguwar kishiya

Wannan yana daga cikin karin maganan da ake ginawa tare da amfani da wasu kalmomi waɗanda ba a tantance ma’anarsu ba a Hausa. Ana amfani da irin waɗannan kalmomi don ƙara wa zance armashi da nuna gwanintar harshe ta amfani da sautin da zai dace da saƙon karin maganar (Koko 2011 sh. 47). Da jin kalmar ‘Azarangaɗi’ za a fahimci cewa, wani sauti ne da yake bayyana muna siffar wata kishiya mai mugun hali wadda ake tsoron sharrinta da muguntarta.

12. Cin tuwon kishiya ramko

Ga al’adar Hausawa, matan da suke kishiyoyi suna gudanar da girki (dafa abincin da mutanen gida suke ci) ta hanyar karɓa – karɓa, kwana biyu- biyu ko ɗaya - ɗaya bisa ga yarjejeniyar da suka ƙulla a tsakaninsu ko da mijinsu. Saboda haka, duk kishiyar da aka dafa wa abinci ta ci a yau, to ta yi shirin yin nata girkin gobe ko jibi. (Usman, 2005 sh. 125).

Karin magana ya taskace al’adar nan ta girki da rabon kwanan aure a ƙasar Hausa. Haka kuma, duk wani abu na rashin jin daɗi da kishiya ta yi ga abokiyar zamanta, ta kwana da shirin za ta mayar mata da wani abu kwatankwacinsa. Ana amfani da wannan karin magana wajen bayyana al’ada ko ɗabi’ar nan ta cuɗe-ni-in-cuɗe-ka da ba-ni-in-ba-ka.

13. Kowa da kiwon da ya karɓe shi, kishiyar mai akuya ta sayi kura

Wannan karin magana ɓaro-ɓaro tana ɗauke da saƙon mugunta da yakan faru tsakanin kishiyoyi. Kowa ya san cewa akuya da kura dabbobi ne da ba za su haɗu a wuri ɗaya a zauna lafiya ba, amma duk da haka kishiyar mai akuya ta sayi kura wadda ita ga al’ada ba dabbar da matan aure suke kiwo ba ce, domin kawai ta cutar da abokiyar zamanta da kuma neman fitina. A nan, ana nufin duk wani abu da abokiyar zama ba ta son sa a rayuwa, kishiya tana iya ɗaukar sa abin so ta kuma riƙe shi sosai, saboda ta san ba zai taɓa samar da zaman lafiya tsakaninta da kishiyarta ba. Akan yi haka ne, ganin cewa kowane a cikinsu yana da ‘yanci ko iko na ya yi wani abu wanda tsarin zamantakewar aure ya ba shi dama. Don haka, sai mace ta yi amfani da irin wannan dama domin ta muzgunawa abokiyar zamanta. Ana amfani da wannan karin magana, idan ana son a nuna bambancin ra’ayi ga kowane al’amari.

14. Zuƙwi, doron kishiya

Wannan karin magana tana daga cikin karin maganan tsokana ta fuskar halitta ta hanyar amfani da kalma mai nuna gwanintar harshe. A ƙamusun Hausa na (CNHN, 2006:495) an nuna cewa kalmar ‘Zuƙwi’ daidai take da kalmar ‘buƙui’ inda aka bayyana kalmar ‘buƙui’ a (CNHN, 2006: 52) da ‘Wani abu mai burtsowa’ haka kuma a (CNHN 2006:52) an bayyana kalmar ‘buƙwi- buƙwi’ da cewa ‘kalma mai sifanta tafiyar mai ƙusumbi’. Don haka, wannan karin maganar ɓaro-ɓaro tana bayyana suka ne da ake yi da kuma tsokana tsakanin kishiyoyi. Wannan akwai alaƙa tsakanin karin magana da ke cewa:

15. Allah suturu buƙui, inji kishiyar mai doro

Wannan karin magana tana ƙunshe da gugar-zana da tsintsar tsokana. Allah shi ne wanda Musulmai suke bauta wa, suturi na nufin sutura, wadda kalmar larabci ce, wato tufa ko tufatar da wani ko wata ko kuma wani abu, buƙui alama ta doro ce, wato yadda yake zaune a baya kamar goyo. Kishiya kuwa ita ce abokiyar zama a gidan miji mai mace fiye da ɗaya. Doro kuwa wani ciwo ne da ke sa baya ya kasance da tarin tsoka, mai kama da tozon raƙumi ko shanu. Wannan karin magana, tsokana ce ta hanyar shaguɓe da kishiya ke wa kishiya na nuna mata cewa wai tana tausaya mata ga wani makasa ko cikas da ya sameta, kuma ya bayyana a fili yadda kowa yana iya ganinsa tare da yi mata fatan Allah mai ikon waraka da wannan damuwa ya rufa mata asiri kuma ya yaye mata.

16. Haka tara inji kishiyar mai mageduwa

A ƙamusun Hausa (CNHN, 2006 sh. 316) an bayyana ma’anar kalmar ‘mageduwa’ da cewa, ‘wani irin ciwo da yake cinye ‘yan yatsun ƙafa mai faruwa a dalilin cizon wani ƙwaro mai suna ‘mageɗuwa’. Wanan karin magana shaguɓe ne ga kishiya mai wannan ciwo na rasa yatsu. Saboda haka, wasu Hausawa cewa suke; haka tara, inji kishiyar mai yatsu tara’ domin kawai a ɓata mata rai.

17. Haka ratata, inji kishiyar mai ‘ya’ya tara

Wannan karin magana tana nuni ne ga tsokana da gugar zana da ake samu tsakanin kishiya da abokiyar zamanta musamman wadda ta tara 'ya'ya da yawa a gidan sakamakon gwarne, watau ɗaukar ciki kafin yaye na goye. Saboda hasada da kushe ne suka sa kishiyar mai ‘ya’ya tara ta bayyana kishinta da cewa ‘haka ratata’ (Muhammad 2003 sh. 36).

18. Ba zafi, barkonon taro a idon kishiya

Kome ƙarancin barkono (yaji) yana da zafi a ido, amma tun da yake a idon kishiya ne, ba wani abun damuwa ba ne, kasancewar kishiya ba ta yi wa kishiyarta fatar alheri, kusan koyaushe tana yi mata mummunar fata. Kishiya takan yi amfani da karin maganar domin ta fusata kishiyarta a yi faɗa ko cacar baka (Usman, 2005 sh. 122). A ƙamusun Hausa (CNHN, 2006 sh. 429) an bayyana ‘taro’ da cewa’ Kuɗi mai darajar kwabo uku a zamanin sulai da kwabo kafin zuwan Naira. Akwai mamaki ƙwarai a yadda wasu mata suka ɗauki kishiyoyinsu manyan maƙiya. Saboda irin wannan zafin kishin ne zai sa mace ta ce barkono har na taro (wanda kuɗi ne masu yawa a wancan zamanin) ba shi da zafi a ido, amma idon kishiya (Yunusa, 1989 sh. 83).

Wannan yana nuna cewa, duk wani abu na rashin jin daɗi da ake ganin kishiya ta yi wa kishiya, ba ta ganin girma ko nauyin abun da ta yi. A ganinta mene ne aibin wannan abin, saboda ita ma tana yi mata abubuwa masu zafi wanda suka wuce zafin barkono.

19. Rashin aiki, ta da kishiya daga barci

Wannan karin magana tana nuna wani salon tsananin kishi wanda ake ganin cewa mace ta tayar da kishiyarta daga barci. Wani rashin aikin yi ne ga mace kawai yake sa ta yi hakan, madadin haka ta bar ta ta yi ta sharar barcinta saboda mugunta. Wato kishiya tana ganin rashin aikin yi ne kaɗai zai sa a kama ma kishiya aiki, ko kuma a lurar da ita wani abu da ta sha’afa game da shi. A tunanin kishiyoyi, idan aka ga kishiya ta manta da abin da ya kamata ta aiwatar, kamata ya yi a ƙyaleta. Tunatar da ita rashin aikin yi ne musamman ga kishiyar da ke yin haka.

20. Aiki inda kishiya ba ya gudu

Ga al’ada kishiyoyi suna zaune wuri ɗaya kuma sukan gudanar da ayyuka tare. A mahangar al’umma, idan aka ƙarfafa guiwar kishiyoyi da gudanar da ayyuka tare, hakan zai sa su fahimci juna, su kuma zauna lafiya. Sai dai zahirin karin maganar na nuna cewa gudanar da ayyukan tare ba ya da wani amfani ko taimako, saboda kawai a rura wutar kishi (Usman, 2005:123).

Ana amfani da wannan karin magana a nuna cewa aiki tare da kishiya ba abin so ba ne, sai dai idan ya zama tilas.

21. Tallar kai, sata ɗakin kishiya

Wannan karin maganar tana bayyana cewa duk kishiyar da ta yi sata a ɗakin kishiyarta, wannan mata ta kai ga ƙololuwar fallasa, domin kuwa asirinta zai fi bayyana lungu-lungu, saƙo- saƙo, fiye da wadda ta yi sata a wani wuri na daban. Al’adar Hausawa, a mafi yawan lokuta akan kalli kishiya a matsayin mai bibiyar kishiyarta da sharri, kamar yadda aka gani a karin maganan da suka gabata. Haka kuma, nuna kasawa ne kishiya ta yi wani abu da bai dace ba a gaban kishiyoyinta ko ma a ɗakinta. Yin haka zai jawo mata rashin ƙima da tozarci a zamantakewarsu.

22. Mulkin mallaka biyan bashi da ɗakin kishiya

Wannan karin maganar tana bayyana cewa, saboda raini da fin ƙarfin kishiya, har ya kai ga kishiyarta ta yi biyan bashi da kayan ɗakin kishiyarta, domin ta mayar da ita ba kowa ba. Baya ga haka, karin maganar na nuna, idan kishiya ta rena abokiyar zamanta, to za ta juya ta tare da duk wani abu da ta mallaka ta hanyar sarrafa su daidai da abin da take da cikakken iko kansa.

23. Wada da wadaƙa, ta da kai da kishiya

Wannan karin magana tana bayyana cewa saboda wadata da kuma samun dama, kishiya ta ɗora kanta da za ta yi barci a saman jikin kishiyarta a matsayin matashin kanta (Filo). Kishiyoyi suna amfani da wannan karin magana don shaguɓe da tsokana. Wannan shi ma, yana nuna isar kishiya na samun mallakar kishiyarta wurin yin amfani da ita ga ayyukan gida, da duk wasu abubuwa da take so, saboda ta fi ta gata, ta mallake ta, ta fi ƙarfinta babu yadda za ta yi da ita.

24. Ikon gwatse, kishiya hana kishiya amsa waƙar miji

Wannan karin magana tana bayyana yadda wasu kishiyoyi idan suka samu dama suke hana kishiyoyinsu sakat da kuma rawar gaban hantsi a gidan miji.

25. Ikon mallaka, hana kishiyar tari ko tana mura

Wannan karin magana tana nuna cewa, irin karfin ikon da ke da kishiya a gidan mijinta, wanda har tana da ikon hana wasu abubuwa da ke faruwa a gidan mijin ko ta yi wani hukunci wanda maigidan ya kamata ya zartar da shi, amma saboda karfin ikonta, duk abin da ta zartar ya zartu. Kamar dai Bora da Mowa. Wannan kamar wadda ta gabata ne, hana wa kishiya walwala a gidan mijinta.

26. Magana ba mai ƙarewa ba, an sai da akuyar kishiya an sai wa amarya zane

Wannan karin magana tana bayyana muna tsananin kishin mata, musamman ma dai amarya wadda ba su riga suka shaƙu da juna ba. Saboda haka, idan har miji ya ƙwari uwargida don kawai ya kyautata wa amarya, haƙiƙa ya ɓamɓaro magana mai tsawo wadda za a daɗe ba a bar tattauna ta ba. Ita wannan karin magana tana nuni ne a kan cewa, matuƙar ana son samun zaman lafiya mai ɗorewa tsakanin kishiyoyi, to kar a yi amfani da wani abu mallakar kishiya a sarrafa shi ta hanyar amfanin kishiyarta, ko kuma wani abu da zai kawowa kishiyar ci gaba matuƙar ana son kauce wa mita da jinini.

27. Dabara ƙafa, inji kishiyar gurguwa

Wannan karin magana shaguɓe ce ga kishiyar da take da wani rauni ko tawaya wajen cimma wani guri a rayuwa. Gurguwa mace ce wadda ƙafafunta ba su da lafiyar da za su yi mata wata cikakkiyar moriya, ga shi kuma an ce dabara ta rage ga wanda ke da ƙafa.

28. Da alheri, kishiya ta hau kura da dare

Kusan koyaushe ba a yi wa kishiya fatar alheri. Saboda haka duk abin da ya faru da ita ko ya same ta komai illarsa komai haɗarinsa. yakan zama abin farin ciki da sambarka ga kishiyoyinta. Wannan ya sa duk da haɗarin da ke tattare da kura, amma ba a tausaya wa kishiya da ta yi izgilin hawan ta ba, balle a yi mata fatar sauka lafiya. (Usman, 2005 sh. 121).

29. Da alheri, kishiya ta taɓi kishiya da bakin wuta

Shi ma wannan karin maganar kamar wanda ya gabace shi ne, watau dai komai girman matsalar da ta shafi kishiya, suna ganin wani abin alheri ne a gare su. (Usman, 2005 sh. 124). Dalilin tsananin kishi da ƙeta ya sa mace ta taɓi kishiyarta da bakin wuta, amma ta ce, wai ta taɓe ta da alheri (Muhammad, 2003 sh. 36). A wani lafazin wasu Hausawa sukan yi amfani da wata kalma ta girmamawa a ce; Yaya, na taɓe ki da alheri, kishiya ta taɓi kishiya da bakin wuta. Duk wani aiki mai muni ko na jin zafi da yake bayyana a zahiri ko ƙunshe cikin karin magana, wanda kishiya ce take aiwatar da shi ga abokiyar zama, ana ganin wannan abu ba komai ba ne. Dalili shi ne, irin abubuwan da ake yi mata ke nan, ko irinsa take sa ran za a yi mata, wanda ta saba da gani da ji daidai da aikin ƙwarai.

30. Me na iya da abin da ya gagari wuta? Inji kishiyar ƙonanniya

Yaya zan yi da abin da ya gagari wuta? Inji kishiyar ƙonanniya. Wannan karin magana tana bayyana mugunta da shaguɓe da tsokana a tsakanin kishiyoyi. Mace ce wuta ta ƙone mata jiki, iyakar musiba kuwa ke nan da ya kamata a tausaya wa wadda ta shafa, amma saboda tsananin kishi har kishiyarta tana ganin bai dace ba a ce wutar ba ta ƙone ta ƙurmus ta huta da ita ba, domin laifinta ya cancanci abin da ya wuce hakan. Manufar wannan karin magana ita ce shaguɓe ga kishiyar da wuta ta ƙone don a bayyana ta a matsayin babbar mai laifi (zunubi) (Usman, 2005 sh. 124).

A wannan karin maganar an nuna cewa wannan magana ta faru ne a tsakanin kishiya da kishiya, inda aka nuna cewa, ɗaya kishiyar ta taɓa yin gobara ta ƙone, sai dai ba ta mutu ba. Saboda haka, duk lokacin da kishin ya motsa, ita kishiyar kan jefa wannan magana don ta ɓata mata rai. Misali; ta ce, ni ɓata lokaci ma nake yi, tun da wuta ma ta ci ta bari, ni me zan iya yi (Malumfashi, 2014: 98). Don haka zan iya cewa, saboda tsananin kishi da kishiya ke yi wa yar uwarta har ya kai ba tausayi tsakanin su, saboda tsananin kishi. Ita dai kishiya a koyaushe an ɗauketa a matsayin wata abar ƙi wadda tsakanin ta da abokiyar zamanta, kawai ƙiyayya ce tsakanin su, ba tausayawa, ba aminci, haka kuma idan abu ya haɗa su ba batun haƙuri ko yafiya a tsakaninsu. Dalilin bayanin da ya gabata, wasu Hausawa cewa suke yi; yaya na iya da kingin wuta, inji kishiyar ƙonanniya.

31. Da zaman banza gara aikin kishiya

Wannan karin maganar tana nuna al’adar nan ta matan Hausawa ta matsanancin kishin da ke tsakanin mata a ƙasar Hausa. Amma duk da wannan kishin matar Bahaushe ta yarda da faɗin da zaman banza gara aikin kishiya (Malumfashi 2000 sh. 4). Saboda muhimmancin da Bahaushe ya ba wa tattalin arziki, ya sa duk da matsanancin kishin da ke tsakanin kishiyoyi a ƙasar Hausa, matar Bahaushe ta amince da hakan. Ga al’ada da ɗabi’ar mata, ana kallon kishiya a matsayin wadda ba ta da muhimmanci ko amfani, saboda haka ne aka danganta ta da zaman banza. Akan yi amfani da wannan karin magana don a harzuƙa kishiya zuwa ga faɗa (Usman, 2005 sh. 123).

Wannan karin maganar tana daga cikin karin maganan da suke zaburar da mutane da kuma sa masu ƙaimi na su tashi daga zaman banza, su samu wani aiki, komai ƙanƙantar muhimmancinsa, su yi. A wannan hali, a iya cewa, ita dai kishiya kurarta ta rigaya ta yi kukan akan ɓacin suna.Duk wani abu da aka ɗauko ko kishiya ta ɗauko za ta yaɓa wa yar uwarta ne ta kishi, haka kuma za a riƙa jin kalamai waɗanda ba su dace ba duk tana jefa mata. Ita wannan karin magana tana nuni ne a kan cewa; komai lalacewar mutum ko jin kasalar jikinsa, ya kamata ya tashi ya nemi na kansa ko dan ya kore wa bakinsa ƙuda, wato komai lalacewar aiki in dai za ka samu to gwara ka tashi ka yi, ya fi ka zauna kana jiran tsammanin warabbuka, “Malam ya ƙi noma don zakka”.

32. Ko miye daɗinki da kishiya, inji babbar ƙawar amarya

Wannan karin magana tana bayyana yadda wasu makusanta ko dangin mace waɗanda suke da kusanci ko danganta da ita a kan bijire wa kishiyarta da suke zaman lafiya da ita, ta hanyar ƙirƙirar karan tsana su ɗora mata domin a tsunduma ta cikin al’adar kishi. Ke nan, wani kishi yana samuwa daga ƙawaye, masu kawo ziyara gidan amare.

A nan, babbar ƙawar amarya ce ta ga ƙawarta (abokiyarta) tana kyakkyawan zamantakewa da uwargidanta, maimakon ta ji daɗin haka, sai ta ɓuge da zuga zuwa ga rufe shafin kyakkyawar zamantakewa da buɗe shafin mummunan kishi.

33. Ban ce a mutu ba, ban ce a warke ba, ciwon kishiya a yi ta lalacewa kan gado

Wannan karin magana tana bayyana zazzafan kishi da rashin tausayi ga wasu mata, inda a nan kishiya ce ba ta da lafiya, maimakon abokiyar zamanta ta tausaya mata da yi mata fatar samun sauƙi, idan ciwon mai warkewa ne da kuma yi mata addu’ar neman kyakkyawar cikawa, idan ciwo ba mai barin ta ba ne. To amma saboda mugun kishi sai take yi mata fatar kada ta samu waraka daga lalurar ciwon, kuma kada ta mutu don kada ta huta daga wahala, ta fi son ta ci gaba da rayuwa cikin wahala tana lalacewa a kan gado kullum. Kishiyar da ake neman taimakonta a kan wata matsala da kishiyarta ta afka wa, takan iya yin amfani da wannan karin magana (Usman, 2005 sh. 126).

34. Abin kamar bi ta da ƙulli, bin kabarin kishiya

Wannan karin magana tana bayyana cewa duk da yake kishiya ta mutu har an binne ta a ƙabari, amma kishiyarta ba ta zauna lafiya ba, har sai da ta yi takakkiya zuwa ƙabarinta da tsakiyar rana. Ana amfani da wannan karin magana a yi bayani a kan duk wanda idan wutar rikici ta lafa, sai ya yi ƙoƙarin tona ta (Usman, 2005 sh. 124).

35. “Bi ta da ƙulli, bugun kabarin kishiya da muciya, (Koko 15 & 26).

Ita ma wannan karin maganar kamar wadda ta gabace ta ne, bambanci kawai shi ne, an tafi da abin bugu, watau ‘muciya’ kuma an bugi ƙabarin, saboda haka fitinar ta fi tsananta a nan. Irin wannan bi ta da ƙulli tsakanin kishiyoyi, yana nuna ko bayan mutuwar kishiya, ana yin kishi da ‘ya’yanta da danginta da abokanta, da abokan hulɗarta.



[1] Wannan kalma ta zugurnugu tana nufin wani babban al’amari ko wani tarin abu mai yawa wanda zai yi wa mutum wahalar ɗauka.

Manazarta

Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449 

Post a Comment

0 Comments