Ticker

6/recent/ticker-posts

Gurbin Aure a Rayuwar Hausawa

Daga

Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani

Aure a Kunshiyar Karin Magana

Aure yana da babban matsayi a wurin Hausawa. Hasali ma, al’adar Hausawa ba ta lamunci mu’amalar saduwa tsakanin namiji da mace ba sai ta dalilin aure. Dalili kuwa shi ne ta hanyarsa ne ake samar da al’umma halastacciya bisa mizanin al’ada. Bugu da ƙari, wani ma’auni ne da ake auna kamalar mutum da shi a wasu lokutan. Rashin aure abun ƙyama ne a idon Bahaushe. Dalilin haka ne ma ya haifar da al’adar nan ta tsangwamar gwauro/gwabro da gauruwa/gwabruwa a wasannin tashe da ake gudanarwa a cikin watan azumi.

Alhassan da wasu (1982 sh. 9) sun jajjada matsayin aure ga Hausawa yayin da suka bayyana ɗaya daga cikin amfaninsa da cewa: “Ana yin sa ne saboda abin da aka haifa ya sami asali, da mutunci, da kiwon iyaye.” Aure shi ne tushen samuwar iyali wanda hakan yakan haifar da zuri’a ko dangi tsarkakakka. Daga nan ne akan samu iyaye da yayye da ƙanne da sauran ‘yan’uwa kamar yadda Malumfashi da wasu (2000 sh. 65) suka bayyana.

Manazarta

Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449 

Post a Comment

0 Comments