Ticker

6/recent/ticker-posts

Hoton Kyakkyawar Zamantakewar Ma’aurata a Karin Magana

Daga

Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani

Aure a Kunshiyar Karin Magana

Akwai wasu jerin karin magana da ake amfani da su a ƙasar Hausa domin a bayyana yadda kyakkyawar zamantakewa tana gudana tsakanin ma’aurata.

1. Dace da masoyi riba

Wannan karin magana tana nuna cewa duk wanda ya samu sa’a kuma ya yi nasarar auren wanda yake so kuma shi ma yake son sa, to ya ci riba, watau, ya yi nasara. Ana amfani da wannan karin magana ne a wurin nuna cewa, bayan mutum ya sami abin da yake ƙauna, sai kuma abin ya zame masa mai matuƙar amfani.

2. Zaƙin zaƙafere, mai gida fere kabewa

Wannan karin magana tana daga cikin karin maganan da suke farawa da kalmomi na nuna gwanintar harshe waɗanda ake kwatanta bayanin ma’anarsu ta hanyar sautinsu da saƙonsu. Ma’anar wannan karin magana shi ne, zamantakewa ta yi daɗi sosai tsakanin ma’aurata (Miji da mata) wanda har maigida ya kama yin aikin gida irin wanda ga al’ada aikin mata ne ba na miji ba, watau fere kabewa.

Ana amfani da shi ne wajen bayyana alamun farin ciki da wani ya shiga, wanda har ya kai yana aikata abin da ga al’ada ba kasafai ya ke yi ba.

3. Mamakin makiro, miji ɗaka mata wuri suna rabkar dariya

Wannan karin magana tana nuna faruwar wani abu mai ɗaukar hankali wanda ba a saba gani ba kuma mai sa mutanen gida su yi dogon tunani game da kyakkyawar zamantakewar ma’aurata da ta sa su yawaita dariya, don nuna suna cikin farin ciki da annashuwa, alhali suna wurare daban-daban, miji yana cikin ɗaki, ita kuwa matar tana waje.

Ana amfani da shi wajen nuna ta’ajibin faruwar wani abu ba ta fuskar da aka saba gani ba.

4. Daɗin aure shi ke sa a ce wa miji baba

Ga al’ada, miji abokin zamantakewar matarsa ne, amma idan har zamantakewar auren ta yi daɗi fiye da yadda aka yi tsammani, matar takan ƙara masa matsayi da mutunta shi ta hanyar karrama shi da wasu sunaye masu daɗi na girmamawa. Wannan karin maganar tana nuna cewa idan zamantakewar aure ta yi daɗi tsakanin mata da miji to, babu sunan da ba za ta iya kiransa da shi ba na girmamawa.

Ana amfani da shi wajen nuna cewa, kyakkyawar zamantakewa ke haifar da kyakkyawan kalamai na girmamawa ga masu zaman tare.

Manazarta

Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449 

Post a Comment

0 Comments