Daga
Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani
Kamar yadda aka tattauna a babi na farko, aure babban ginshiƙi ne daga ciki matakan rayuwar Hausawa. A bisa wannan dalili, babu mamaki idan aka same shi cike a karin magana domin nuna matsayinsa. Duk wata matsala ko nasara ko ƙalubale da aka samu a rayuwar aure, sai an samu karin magana mai nuna tunanin Hausawa a kan abin kamar yadda za a gani, a cikin misalan da aka kawo a ƙasa:
1. Aure yaƙin mata
Mata sukan ɗauki
hidimomin aure da muhimmanci. Misali, iyaye mata sukan fara tara kayan ɗakin ‘ya’yansu mata tun ‘ya’yan suna ƙanana
don dai fita kunya. Haka kuma, mafi yawan hayaniyar aure sun shafi mata ne,
musamman abin da ya shafi kishi (kishi da kishiya ko da kishi-balbal[1] ko da uwar miji ko da
agola, da sauransu).
Wannan karin magana yana nuna matsayin aure da kuma sadaukarwa da
jaruntakar mata a wajen gudanar da shi. Kusan a wajen sha’anin aure, mata sun
fi maza kazar-kazar ta hanyar kai da kawonsu a lokutan shagulgulan buki da
zaman auren kacokam. Don haka, aure da duk wahalolinsa suka zama yaƙin
mata.
2. Allah ya yi abin inji mafaɗin aurensa
Karin maganar yana nuna al’adar Hausawa ta kunya, inda yake sakaya sanarwar
aurensa ga jama’a ta hanyar kinaya. Ga al’adar Hausawa akwai jin nauyi saurayi
ko budurwa su ce "na yi aure" a cikin jama'a, saboda haka, sai
a sakaya a ce "abin". Idan mutum yana jin kunyar ya faɗi labarin wani abin alheri, mai daɗi da ya same shi, wani lokaci yakan yi waɗansu ‘yan kwane-kwane domin mutane su
sani. Haka kuma, karin maganar yana nuni da yadda mafaɗin yake cike da alamun nuna farin cikinsa
na tsallake wata jarabawa ko wani ƙalubale na yaƙin aure.
A wata faɗar
kuma cewa aka yi:
3. Allah ya yi, aure da maras kwabo[2]
Aure sha’ani ne wanda yake buƙatar kuɗi. Hidimomin da suka shafi kula da iyali tun daga
kan ciyarwa da tutafatarwa da sauransu, duk suna buƙatar kuɗi. A nan, karin magana tana nuna lallai
hidimar aure batu ne na wanda yake da kuɗi. Babu yadda za a yi mutum ya yi aure ba tare da
ya nemi kuɗi ko
yana da kuɗi ba.
Akwai abubuwan buƙata masu yawa waɗanda mai neman aure zai samar ga wadda
yake nema da aure, musamman daga lokacin da aka sanya masu rana. Ambatar kwabo
a nan yana nufin ya kasance mutum yana da kuɗi na yin wasu hidimomi da suka zama wajibi
gare shi. Misali kayan sa rana, biyan sadaki, kayan lefe da dai sauransu, akwai
abubuwa masu yawa da suka zama dole ango ne zai yi wa kansa, ba a kawo su a
matsayin gudunmawa. Don haka ake ganin akwai mamaki aure ya yiwu ga marar
kwabo. Hasali ma, mata sun fi son auren mai kuɗi saboda su samu gidan hutu da bushasha.
Ana amfani da wannan karin magana a duk lokacin da wani mawuyacin al’amari
ya gudana cikin sauƙi. Kwabo, shi ne kuɗi mafi ƙanƙanci a tsarin darajar kuɗin Nijeriya a yanzu.
4. Arha, aure bashi/Araha, auren bashi
Hausawa suna kyamar yin aure da bashin sadaki, duk da cewa shari’ah ta aminta da shi. A fannin rayuwar
aure, ba kasafai akan aiwatar da shi ta hanyar bashi ba. Saboda haka ake ganin
cewa duk auren da aka gina shi a bashi, to ya yi sauƙi ƙwarai kuma ya yi rahusa.
Ana amfani da wannan karin magana wajen bayyana duk wani abu da mutum ya
samu ta wata hanya mai sauƙi, ba irin wadda aka saba da ita ba. Sai dai, aure
bashi yana da wasu matsaloli da suka haɗa da gori
da saɓani da samakamantansu.
5. Abin da kamar wuya, gurguwa da aure nesa
Wannan karin magana yana bayyana al’adar Bahaushe ta cewa duk wani ɗan’uwa mai wata naƙasa ko tawayar rayuwa,
ba kasafai ake bari ya yi nisa da ‘yan’uwansa
ba, saboda buƙatuwarsa ga taimako da kuma kulawar ‘yan’uwansa. Bisa ga wannan duk da aure ba a cika barin mai rauni ya yi nisa da gida
ba. Ta wata fuskar kuma, yayin da mai naƙasa ya yi aure a nesa da gida, musamman
mace, to hakan zai zama ƙalubale musamman a rayuwa irin ta gargajiya.
Ana amfani da wannan karin magana wajen hannunka mai sanda ga duk wani
lamari da ake ganin wahalar yiwuwarsa ga wani.
6. Aure farin cikin babba da yaro
Wannan karin magana yana nuna mana yadda aure yake abin farin ciki da nishaɗi da murna ga kowa da kowa, musamman a
lokutan da shagulgulansa da bukukuwansa suke gudana.
7. Auren baya, shi ne sadakin na gaba
Yunusa (1989 sh. 4) yana da fahimtar cewa, wannan karin maganar yana nuna
cewa irin halayen kirki da mace ta nuna a aurenta na baya, su ne suke taimaka
mata wajen sake samun wani mijin aure da wuri kuma a cikin sauƙi. To
amma idan ta nuna halaye marasa kyau a aurenta na baya, ba za ta sami miji
nagari cikin sauƙi ba. Haka abin yake ga shi ma namiji.[3]
Ana amfani da wannan karin magana a nuna cewa duk wanda ya aikata halayen
nagarta a mu’amalar farko, to zai samu karɓuwa a harkoki na gaba. Idan kuma bai nuna
halin nagarta ba to ya ɓata
harkokinsa na gaba. Shi ya sa Hausawa suke cewa mutunci madara ne.
8. Zaman lafiya ya fi gara
Wannan karin maganar tana bayyana cewa zaman lafiya tsakanin ango da amarya
ya fi muhimmanci bisa ga al’adar nan ta gara. A ƙamusun Hausa an bayyana ‘gara’ da cewa: “Kaya, musamman na abinci da iyayen
amarya kan kai wa ‘yarsu bayan an gamo bikin aure ko haihuwa” (CNHN, 2006
sh. 157).
Dangane da wannan karin maganar, Yunusa (1989) ya yi tsokaci da cewa: “Wato,
mutum ya sami zama lafiya tare da amaryarsa, ya fi a kawo musu gara mai yawa,
amma babu kwanciyar hankali. Zaman lafiya da so da yarda da aminci mai ɗimbin yawa, ya fi a kawo wa amarya dukiya
mai yawa, amma ba zaman lafiya da salama, ita da mijinta” (Yunusa, 1989 sh. 122).
Ana amfani da wannan karin magana a cikin harkokin yau da kullum a nuna
cewa, zaman lafiya shi ne jigon zamantakewa da kowace irin mu’amalar rayuwa,
kuma duk wani samu idan ba ya tare da zaman lafiya, to samun banza ne. A ɓangare ɗaya kuwa, ana amfani da ita domin nuna
cewa, ya fi dacewa a samu nasara ta dindindin a maimakon a mayar da hankali kan
wata nasara ko burgewa ko nishaɗi na ƙanƙanin
lokaci.
9. Fallasa, aure bashi
Kalmar fallasa tana nufin tonon asiri ko tonon silili. Wannan karin
magana tana bayyanawa ƙarara cewa, duk da yake aure bashi yana da arha,
to sai dai bai cika rabuwa da fallasa ba. Saboda haka a al’adar Bahaushe duk wanda ya yi aure bashi,
yakan gamu da tonan asiri a wasu lokuta har dai idan aka yi rashin arzikin
biyan sadakin bayan tsawon lokaci. Baya ga haka, wadda aka auro idan ya kasance
ta iske wata matar mijin a gida (kishiya), za ta gamu da gori kullum. Haka
kuma, duk wadda ta yi saɓani da
ita, za ta iya goranta mata cewa bashi aka auro ta, tamkar an gaji da ita, an ƙosa a
aurar da ita; don haka ne, aka aurar da ita bashi. Bugu da ƙari, a
tsakanin dangin miji ma ba za ta yi daraja da kuma ƙima ba. Duk lokacin da
aka sami saɓani da
ita ana iya goranta mata.
Ana amfani da wannan karin magana a matsayin alamar motsin rai game da wani
lamarin fallasa da ya auku. Misali:
Alƙali ya bankaɗo badaƙalar da suka yi,
har an yaɗa a jaridu. Wannan shi ne fallasa, auren bashi!
10. Je-ka-na-yi-ka, aure bashi
Shi kuwa wannan karin magana yana nuna wata illa da auren bashi yake
tattare da ita. Aure ne da zai iya kasancewa marar armashi da ƙima a
idon al’umma.
A ɓangaren ma’aurata kuwa,
duk wanda ya yi shi, yakan iya kasancewa mijin je-ka-na-yi-ka. Ma’ana, wanda ba
ya da ta cewa sai yadda aka yi da shi. A nan miji ba shi da wata kataɓus, ba shi da ta cewa a gidansa, kuma ba
shi da ikon sa wata doka a gidan, saboda bashi ya yi auren.
Ana amfani da wannan karin magana domin nuna wani lamarin da ba shi da
armashi, wato na je-ka-na-yi-ka. Misali:
Ai gwamnati ba gaskiya take yi ba game da wannan
shirin. Ba ta ɗauke shi da muhimmanci ba. Je-ka-na-yi-ka ne kawai, auren bashi.
[1]
Kishi-balbal ita ce matar wa ko matar ƙani.
Matan ‘yan’uwa sukan yi kishi a tsakaninsu.
[2]
Wani lokaci akan ce: “Allah ya yi abin, aure da maras kwabo.”
[3]
Buƙatar sake aure takan
taso yayin da aka samu rabuwar aure (saki) ko kuma rasuwa.
Manazarta
Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.