Ticker

6/recent/ticker-posts

Haihuwa a Al’umar Hausawa: Nazari Daga Tatsuniyoyi

Article Citation: Binta Musa Hassan (2019). Haihuwa a Al'umar Hausawa: Nazari Daga Tatsuniyoyi. DEGEL: The Journal of the Faculty of Arts and Islamic Studies, Vol. 17, No. 1. ISSN 0794-9316

HAIHUWA A AL’UMAR HAUSAWA: NAZARI DAGA TATSUNIYOYI

By

Binta Musa Hassan
Sashen Koyar da Harshen Hausa
Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi, Kumbotso, Kano
bintamusahassan@gmail.com

Tsakure

Wannan takarda mai taken haihuwa a al’umar Hausawa: nazari daga tatsuniyoyi.Ta yi waiwaye ne a kan matsayi da fa’idojin haihuwa da kuma wasu al’adun haihuwa daga tatsuniyoyin Hausa. Manufar wannan bincike ne, ƙyallaro ir-iren hidimomin da Hausawa ske yi a duk lokacin da aka sami haihuwa. Za a kalli tatsuniyoyi na Hausa a yi bitarsu da duk waɗansu ayyuka masu nasaba da hakan domin daidaituwar matani. Tabbas haihuwa na da muhimmin matsayi a rayuwar Hausa, wanda ya sa ta sami gurbi a ɗaya daga cikin adabin baka na Bahaushe, wato tatsuniya. An gano cewa akwai al’adu masu tarin yawa da suka shafi haihuwa a cikin tatsuniyoyi da suka haɗa da wa dai kyauta ce daga Ubangiji kuma tana ƙara wa duk mutumin da Allah ya albarkace shi da ita kima da daraja. Duk wanda Allah Ya ba shi ɗa, an gama masa komai na duniya. Musamman idan ya yi wa ‘ya’yan kyakkyawar tarbiyya, hakan ka iya zama sanadiyar shigarsa aljanna. Hausawa kuwa mutane ne masu son haihuwa da son tara ‘ya’ya da yawa. Wasu lokutan waɗanda Allah bai ba wa haihuwa ba, kan samu kansu cikin takaici da damuwa. Har sukan kasa yin haƙuri, sukan yi ta yin ƙoƙari iri-iri don ganin su ma Allah Ya ba su nasu ‘ya’yan. Takardar ta kuma yi bayani a kan alamomin samun juna biyu. Sannan aka kalli wasu daga cikin hanyoyin da Hausawa kan bi wajen kula da da kuma renon ‘ya’ayansu, kamar irin su goyon ciki da wankan jego da reno da sauransu.

Gabatarwa

Al’ada tsarin rayuwa ne da mutune suka saba yi a cikin rayuwarsu ta duniya, ta ƙunshi harkokin da suka yi ko suke yi da waɗanda suka faru gare su na alheri da akasin haka da dukkan buƙatunsu na zaman duniya. Ciki kuwa har da fasaharsu da ƙere-ƙere da tarbiyya da horo da hani da sauran wasu halaye da ɗabi’un kirki ko akasinsu, waɗanda ɗan Adam ke yi, kuma al’umma ta aminta da su. Al’ada ta haɗa da nasarorin da jama’a suka samu a shekara da shekaru domin ganin sun mallaki abubuwan da ke kewaye da su domin biyan buƙatunsu na rayuwa. Al’ada muhimmiyar aba ce kuma ja gaba a tafiyar harkokin yau da kullum na rayuwar al’umma, domin ita ce rayuwar al’umma baki ɗaya, tun daga haihuwa zuwa mutuwa. Tana kuma taimakawa matuƙa wajen warware matsalolin rayuwa da kuma samar wa al’umma ingantaccen tsari da tsaro.

Adabi kuwa, wata hanya ce da al’umma ke amfani da ita don bayyana al’adunta. Wato dai, ta nazarin adabin wata al’umma, mutum zai iya samun tarihin rayuwar al’ummar. Ya gane irin ɗabi’un jama’arta da basirarsu da yadda tunaninsu ke gudana da irin tsarin rayuwarsu, a fannonin mulki da tattalin arziki da zamantakewa da tarbiyya da duka ɓangarorin rayuwa tun daga haihuwa zuwa mutuwa. Adabi madubi ne da ake amfani da shi domin a haskaka, a kuma tantance yadda al’umma ke aiwatar da al’amuranta na hikima da fasaha a gargajiyance kamar, waƙe-waƙe da azancin magana da wasanni da labaru da tatsuniyoyi da sauransu.

Al’ummar Hausawa suna da nau’o’in adabin baka, waɗanda suka haɗa da waƙa da zube da wasan kwaikwayo da kuma zantuttukan azanci da hikima. Tatsuniya wadda wannan takarda za ta yi nazari a kai, ɗaya ce daga cikin ‘ya’yan zube a adabin baka na Hausa.

Tatsuniya wata hanya ce ta dabara, wadda mata, musamman tsofaffi da sababbin amare suke sarrafa harshe tare da ƙuƙƙula wasu maganganu na basira cikin azanci domin isar da wani saƙo ko cimma wani buri (Muhammad, 2003: 8). Tatsuniya, tana da amfani domin a lokacin da, da ilimi da karatu ba su samu ba a ƙasar Hausa da ita ake koyar da tarbiyya ga yara. Tatsuniyoyi da labarai, su ne makaranta ta ‘ya‘yan Hausawa, inda suke koyon tarbiyya ko halayen kirki da hani da miyagun halaye da kuma dabarun zaman duniya, kamar dabarun kare kai, samun abinci da sauransu (Ɗangambo, 1984:16).

Akan iya fahimtar tunanin al’umma da al’adunsu ta hanyar tatsuniyoyinsu. Domin a cikinta akwai tarin abubuwa waɗanda suka shafi rayuwar al’umma. Sannan akan iya sauya tunanin al’umma dangane da yadda ake buƙata ta zama ta fuskar adabi da tarihi ta hanyar tatsuniyoyinsu. Don haka wannan takarda ta sa tatsuniya a gaba domin duba hoton al’adun haihuwa a cikinta.

Haihuwa

Balarabe (1980) ya ce, haihuwa ita ce dandamalin kusantuwar al’umma a matsayinta na dunƙulalliyar jama’a mai al’adu iri ɗaya. Bayan tsarin aure ya tabbata, haihuwa c eke bayar da tafarkin yin tarbiyya inda ake koya wa mazowa baya yanayin rayuwar jama’arsu su tashi da ita.

Shi kuwa Abdullahi (2008) sai ya ce, haihuwa karuwa ce ta hanyar fitowar wani abu mai rai daga jikin wata halitta jinsin mace wanda ya ɓoyu a wani wuri na musamman na wani ƙayyadadden lokaci sakamakon saduwar jinsin mace da namiji.

Haihuwa tana daga cikin tsarin matakan rayuwa guda uku, aure da haihuwa da mutuwa. Haihuwa ita ce gaba da aure kuma baya ga mutuwa. Haihuwa ita ce mafi girman hanyar yaɗa zuriya da yawaitar da jama’a. Kuma ta haihuwa ne al’umma kan bunƙasa ta fifita tsakanin al’umomi.

Fa’idojin Haihuwa Daga Tatsuniya

“Haihuwa maganin mutuwa, ba don ke ba da iri ya ƙare”. Wannan na daga cikin kirarin da Hausawa ke yi wa haihuwa. Haihuwa hanya ce muhimmiya wajen yaɗa zuri’a da yawaita jama’a. Ta hanyar haihuwa ne kaɗai ake samun zuri’a, a samu magada. Hausawa sukan ce, “Kyawun gida da magaji”. Ta hanyar haihuwa ce al’umma ke bunƙasa, a yawaita a duniya. Yawan jama’a kuwa a cikin al’umma abin alfahari ne ga tattalin arziki da kuma siyasa, musamman ga Hausawa waɗanda suke da tsarin iyali ‘mai yaɗo.’ Samuwar yara a cikin iyali martaba ne ga maigida da sauran mutanen gida, domin taimakawar yaran ga harkokin gida, musamman wajen aikin noma da sauran aikace-aikace da aike-aike daga wannan wuri zuwa wancan. Har Hausawa sukan ce: “Haihuwa mai rana ko kana gudu haifi ka yar, wata rana sai ka waiwaya”. Haihuwa kan yi ranarta a duk lokacin da mutum ya mori ɗansa ko ‘yarsa. Misali samun taimako tatsuniyar Ɗan-ƙashin-gwiwa, ta yi nuni da haka:

Samun Taimako

“Wata rana an yi wata mace mai yawan roƙon haihuwa. Ran nan sai wani ɗan ƙurji ya fito mata a kan gwiwarta. Sai ta ce, “Allah ka ba ni ɗa ko da na ƙashin gwiwa ne ma mana”. Shi ke nan, take sai ta ɓincine ƙurjin nan na kan gwiwarta. Sai kuwa ta ga ɗa ya fito suɓul. Sai ta yi murna. Bayan ta gama murna, sai ta ce; “To, yau kuma ina zan sami itacen wanka?” Sai Ɗan-ƙashin-gwiwa ya ce, “iya ba ga ni ba”. Sai kuwa ya je ya yiwo mata ita ce mai yawa, ya kawo mata. Ta kuma cewa, “ko ina zan sami abincin da zan ci?” Sai ya ce, “iya ba gani ba. Sai ya je gidan namun dawa ya ɗebo mata alkama da shinkafa da dai hatsi iri-iri ya kawo mata” (Yahaya, 1972:38).

A nan haihuwa ta yi wa Iyar Ɗan-ƙashin-gwiwa rana, domin ga shi daga haihuwarsa har ta more shi, ya samo mata itacen wanka da abinci.

Tatsuniyar Wata Tsohuwa ta ƙara fito da fa’idar haihuwa, domin abin da ya faru ga ‘yar tsohuwa na wahala a wajen ɗiban ruwa da tana da ɗa ko jika da shi zai samo mata ruwan tana zaune, ya kawo mata, da ba ta sha wahalar da ta sha ba. Kamar yadda tatsuniyar ta nuna:

“Ana nan cikin warkajamin ɗiban ruwa, sai ga wata ‘yar tsohuwa tukuf da ita wai ita ma ta zo ɗiban ruwa. Akwai wani abin tausayi game da wannan ‘yar tsohuwar. Watau tana da miji, amma tun da Allah Ya halicce su, ba su taɓa haihuwa ba. Kullum sai roƙon Allah suke yi Ya ba su haihuwa tun kafin su kwanta dama, amma ba su samu ba” (Yahaya, 1977:4).

A tatsuniyar an nuna ita dai wannan tsohuwa tun safe ta zo ɗiban ruwan nan, amma har magariba, kai maƙato maƙato har sai da gari ya waye ba ta samu ruwa ko da na sha ba. Shi kuma ruwan saboda wuyarsa da ƙoƙon ƙwara ake ɗiban sa.

Adon Rayuwa

Bayan haka kuma, haihuwa adon rayuwa ce mai bai wa mutum damar jin ya ci ribar zamansa na duniya. Domin tana cusa wa ɗan Adam farin ciki a rayuwa da kuma gamsuwa. Wannan dalili ne ma ya sa Hausawa kan ce, ‘wanda ya shuri arewa, amma ya bar ‘ya’ya rasuwa ya yi, ba mutuwa ba’. Wato ya bar na baya, waɗanda za a dinga gani ana tunawa da shi, kuma waɗanda za su riƙa yi masa addu’a. Sannan tana kafa tushen zumunta da ƙarfafa wanda ke tsakani da kuma kyautata soyayya da ƙarfafa danƙon aure tsakanin ma’aurata. Domin da an yi aure, babban burin ma’aurata da duk masoyansu shi ne samun ƙaruwa, wato zuri’a, ‘ya’ya nasu na kansu. Saboda haka ne akan yi addu’a da cewa; ‘Allah Ya kawo ƙazantar ɗaki, amma ba ta rashin shara ba.’

Farin Ciki

Haihuwa tana sa farin ciki da jin daɗin a rayuwa, rashinta kuma akwai sosa rai da takaici. Saboda wannan dalili ya sa wasu matan sukan roƙi Allah cewa, ko da bayan Ya ba su zai karɓi abinSa, to a ba su, a ce dai su ma sun taɓa haihuwa. Tatsuniyar Reru ta nuna:

“A wani gari mai nisan gaske, an yi wata mace wadda ta ɗauki lokaci mai tsawo ba ta sami haihuwa ba. Wata rana suna hira tare da wasu abokanta mata masu haihuwa suna cewa, “haihuwa tana faranta rai, lokacin da aka haifi ɗa namiji ko ɗiya mace. Kuma rai yana ɓaci lokacin da aka rasa abin da aka haifa. Sai wannan mata da ba ta taɓa haihuwa ba ta ce, “ ita kam ko wanda Allah za Ya ba ta ya koma ya karɓa tana so”. (Koko, 2009: 120).

A tunanin Hausawa ‘ya’ya maza sun fi ‘ya’ya mata, don haka idan mace ta cika haihuwar ‘ya’ya mata, ba ta haifi namiji ba, shi ma an gudu ne, ba a tsira ba. Akwai wani karin magana da ake cewa, ‘gwamma da ku da rashinku’. Wannan yana nuni da yadda Hausawa ba su cika son a haifa masu ‘ya’ya mata ba. Domin har kullum Hausawa, musamman maza na ganin ɗa namiji shi ne magaji, ita kuwa ‘ya mace ‘yar gidan wani ce, domin duk daɗewar ‘ya’ya mata a gidan iyayensu, wata rana za a aurar da su. Wasu kuwa ba sa son ‘ya’ya mata ne saboda irin tsarabe-tsaraben da ke tattare da su, tun suna yara, har zuwa lokacin aurensu, irin kuɗaɗen da za a riƙa kashe masu na kayan ƙyale-ƙyale a lokacin da suka zama ‘yammata da na kayan ɗaki a lokacin aurensu. Sannan wasu na ganin ‘ya mace na iya jawo masu abin kunya, idan ba mai kamun kai ba ce. A tatsuniyar Wata ‘Yar Sarki an nuna yadda kullum Sarki yake ta roƙon Allah Ya ba shi ɗa namiji, amma ba ya cewa mace:

‘An yi wani Sarki mai jama’a da yawa da kuma arziƙi. Shi dai Allah bai taɓa ba shi haihuwa ba. Kullum yana ta roƙon Allah ya ba shi ɗa namiji. Idan ya je masallaci bayan an ƙare salla, sai ya ba malamai kuɗi su taya shi roƙon Allah don samun ƙaruwa’ (Ɓaɓura,1986:83).

Ganin haka sai su ma matan suka fi son haihuwar ‘ya’ya maza maimakon mata, don ko sa sami ƙarin so daga wajen mazajensu. Kuma idan mijin mai muƙamin sarauta ne, tana tunanin nan gaba ɗanta zai gaji sarauta. Sannan kuma duk matar da ke haihuwar ‘ya’ya maza, ita ke da gida, domin sai ta fi sauran matan samun karɓuwa a wajen maigida.

Wasu Al’adu da Batutuwa Game da Haihuwa

A al’ummu, fahimtar cewa mace ta sami juna-biyu kan danganta ne ga abubuwa da dama. Waɗannan alamu sun haɗa da; canzawar kalar fata zuwa fara, da yawan zubar miyau, da sauransu. Al’adun haihuwa da aka san Bahaushe das u sun haɗa da iccen biƙi da kayan yaji da na jiƙo da na dafa ruwa da kuma na wanka.

Ba ma ga al’umma ba, ko ga mutum guda, haihuwa aba ce babba. Tare dad a kasancewar ‘ya’ya wani irin adon rayuwa mai bai wa mutum ƙarin farin ciki da annashuwa. Misali;

Son Haihuwa

Hausawa mutane ne masu son haihuwa, kuma ba sa gajiya da ita komai yawan ‘ya’yan da suka samu, har sai ta tsaya da kanta. An tsinkayi haka a cikin tatsuniyar Ɗan’auta da yayyensa Dodanni:

“Wata mace ce dai ta haifi ɗanta mai kai goma. Da ta tashi sake haihuwa sai ta haifi mai kai tara. Ta kuma sake haihuwa ta haifi mai kai takwas. Ta sake haihuwar mai kai bakwai. Ta kuma haihuwar mai kai shida. Ta ƙara haihuwar mai kai biyar. Sai ta haifi mai kai huɗu. Sannan ta haifi mai kai uku. Sai kuma ta haifi mai kai biyu. Daga ƙarshe sai ta haifi mai kai ɗaya” (Yahaya,1974:28).

Mace ɗaya tal ta haifi ‘ya’ya goma, a tsarin iyalin Hausawa na auren mata huɗu, wannan ya nuna lallai Hausawa mutane ne masu son tara ‘ya’ya da yawa. Domin sukan sakar wa matansu su yi ta haihuwa ba iyaka, har sai sanda Allah ya tsayar da ita. Ko da za su haifi ‘ya’ya nawa, murna ake yi da farin ciki da yi masu ɗawainiya da kuma barka da arziki.

A tatsuniyar Na-goma, ma an kuma nuna: “Wata rana, an yi wani mutum wanda yake da ‘ya’ya goma……”(Yahaya,1971:34).

Addu’a da Neman Magani

Saboda ƙaunar da Hausawa ke yi wa haihuwa, ya sa duk arziƙi ko sarauta ko muƙamin da mutum yake da shi, idan ba shi da ‘ya’ya banza ne. Kuma irin waɗannan mutane sukan yi duk ƙoƙarin da za su iya don su sami haihuwa domin su sami magada kuma su bar baya. Sukan bi hanyoyi da dama wajen ganin sun sami haihuwa. Waɗansu sukan yi addu’a ko su sa malamai su yi masu. A tatsuniyar Wata ‘Yar Sarki an nuna:

 An yi wani Sarki mai jama’a da yawa da kuma arziƙi. Shi dai Allah bai taɓa ba shi haihuwa ba. Kullum yana ta roƙon Allah ya ba shi ɗa namiji. Idan ya je masallaci bayan an ƙare salla, sai ya ba malamai kuɗi su taya shi roƙon Allah don samun ƙaruwa’(Ɓaɓura,1986:83)

Wasu kuwa maganin haihuwa suke karɓa daga wajen masu maganin gargajiya don ko sa dace da samun ‘ya’ya. Tatsuniyar Ɗan Sarki ya Zama Maciji ta nuna haka:

Wani mutum ne dai yana da matansa uku, ya fi son biyu daga cikin matan nasa. Ɗaya ba ya son ta sosai---. To shi dai wannan mutum ba shi da ɗa ko ‘ya ko ɗaya. Ya damu saboda rashin ‘ya’ya. Ana nan, ranar nan, sai ya ji ana tallan maganin haihuwa. Sai ya sayo wa matan nan guda biyu waɗanda yake so, ya ƙi sayo wa Bora (Yahaya, 1972:9

Ƙara Yin Aure Don Haihuwa

Wani lokaci kuwa wasu mazajen sukan ƙara aure ne don burin ko za su sami ƙaruwa, idan ya zama mace ko matan da suke tare da su ba su haihu ba. Misali a tatsuniyar Wani Sarki da Matansa an bayyana:

Wani Sarki ne mai mata uku, amma Allah bai taɓa ba shi haihuwa ba. Ana nan, wata rana sai ya nemi shawarar fadawansa a kan abin da ya kamata ya yi saboda wannan rashin haihuwa. Sai suka ce ya kamata ya ƙara aure. Shi kuwa ya ɗauki shawararsu, ya sa aka a budurwa kyakkyawa ya aure ta. Bayan‘yan watanni sai Alllah Ya ba ta ciki”. Labari ya gama ko’ina, matar Sarki tana da ciki (Usman, 2012: 10).

A wasu lokutan kuwa, akan yi rashin dace, neman haihuwa kan jefa wasu cikin hallaka, musamman mata kamar yadda ya faru ga kaza a tatsuniyar Kaza da Malam:

Wata kaza ce wadda ba ta taɓa haihuwa ba. Kullum ba ta da wani aiki sai roƙon Allah Ya ba ta haihuwa. Duk inda ta ji labarin wani malami ko boka sai ta yi can jiki na rawa, amma har yanzu ba ta dace ba. Ana nan cikin wannan hali sai kaza ta ji labarin wani shahararren malami wanda ya ƙware wajen ba da magani kala-kala. Kaza ta ce, ban ga ta zama ba, nan take ta garzaya wajen malam. Nan dai malam ya ce ma kaza ta je ta samo gishiri da magi da ruwa da kayan miya da duk abin da ake haɗawa wajen dafa kaza. Bayan ta kawo masa ne, ya buge ta ta faɗa cikin wuta, ya yi sauri ya yanka ya kai ma amaryarsa ya ce, ta haɗa masu farfesu. (Koko, 2009:114).

A tatsuniyoyin da suka gabata, an nuna yadda Hausawa suka ba wa haihuwa muhimmanci. Inda har waɗansu sukan yin addu’a ko su sa malamai su yi masu don samun haihuwa. Wasu kuma maganin haihuwa suke karɓa daga wajen masu bayar da magungunan gargajiya. Yayin da wasu mazajen sukan ga ƙara aure shi ne mafita, idan har matan da suke tare da su ba su haihuwa.

Matsalar Haihuwa

Sanin kowa ne Allah ne mai bayar da haihuwa ga wanda Ya so, Ya kuma hana wanda Ya so, ba domin ya yi masa wani laifi ba. Sau da yawa malaman addini Musulunci kan faɗakar da waɗanda ba su haihu ba cewa, hakan da Allah Ya yi masu shi ya fi dacewa da su, kuma cikin RahamarSa akwai kyakkyawan tanadin da Ya yi masu a ranar gobe kiyama. Amma duk da haka, a wasu lokutan Hausawa kan shiga halin damuwa da takaici, musamman idan tsufa ya zo, ba su haihu ba.

Tatsuniyar Mai Mazare Uban Lawaya, ta nuna haka lokacin da yake ba wa ‘yar tsohuwa labari;

Ni ne dai tun ina da mata, har na rabu da su duk, har ga shi tsufa ya kusan kama ni Ubangiji Allah bai ba ni haihuwa ba. Ni ko na ce, Allah Allah ka hore mini ko da ɗan ƙurji a guiwa mana wanda zan samu ɗa da shi, in ga ƙwai na a duniya...(Yahaya, 1974:55)

A mafi yawan lokuta Hausawa sukan jingina al’amarin rashin haihuwa ga mace. Sukan yi ƙoƙarin jefa matar da ba ta haihu ba cikin takaici da baƙin ciki. Ta hanyar tsangwamar ta da munanan kalamai da kuma yi mata habaice-habaice da gori. Sannan irin waɗannan mata kan fuskanci matsi daga wajen iyayen miji da ‘yan’uwansa da kishiyoyi, wani lokacin ma har daga wajen maigidan da kuma jama’ar gari.

Tatsuniyar Juya ta Sami Gagare ta fito da irin takaicin da matan da ba su haihu ba ke ɗanɗana, har a kan riƙa ya masu da magana da habaice-habai da kiransu da juya:

“Akwai wata mata da mijinta, ba su taɓa haihuwa ba. Sai ‘yan gaza-gani a garinsu suka shiga cewa ita juya ce ba mai haihuwa ba, irin waɗannan maganganu kuwa sukan dame ta” (Usman, 2012:15).

Idan ita kaɗai ce matarsa, akan matsa masa ya ƙara aure, wanda idan har kishiya ta zo ta haihu, ai shi ke nan, sai matsi da tsanani da habaici da gori ya yi gaba. A wasu lokutan kuma idan uwargida ta ga amarya ta zo daga baya za ta haihu, ita kuwa ko ɓatan wata ba ta taɓa yi ba, sai ta ɗaga hankalinta. Idan kuma su biyu ne, sai su haɗe wa amaryar kai, su matsa mata. Wani lokacin ma har su yi ƙoƙarin zubar da cikin ko kuma idan an haifi ɗan su yi ƙoƙarin nakasa shi ko kuma a nuna kishi da baƙin ciki ƙiri-ƙiri a kan ɗan.

Tatsuniyar Ba-da-baki, tana ɗauke da wannan salo na muzguna wa matar da ta sami juna biyu. Hakan ya fito fili a lokacin da Ba-da-baki ke bayyana wa Sarki cewa:

“Ni ce dai Sarkin garin nan ya aure ni. To da man yana da matansa da ‘ya’ya. To da kishiyoyina suka ga ina da ciki sai suka sa mini tsama. Suka dame ni. Sai na ce a raina tun da yake haka ne na daina yin magana da kowa a gidan, sai na haihu na samu lafiya tukuna” (Yahaya, 1974:46).

Amma kuma sai suka ci gaba da ƙulla mata makirci iri-iri ta hanyar kashe dabbobin Sarki suna cewa ita ce, har ta kai ga sun kashe ɗan Sarki wanda ya fi ji da shi. Duk suka ce ita ce. Daga ƙarshe dai Sarki ya ce da fadawa su kai ta bayan gari su kashe ta.

Tatsuniyar ‘Yammata Huɗu Masu abin Mamaki, ita ma ta nuna yadda matar Sarki ta shiga ɗimuwa da takaici da baƙin ciki yayin da amaryarsa ta durƙusa ta haifi ‘ya’yanta guda biyu da mace da namiji. Ɗaya da cibiyar azurfa, ɗaya da ta zinari. Amma da uwar ta tafi ɗauraya, sai kishiyar ta kama ‘ya’yan ta watsa su ta bayan gida, cikin tafasa. Ta ɗebo ƙadangaru guda biyu ta zuba mata.

Sannan a tatsuniyarWani Sarki da Matansa shi ma an nuna yadda matan Sarki suka shiga baƙin ciki yayin da suka ji labarin amaryar Sarki ta sami juna biyu. Domin su sun daɗe a gidan Sarki ba tare da ko ɗaya daga ciknsu ta sami ko da ɓatan wata ba. Suna ganin cewa ta zo daga bayansu za ta gaje gida. Don haka, sai suka shiga neman hanyar da za su bi su zubar da cikin, amma abu ya gagara, har lokacin haihuwa ya zo. Lokacin da suka tabbatar da ta kusa haihuwa, sai suka je wurin Sarki suka nemi izini su je shan iska da saran itace a jeji tare da bayinsu. Da fari Sarki ya ce, ba za su je da amaryarsa mai juna biyu ba, amma da suka nace, sai ya bar su suka tafi jeji da ita. A dajin naƙuda ta kama ta, suka kai ta gindin bishiya, suka kwantar da ita, ta haihu. Da suka ga ta haifi ‘ya kyakkyawa, kuma ba ta cikin hayyacinta, sai suka ɗauki jaririyar suka jefa a kan bishiya. Can da rana ta yi sanyi, sai su da bayinsu suka kama hanyar gida, tare da mai jego. Suka gaya wa Sarki wai matarsa ta haifi wani ɗan itace ne, ba mutum ta haifa ba (Usman, 2012:10).

Wasu kuwa ba su iya ɓoye zafin rashin haihuwa, musamman ga ‘ya’yan kishiyoyinsu. Sukan nuna tsana da halin ko-in-kula ga ‘ya’yan. Tatsuniyar Wasu Kishiyoyi Biyu, tatsuniya ce da ta ƙunshi wasu kishiyoyi guda biyu ɗaya tana da ɗa ɗaya, ɗayar kuma ba ta taɓa haihuwa ba, kuma ita ce uwargida. Dukkansu suna da randar ajiye ruwa. Ran nan sai uwargida ta fita, sai yaron amarya ya kama kuka ruwa yake so. Ta duba randarta ashe babu ruwa, sai ta je wajen randar uwargida ta ga ruwa, sai ta ɗiba ta ba yaronta ya sha. Amma saboda zafin cewa, ita ba ta haihu ba, sai ta ƙeƙasa ƙasa ta ce, sai an biya ta ruwanta. Kuma ga shi ranar ba a zuwa ɗibar ruwa gulbin garin. Ta ce kuma sai wannan ruwan take so don kawai ta ƙuntata mata. (Koko, 2009: 48).

Wani lokacin kuma akan ɗauki ɗa a ba wa matar da ba ta haihuwa riƙo, a nan ma ba ta tsira ba, domin za a riƙa cewa, za ta raba ɗa da mahaifiyarsa. Ko kuma ma masu ɗan su karɓe abinsu rana tsaka. Tatsuniyar Dagaci da Malaminsa ta fito da kyakkyawan misali:

“An yi wani dagaci a wani gari da matarsa, to amma matar ba ta taɓa haihuwa ba. Ba tare da saninsa ba, wata rana matar wani babban malami ta je wurin matar dagaci hira a gidansa. Suna cikin hira sai matar dagacin ta fara ba matar malamin labarin tashin hankalin da take ciki na rashin haihuwa. Kuma ga shi maigidanta, watau dagacin, ya ce, yana son ya sami ‘ya’yan da za su zo su gaje shi. Kuma ya ba matar tasa wasu ‘yan watanni, idan ba ta sami ciki ba zai kore ta, ya auro wata matar. Wannan barazana ce fa ta sa matar dagaci ta fara kuka da baƙin ciki. Amma da matar malami ta ji yadda labarin yake, sai ta ce, da matar dagaci, tana da ciki wata biyu, amma idan Allah Ya sauke ta lafiya, za ta kawo wa matar dagaci abin da ta haifa, domin ta nuna wa maigidanta cewa ta haihu. A ranar da matar malami ta haihu kuwa, kamar yadda aka yi alƙawari sai ta ɗauki jaririnta ta kai wa matar dagaci, ba tare da kowa ya sani ba. Matar dagaci ta ci gaba da renon jaririn matar malam. Amma ana gobe suna sai matar malami ta dawo ta ce, mijinta ya ce, shi ba zai ba da ɗansa ba, saboda haka a dawo masa da ɗansa. Haka dai matar dagaci ta sha fama da roƙon matar malami da ta rufa mata asiri, ga shi gari duk ya ɗauka cewa, ta haihu, amma ta ƙi yarda. Daga ƙarshe dai ta karɓi ɗanta ta tafi gida. Matar dagaci ta rasa yadda za ta yi” (Usman, 2012:32).

Wannan kaɗan ne daga cikin baƙin ciki da takaicin da waɗanda ba su haihuwa ba ke ɗanɗana. Domin wasu sai sun gama wahala da ‘ya’yan, sannan iyayensu za su ƙwace su.

 Alamomin Samun Juna-Biyu

 Akwai alamomi da Hausawa ke amfani da su wajen gane mace ta samu juna biyu da suka ƙunshi zubar da yawu, ko amai, ko tsaginagini wajen cin abinci, ko canza kamanni. Amma mace da ta sami juna- biyu tana gane ta ɗauki ciki ne idan ta yi ɓatan wata. Irin waɗannan al’adu sun fito a cikin tatsuniyoyi da dama, kamar haka :

Tatsuniyar Dagaci da Malaminsa ta fito da wannan babbar alama ta gane mace ta sami juna-biyu. Ga abin da tatsuniyar take cewa :

‘Bayan’yan kwanaki sai matar Dagaci ta gaya wa Dagaci cewa ta yi ɓatan wata. Da Dagaci ya ji wannan labari, sai ya shiga murna. Ya fara faɗawa fadawansa da mutanen gari cewa matarsa tana da juna-biyu (Usman, 2012 : 30).

 Sannan yayin da aka ce mace cikinta ya girma Hausawa sukan ɗauke mata yin ayyukan wahala don kiyaye lafiyarta da ta abin da take ɗauke da shi, duk dai a tatsuniyar an nuna:

‘Saboda cikin, Dagaci ya ba da umarni a kai matarsa wani gyararren gida. Ya sa a riƙa yi mata duk abin da take so. Kuma ya ce kada ta taka ko ƙofar gida don kada ta wahala a lokacin da take renon ciki har ranar haihuwa’ (Usman, 2012: 31).

 Kula da ‘Ya’ya

 Hausawa tun ‘ya’yansu suna ciki suke ɗaukan matakan kulawa da su. Akwai wasu zaunannun al’adu da suke yi, tun daga lokacin da aka ce mace ta ɗauki ciki, har lokacin da za ta haihu. Irin waɗannan al’adu sun haɗa da goyon ciki da wankan jego da shayar da nono da reno da sauransu. Duka waɗannan hanyoyi ne na kula da abin da za a haifa da kuma ita uwar.

Bisa ga al’ada, mai ciki, akasari na fari, takan je gidansu ta haihu a can wajen iyayenta har ma ta yi wankan jego a can. Tsawon lokacin da akan ɗauka wajen goyon ciki yakan bambanta daga wuri zuwa wuri.

Tatsuniyar ’Yan Mata Masu Kamun Kifi wadda ta ƙunshi labarin wani Sarki da bai taɓa samun haihuwa ba ta fito da wannan al’ada:

 ‘To shi Sarkin bai taɓa haihuwa ba, duk sanda matansa suka ɗauki ciki, sai ya zube. Ran nan bayan ‘yan shekaru da auren Marainiya da Sarki ya tara matansa, bayan ya tabbatar kowace tana da ciki. Ya ce da su kowacce ta tafi gidan iyayenta, kuma kada ta dawo sai ta haihu (Usman, 2012:57).

Wankan jego al’ada ce da Hausawa suka ɗauka da muhimmanci domin sun ɗauka cewa dole ne a yi wankan jego, in har mace ba ta yi ba takan ɗanyace. Wato takan kumbura ta yi ta fama da rashin lafiya. Dangane da tsawon lokaci da akan ɗauka wajen yin wankan kuwa, yakan bambanta daga wuri zuwa wuri. Sai dai, ba yakan gaza kwana arba’in ba. A waɗannan kwanaki akan yi wanka safe da yamma.

 Tatsuniyar Ba-da-Baki ta nuna yadda ta yi wankan jego. Ga abin da tatsuniyar take cewa:

  ‘Sai ran nan ta haifi ɗanta namiji. Ta je ta samo itacenta na wanka ta ɗora ruwan wanka a wuta. In ya tafasa ta kwashe ta kai ban-ɗaki ta yi wanka (Yahaya, 1974:48).

Sannan idan mai jego ta yi arba’in, wato ta gama wankan jego takan je gidan iyaye da ‘yan’uwa yawon arba’in. A tatsuniyar Ɗandamariye ma Yagunamu da ta haihu ta yi arba’in, sai ta je ta ga iyayenta domin su ma su ga abin da aka haifa (Koko, 2009: 88).

A Bahaushiyar al’ada uwa ita take ba wa jariri nononta, har sai ya kama abinci ya bari don kansa. Mata sukan shayar da ‘ya’yansu lokaci mai tsawo, domin wasu sukan kai har shekara uku kafin su yi yaye.

Tatsuniyar Abotar Zaki da Mutum ta nuna mata Hausawa su suke shayar da ‘ya’yansu nono: “ Idan ta sami abinci ta ci sai ta dawo cikin kogon nan ta ba ɗanta nono ya sha”(Koko, 2009:39).

Tatsuniyar Wata Tsohuwa da Aljana, shi ma an nuna yadda tsohuwa take shayar da ɗanta:

“Yanzu ga shi Sarkin garin ya ji labarin haihuwarki, ya sa an zo an ɗauke miki ɗanki, amma ka da ki ji kome. Ɗanki duk lokacin da y yi motsi zan ɗauko miki in kawo shi gurinki ki ba shi mama” (Yahaya 1977: 6).

 Sannan su dai matan suke kula da kuma renon ‘ya’ya tun suna jarirai har zuwa girmansu. Tatsuniyar Kura da Zomanya ta nuna:

“A can cikin wani ƙungurmin daji akwai wata zomanya mai ciki, wadda gidanta yake kusa da na wata kura, ita ma mai juna biyu. Suna zaman lafiya da junansu irin na maƙwabta. Wata rana sai zomanya ta je wurin kura ta ce mata: “Kin ga ni da ke mun kusa haihuwa, ya kamata mu nemi wurin da za mu rinƙa ɓoye ‘ya’yanmu”. Sai kura ta ce: “E, gaskiya ne, to bari mu tona rami babba domin mu saka ‘ya’yanmu a ciki’ (Usman, 2012: 14).

Haka kuma a cikin tatsuniyar ‘Yammata Huɗu Masu Abin Mamaki, nan ma an nuna yadda ɗaya daga cikin ‘yammatan da ta haifa wa Sarki ‘ya’ya biyu ta rene su: “Tana renon ‘ya’ya tana renon ‘ya’ya har Allah Ya raya su”(Yahaya 1977: 33).

Wannan ya nuna yadda mata ke reno da tattali da adana ‘ya’yansu.

Kammalawa

Haihuwa mai daɗi, ‘ya’ya ababen ƙauna da alfahari da tunƙaho. Waɗanda Allah Ya ba wa Allah Ya raya masu, Ya yi masu albarka. Waɗanda kuma Allah bai ba su ba, Allah Ya ba su, idan ba sun alheri ne a gare su. Idan kuwa akasin haka ne, to, Allah Ya yi masu zaɓi ma fi alheri. Takardar ta yi tsokaci ne a kan halayyar Hausawa ta son samun magada, tare da fito da hanyoyi daban-daban da sukan bi wajen ganin sun sami magadan. Da kuma hanyoyin da sukan bi wajen kulawa da kuma renon abin da Allah Ya ba su. Duk an yi waɗannan ne ta hanyar nazarin tatsuniyoyin Hausa. Tabbas tatsuniyoyi madubi ne da suke haska rayuwar al’umma gaba ɗaya.

Manazarta

Adamu, M. T. (2015). Haihuwa Da Suna a Bahaushiyar Al’ada. Kano: Salma A’aruf Publishers.

Alhassan da Wasu (1982). Zaman Hausawa. Institute of Education, ABU Zaria.

Ɓaɓura, S.A. (1986) “Narrator As Interpreter: Stability and Ɓariatoin in Hausa Tales”. Ph. D. Thesis. London: University of London.

Ɗangambo, A. (1984) Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kano: Triumph Publishing Company.

Ibrahim, M. S. (1982) “Dangantakar Al’ada da Addini: Tasirin Musulunci Kan Rayuwar Hausawa”. Kundin Digiri na Biyu. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya Kano: Jami’ar

Koko, H.S. (2009) Jagoran Nazarin Tatsuniya. Sakkwato: Mathi Production.

Madauci, I. da Wasu (1968) Hausa Customs. Zaria: N.N.P.C.

Muhammad, Y.M. (2003). Adabin Baka. Zariya:ABU Press Ltd.

Umar, M. B. (1980). Al’adun Haihuwa a Ƙasar Hausa. Zaria: Hausa Publications Center.

Umar, M.B. (1987) Dangantakar Adabin Baka da Al’adun Garagjiya. Kano: Tofa Commercial Press.

Usman, B. (2012) Taskar Tatsuniyoyi. Kano: Gidan Dabino Publishers.

Yahaya, I.Y. (1971) Tatsuniyoyi da Wasanni na 1-4. Ibadan: Oxford University Press.

Yahaya, I.Y. (1972) Tatsuniyoyi da Wasanni na 5-6. Ibadan: Oxford University Press.

Yahaya, I.Y. (1972) “The Style and Content of a Hausa Tale”. A cikin

 Harsunan Nijeriya Vol. II. Kano: Jami’ar Bayero.

Yahaya, I.Y. (1974) Labarun Gargajiya na 1. Ibadan: University Press

Yahaya, I.Y. (1977) Labarun Gargajiya na 2. Ibadan: Uniersity Press

 Degel Journal

The official website of the DEGEL Jounal is https://www.degeljournal.com

Post a Comment

0 Comments