Daga
Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani
Duk da cewa asalin aure abu ɗaya ne, masana suna bayar da rabe-rabensa ta la’akari da abubuwa daban-daban. Akan yi la’akari da yanayin neman auren ko ɗaura shi ko yanayin zamantakewar aure domin saka shi a wani rukuni na musamman yayin samar da rabe-raben aure. Daga cikin fitattun ire-iren auren Hausawa akwai:
1. Auren Soyayya
Aure ne wanda namiji da mace sukan ƙulla dangantakarsu ta soyayya da juna
sannan iyayensu su amince a yi aure. Nau’in ya fi shahara bayan shigowar
Musulunci ƙasar Hausa da kuma musamman lokacin da aka samu tasirin zamani a rayuwar
Hausawa. Gabanin wannan lokaci, sau da dama akan gina soyayya ne a gidan aure
(bayan an ɗaura).[1]
2. Auren Zumunta/Zumunci
Aure ne na ‘yan’uwa, dangin uwa ko na uba. Akan nema wa yaro yarinya daga
cikin dangin uwa ko na uba. Wani lokaci akan yi hakan ba tare da an shawarci
yaron ko yarinyar ba. Irin wannan aure ana yin sa ne don ƙara ƙarfafa
danƙon zumunta tsakanin ‘yan’uwa. Akwai lokutan da aka kama wa yaro yarinya tun tana jaririya. Akan ce an
yi wa wane kamu. Idan irin haka ta faru, tun suna yara ƙanana mahaifiyar yaron
ko kakarsa (ko wata cikin dangi) za ta riƙa tura kyaututtuka zuwa ga yarinyar da
cewar yaron ne ya bayar da toshi.[2]
Zuwan addinin Musulunci bai dakatar da auren zumunta ba. Hasali ma, addini
ya kawo bayanin waɗanda aure ya halarta a tsakaninsu, da kuma waɗanda
aure bai halarta ba a tsakaninsu sakamakon kusanci na jini.
Dangogin da
Aka Halatta a yi Aure da Su
A Musulunci, an halatta a yi aure da
kusan dukkanin dangogi, ban da waɗanda aka ambata a matsayin haramun. Mafi yawan dangogin
da Musulunci ya halatta a yi aure da su su ne:
a.
'Yan uwa na
nesa (misali, 'yan uwan mahaifi ko mahaifiyar).
b.
Mutanen da
ba dangi ba ne.
c.
Mutanen da
ke da dangantaka da kai ta hanyar shayarwa, amma ba a matakin da ya haramta
aure ba.
Dangogin da
Aka Haramta a yi Aure da Su
Allah (SWT) ya bayyana waɗannan
dangogi a sarari a cikin Alƙur'ani Mai
Girma. Haramcin ya shafi dangantaka ta jini, dangantaka ta surukuta, da kuma
dangantaka ta shayarwa.
Ga ayar da take bayani dalla-dalla kan
waɗanda aka haramta a yi aure da su:
"وَلَا تَنكِحُوا مَا
نَكَحَ آبَاؤُكُم مِّنَ النِّسَاءِ إِلَّا مَا قَدْ سَلَفَ ۚ إِنَّهُ كَانَ
فَاحِشَةً وَمَقْتًا وَسَاءَ سَبِيلًا (22) حُرِّمَتْ عَلَيْكُمْ أُمَّهَاتُكُمْ
وَبَنَاتُكُمْ وَأَخَوَاتُكُمْ وَعَمَّاتُكُمْ وَخَالَاتُكُمْ وَبَنَاتُ الْأَخِ
وَبَنَاتُ الْأُخْتِ وَأُمَّهَاتُكُمُ اللَّاتِي أَرْضَعْنَكُمْ وَأَخَوَاتُكُم
مِّنَ الرَّضَاعَةِ وَأُمَّهَاتُ نِسَائِكُمْ وَرَبَائِبُكُمُ اللَّاتِي فِي
حُجُورِكُم مِّن نِّسَائِكُمُ اللَّاتِي دَخَلْتُم بِهِنَّ فَإِن لَّمْ تَكُونُوا
دَخَلْتُم بِهِنَّ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ وَحَلَائِلُ أَبْنَائِكُمُ الَّذِينَ
مِنْ أَصْلَابِكُمْ وَأَن تَجْمَعُوا بَيْنَ الْأُخْتَيْنِ إِلَّا مَا قَدْ سَلَفَ
ۗ إِنَّ اللَّهَ كَانَ غَفُورًا رَّحِيمًا (23)"
(Suratul
Nisa'i, aya ta 22-23)
Fassarar
Ayar:
“Kada ku
auri waɗanda ubanninku suka aura, sai dai abin da ya gabata,
lalle shi ya kasance alfasha da abin ƙyama,
kuma hanya ce marar kyau. An haramta muku (auren) uwayenku, da 'ya'yanku mata,
da 'yan'uwanku mata, da gwaggwayenku/gwaggwanninku mata, da 'yan'uwan uwayenku
mata, da 'ya'yan 'yan'uwanku maza, da 'ya'yan 'yan'uwanku mata, da uwayenku waɗanda
suka shayar da ku nono, da 'yan'uwanku mata ta hanyar shayarwa, da uwayen
matanku, da 'ya'yan matanku mata waɗanda suke ƙarƙashin
kulawarku daga matanku waɗanda kuka kusance su. Amma idan ba ku kusance su ba, to
babu laifi a kanku (idan kuka auri 'ya'yansu). Haka nan an haramta muku (auren)
matan 'ya'yanku maza na jinin jikinku, kuma ba a halatta a haɗa
'yan'uwa mata biyu a matsayin mata a lokaci guda ba, sai dai abin da ya gabata.
Lalle Allah ya kasance Mai gafara ne, Mai jinƙai.”
Rarrabuwar
Haramcin Aure
Bisa ga wannan aya, dangogin da aka
haramta a yi aure da su sun kasu kashi uku:
i. Haramcin
da Ya Shafi Dangantaka ta Jini (Nasabi):
Uwaye:
Uwa, kaka (uwar uba ko uwar uwa), da kakarta
'Ya'ya
Mata: 'Ya'ya mace, jikanya, da 'yar jikanya
'Yan'uwa
Mata: 'Yar'uwa mace na jini, ko na uba, ko na uwa.
Gwaggwaye/Gwaggwanni
Mata: 'Yar'uwar uba ko na kaka
Uwa da Kaka
da ‘Yan’uwansu: 'Yar'uwar uwa ko na kaka
'Ya'yan
'Yan'uwa Maza: 'Ya'yan 'yan'uwan maza
'Ya'yan
'Yan'uwa Mata: 'Ya'yan 'yan'uwanku mata
ii.
Haramcin da Ya Shafi Surukuta
Matan Uba:
Duk matar da mahaifi ya aura
Matan
'Ya'ya Maza: Duk matar da ɗanka na
jini ya aura
Uwar Mata:
Uwar matar da ka aura
'Yar
Matarka (Rabiba): 'Yar matar da ka aura, idan har ka kusance ta
iii.
Haramcin da Ya Shafi Shayarwa
Haramcin da ya shafi dangantaka ta
shayarwa yana kama da na jini. Idan mace ta shayar da wani yaro, ita ce uwarsa
ta shayarwa, kuma dukkan danginta sun zama danginsa na shayarwa. Don haka, an
haramta auren:
a. Uwar shayarwa
b. 'Yar uwa ta shayarwa
c. 'Yar uwar uba ta shayarwa, da dai sauransu
iv. Haramcin
Haɗa 'Yan'uwa Mata Biyu
Wannan haramci ne na musamman da ya zo
a cikin ayar, inda aka haramta wa mutum ya auri 'yan'uwa mata biyu a lokaci
guda (misali, 'yan'uwa mata biyu, ko kaka da jikarta).
3. Auren Tilas/Dole
Aure ne da iyaye ko maga’isa kan tilasta yaransu a yi auren bisa tilas. Ana
iya tilasta ma’auratan duka su biyu (ango da amarya), ko kuma ya kasance an
tilasta ɗaya
daga cikinsu (yayin da ɗayan
yake so). Auren dole ya ragu sosai bayan zuwan Musulunci ƙasar Hausa. Duk da haka,
akan samu misalansu jifa-jifa har zuwa yau. Musamman a wannan zamani, auren
dole yakan haifar da matsaloli da dama, ciki har da kashe kai ko kisan kai ko
shiga karuwanci, musamman ga mata.[3]
4. Auren Sadaka
Wannan nau’in aure ne da ake bayar da yarinya sadaka ga wanda za ta aura.
Yawanci an fi bayar da sadakar mace ga malami ko almajiri, don neman tubarraki.
Akan kuma bayar ga wani mutum wanda aka sadaukar wa da sadaki kuma har ma a
wasu lokutan a ɗauke
masa wahalhalun ɗawainiyar
bukin aure. A al’ada, wani lokaci irin wannan aure akan ɗaura shi ne da mai suna Muhammadu,
sa’annan a yi ta yawo da matar gida-gida har a dace da mai son sadakar, wanda
kuma yake da damar yin auren.[4]
A yau, wannan al’ada ta ja baya sosai. Auren sadaka ya ƙaranta
matuƙa sakamakon wayewar zamani da guguwar ‘yanci. Ko ba komai, addini bai bayar
da damar tilasta wa mace auren wadda ba ta so ba. Dole ne a samu amincewarta
kafin ɗaura
mata aure da wani.
A cikin Musulunci, babu shakka cewa auren dole haramun ne. Musulunci ya bai
wa mace cikakken 'yanci da 'yancin zaɓe a kan wanda take so ta aura. Babu wani uba, ko
waliyyi, ko wani mutum da ke da ikon tilasta wa mace aure. Wannan ra'ayi an
tabbatar da shi ta hanyar hadisai ingantattu na Manzon Allah (SAW). Misali
"قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: لا تُنْكَحُ الأَيِّمُ
حتى تُسْتَأْمَرَ، ولا تُنْكَحُ البِكْرُ حتى تُسْتَأْذَنَ. قالوا: يا رسولَ
اللهِ، وكيف إذنها؟ قال: أَنْ تَسْكُتَ"
Fassara
Manzon Allah (SAW) ya ce: "Ba za a aurar da
bazawara ba sai an nemi umurninta, kuma ba za a aurar da budurwa ba sai an nemi
izninta." Sai suka ce, "Ya Manzon Allah, yaya izninta yake?" Sai
ya ce: "Shirunta shi ne izninta."
Bayanin Hadisin
Wannan hadisi yana nuni da cewa, duk macen da za a aurar, dole ne a nemi
ra'ayinta. Wannan ya haɗa da
budurwa da kuma bazawara. A wajen budurwa, alamar yardarta shi ne shiru, saboda
kunya da take hana ta faɗa a
fili. Amma idan ta faɗi
ra'ayinta a fili ko ta nuna rashin amincewarta, dole ne a girmama hakan.
Matsayin Auren Dole a Mahangar Fiqihu
Malaman Fiqihu na Musulunci sun haɗu a kan cewa idan mace ta nuna rashin amincewa da
aure, auren bai inganta ba. Idan har waliyyi ya tilasta mata, kuma aka ɗaura auren, to wannan auren ɓatacce ne kuma mace tana da haƙƙin
zuwa gaban alkali don neman soke auren.
Wannan yana nuna cikakken kariya da haƙƙin zaɓi da Musulunci ya bai wa mata, wanda ya
bambanta da al'adu da tsarin zamantakewar wasu al'ummomi a lokutan baya.
5. Auren Soyayya
Wannan shi ne auren da aka saba da shi. Wato aure ne da ake bin dukkannin
matakan da al’ada suka tanadar tun daga kan nema har zuwa ɗaurin aure da tarewa. Akan yi duk wani abu
da aka saba yi a kowane lokaci, misali:
a.
Kayan toshi
b.
Gaisuwar uwa da uba
c.
Lefe
d.
Kuɗin
aure da/ko sadaki
e.
Sayan baki
A ɓangaren
gidan mata, su ma sukan yi hidindimu na kashe kuɗi. Daga ciki har da kayan ɗaki da kayan gara. Abubuwan da ake
gudanarwa da yadda ake gudanar da su a wannan nau’in aure suna da alaƙa da
arzikin ma’auratan.
6. Auren Jari
Aure ne da akan yi shi don nuna kwaɗayi, wato son abin duniya kamar kuɗi ko muƙami. Akan auri mace
kawai ne don kuɗinta
ko muƙaminta, ko kuɗin
iyayenta da maga’isanta ko matsayinsu, ba wai don tsantsar so da ƙauna
ba. Wannan wani nau’in aure ne da mafi yawan lokuta maza kan ƙulla
shi domin cimma wani buri na rayuwa. Duk da haka, su ma mata sukan yi auren
jari. Suna iya auren mutum domin kuɗinsa, ko da kuwa tsoho ne.[5]
7. Auren Ɗiban Wuta/Kashe
Wuta/Kisan Wuta
Wannan nau’in aure ne da ake ƙullawa ba don zama na dindindin ba. Addinin
Musulunci ya zo da tsarin sakin aure. Yayin da aka yi saki da suka kai uku (3),
to matar ta haramta ga wannan miji. Abin da zai sake halarta aure a tsakaninsu
kawai shi ne idan ta je ta yi wani auren bisa sunna, sannan dalili (ba na shiri
ba) ya sa auren ya mutu. A wannan gaɓa ne take da damar sake komawa gidan tsohon
mijinta da ya taɓa yi
mata saki uku.
Mutane suna amfani da wannan dama a matsayin dabarar komawa gidan miji
bayan an yi saki uku. Sukan yi hakan ta hanyar haɗa baki da wani mijin na daban, a inda za a
yi auren wucin gadi. Ba da jimawa ba bayan sabon auren (misali kwanaki ko makonni
ko watanni kaɗan),
mijin zai saki matar domin ta koma gidan tsohon mijinta (wanda ya yi mata saki
uku). Wannan shi ake kira auren kisan wuta.
Auren kisan wuta yana iya faruwa ta fuskoki daban-daban, ciki har da:
a.
Tana iya kasancewa matar da tsohon mijin da kuma
sabon mijin da za ta aura duk sun san da cewa auren kisan wuta ne.
b.
Tana iya kasancewa tsohon mijin ne kawai yake da
masaniya, sai ya haɗa baki
da wani namiji daban domin ya auri matar, sannan ya sake ta bayan lokaci kaɗan, domin shi kuma tsohon mijin ya sake
auren ta.
c.
Tana iya yiwuwa matar ce kawai take da masaniya.
Za ta auri wani namiji, sannan ta kashe auren bayan lokaci kaɗan domin ta koma gidan mijinta. Tana kuma
iya haɗa baki
da wanda za ta aura ɗin
domin su yi auren wucin gadi domin ya sake ta bayan wani lokaci wanda hakan zai
ba ta damar komawa gidan mijinta.
A wasu lokutan, akan biya namijin da zai auri mata da sunan auren kisan
wuta. An samu lokutan da taƙaddama takan kai har kotu a inda wanda ya yi auren
kisan wuta ya tsaya kai da fata cewa shi ba zai sake matar ba.
8. Auren Dangana-Sanda/Jingina Sanda/Ɗauki Sandarka
Wannan nau’in aure ne a inda matar take zama a gidanta na kanta, amma a
garin da mijin yake. Ranar kwanan ɗakin
matar, mijin yakan je gidan nata domin ya kwana. Ana ganin cewar sunan jingina
sandarka ko ɗauki sandarka ya samo
asali ne daga yadda ire-iren waɗannan
mazaje sukan je gidajen nasu da sanda – ko dai don dogarawa, ko don kariyar
kai.
Yayin da mai gida ya shiga gidan matarsa, zai dangana/jingina sandar a
jikin ɗaki ko
dai ta waje ko ta ciki. Haka ma idan lokacin tafiyarsa ta yi yayin da gari ya
waye, zai ɗauki sandarsa kafin
ya tafi.
9. Auren Je Ka da Kwarinka
Wannan nau’in aure ne a inda namiji yake auren wata mata da take wani gari
na daban. A al’adance, idan miji zai tafi wurinta ranar da take da girki, to
sai ya ɗauki
kwari ya riƙe, saboda haɗari ko
hari. Dattawa da zawarawa da masu yawan tafiye-tafiye ne suka fi yin irin
wannan aure. Abin da ya bambanta shi da auren dangana-sanda shi ne, a auren
dangana-sanda, mijin da matar a gari ɗaya suke. A auren je ka da kwarinka kuwa,
suna garuruwa daban-daban ne.[6]
10. Auren Takalmi
Wannan nau’in aure ne da yake matuƙar kama da na je ka da kwarinka. Shi
ma ma’auratan sukan kasance a garuruwa mabambanta ne. Abin da ya bambanta
wannan nau’in da auren je ka da kwarinka shi ne, mai auren takalmi yana
da takamaimain rana ko ranakun
zuwa garin matar. Yawanci akan yi auren ne a garin da mijin yake cin kasuwa ko
kuma wurin da yake zuwa sallar Juma’a (bayan zuwan Musulunci).
Masu zuwa cin kasuwa sukan kwana a rumfunan kasuwanni da sauran wurare masu
kyau da masu muni. A maimakon wannan rayuwar gararamba, mutum yakan auri wata
mazauniyar garin. Duk ranar da ya je cin kasuwa, to a can zai sauƙa.
Akwai ruwayar labarin kunne ya girmi kaka da yake nuna cewa, ana kiran wannan
nau’in aure da suna auren
takalmi kasancewar tafiyar mai nisa ce. Mai yin ta ba zai ji daɗin tafiyar ba har sai ya saka takalmi irin
wanda yake kare mutum daga ƙaya ko ƙananan abubuwan da zai iya takawa a kan
hanya.
11. Auren Ɗaukar Buta
Wannan aure ne da akan yi tsakanin dattijo da dattijuwa, musamman lokacin
da mutum ya tsufa, sha’awar saduwar aure ta fita a ransa, kuma ba shi da mata.
Yakan nemi wata tsohuwa mai ɗan ƙarfi
su yi aure don ta riƙa taimaka masa ga ayyukan yau da kullum kawai, ba
tare da iya gudanar da mu’amalar
saduwa ba. A irin wannan yanayi akan ce, “ai ya yi aure ko da don ya samu mai
zuba masa ruwa a buta.”
13. Huce Takaici/Auren Ɗiban Haushi/Auren Ɗebe Haushi
Akan samu lokutan da mace takan kasance mai matuƙar matsala da rashin
kunya ko rashin ji a gidan aure. Za ta fitini mijinta da wulaƙanci
iri-iri. A wasu lokutan, wasu mazajen da suka fuskanci makamancin wannan yanayi
sukan auro wata matar ko da auren nasu na fari bai daɗe ba. Yayin da suka tashi auren, za su
auro wadda ta fi matar tasu a kyau na halitta da na ɗabi’a da kuma asali. Wannan shi ake kira auren
huce takaici ko auren ɗiban haushi.
A wasu lokutan kuwa, a samari ake yi wa irin wannan aure. Akan yi shi yayin
da wata budurwa ta yaudari yaro ko ta ci mutuncinsa ta hanyar ƙin
auren sa bayan an daɗe ana
kitsa zancen aure, ko kuma idan iyayen yarinyar suka hana auren cikin wani
yanayi na rashin dattaku. A irin wannan lokaci, iyayen yaron za su yi gaggawar
nemo masa wata matar wadda ta fi ta farko a kyawun halitta da na hali da asali.
Wani lokaci ma akan so saurayin ya riga budurwar yin aure. Babban manufar
wannan aure shi ne huce takaici da cusa baƙin ciki ga yarinyar
farkon da/ko iyayenta.
Ana kiran wannan nau’in aure da wasu sunaye da suka haɗa da:
a.
Auren kece raini
b.
Auren ɗiban tsiwa
14. Auren Gayya
Wannan nau’in aure ne da mutum yake yi idan matarsa ta addabe shi. Yakan yi
auren kafin ya sake ta, ko kuma bayan ya sake ta amma gabanin ta gama idda.
Manufar hakan shi ne don kar ta riga shi yin aure. Ana yin wannan aure ne don huce
haushin wulaƙanci da matar ta yi masa ta hanyar maye gurbinta da wata, tun kafin ta sake
wani aure, ko ma kafin ta fita daga gidan miji. Wato dai, ya rama wannan baƙin
hali da ta nuna masa ta hanyar ramuwar gayya wadda ta fi ta gayya zafi.
15. Auren Ɓoyon Wata
Wannan nau’in aure ne da ake ƙullawa kafin azumi, a kuma rabu bayan salla. Mafi
yawa ana ƙulla irin wannan aure ne domin mata zawarawa su yi azumi a gidan aure, su
kuma maza su yi azumi tare da mata, don kaucewa tsangwamar al’adar Hausawa ta watan azumi. Al’adar kamun gwauro sananniya ce a ƙasar
Hausa, inda ake zolayar gwagware a watan azumi.
16. Auren Kangara
Wannan nau’in aure ne a inda masu arziki ko mulki suke ture talakawa. Yayin
da aka yi baikon yarinya, sai kuma wani mai kuɗi ko mulki ya yi amfani da matsayinsa
domin shan gaban wanda aka yi wa baikon domin a ɗaura auren da shi (mai arziki ko mulkin),
to akan kira wannan aure da suna auren kangara.
1.1.2
Ire-Iren Aure Ta Fuskar Ma’aurata
Bayan ire-iren aure da aka tattauna a sama a ƙarƙashin 1.1.1, ana kuma
iya samar da rabe-raben aure ta la’akari da ma’auratan
karan kansu. Wannan ya shafi nazartar waɗanda suka yi auren domin sanya su a cikin rukuni
na musamman. Ta la’akari da ma’aurata, ana iya samar da ire-iren aure da suka
haɗa da:
a.
Auren saurayi da budurwa
b.
Auren bazawari da bazawara
c.
Auren bazawari da budurwa
d.
Auren saurayi da bazawara
Masana irin su Yahaya da wasu (1992 sh. 95) sun tattauna waɗannan fuskokin aure inda suka tafi kan
cewa rukunin farkon (auren saurayi da budurwa) ya fi armashi. A irin wannan
aure ne ake shagulgulan biki masu yawa.
1. Auren Saurayi da Budurwa
Wannan aure ne da ake ƙullawa tsakanin saurayi (samrayi), (yaron da ya
balaga, amma bai yi auren fari ba) da kuma budurwa (sauraya ko samraya), wato
yarinyar da ita ma ba ta yi auren fari ba.
2. Auren Bazawari da Bazawara
Aure ne da ake ƙullawa tsakanin bazawari, wato namijin da ya saki
matarsa ko ta mutu (rasu) ko kuma yana da mata, sai dai yana buƙatar ƙarin
aure a matsayin mata ta biyu ko ta uku ko kuma cikon ta huɗu, da bazawara, wato, matar da aurenta ya
mutu, ko mijinta ya mutu ta gama idda tana zaman gida kafin ta sami wani miji.
3. Auren Bazawari Da Budurwa
Aure ne da ke gudana tsakanin namiji wanda ya yi auren fari, amma ba shi da
mata, yana buƙatar cike gurbinta, ko kuma yana da ita sai dai
yana buƙatar ƙari, da yarinyar da ba ta yi auren fari ba. Yayin da aka yi wannan aure,
matar wadda ta kasance budurwa za ta je gidansa a matsayin matar fari idan sun
rabu ne da matarsa ta faro ko kuma ta rasu. Idan kuwa yana da aure a lokacin,
to za ta je a matsayin mata ta biyu ko ta uku ko kuma ta huɗu.
4. Auren Saurayi da Bazawara
Aure ne da ake ɗaurawa
tsakanin yaron da bai yi auren fari ba da matar da aurenta ya mutu ko kuma
mijinta ya rasu. Yawanci yaro zai yarda da auren ta ne saboda tsananin so ya
yake mata ko kuma yayin da ta kasance tana da kuɗi ko wani muƙami ko daraja ta
musamman a cikin al’umma. Idan
haka ta faru, za a ce ya yi auren jari.
Tsokaci
Ko bayan waɗannan ire-iren aure da aka tattauna a sama, yana da kyau
a fahimci cewa a har kullum zamani yana sake kawo wasu sababbin nau’ukan aure.
Guda biyu da zamani ya kawo kuma ake jin amonsu a yau su ne:
a.
Auren wuf
b.
Auren de
onli (day only)
[1] Yayin da ake nazarin auren Hausawa na
gargajiya (kafin zuwan Musulunci ƙasar Hausa), akan yi amfani da lafazin “hanyoyin
mallakar mace.” Wannan yana nuni da yadda ake da hanyoyi da dama na zamar da
mace matar aure ba tare da gina neman a kan soyayya ba. Daga ciki har da (a)
tsintuwa da (b) yaƙi da (c) cire da (d) kyauta, da sauransu.
[2]
Toshi kyauta ce da namiji yake ba wa mace domin kyautatawa da nuna soyayya. Ya kamata a duba wannan ma’ana ta toshi.
Toshi kyauta ce kuwa? A sake duba lamarin!
[3]
Domin ƙarin bayani game da
matsalolin da auren dole ya haifar a wannan zamani, ana iya duba: BBC Hausa
(2018) da ASAS (2025) da Hamza (2025).
[4] Dattijuwa mai suna Tambayi ‘yar ƙauyen
Mamola na gundumar Rawayya a ƙaramar hukumar Bunguɗu ta bayyana cewa ita ma irin wannan aure
aka yi mata. A lokacin tattaunawa da ita, tana da kimanin shekaru 70 zuwa 72 a
duniya.
[5]
Irin wannan aure ne ake yi wa kirari
da “Auren jiran gado.”
[6]
Akwai ruwayoyin labarai da suke nuna
cewa, ana kiran wannan aure da je ka da kwarinka ne kasancewar mai gidan
ba a gari yake ba. Yayin da zai je garin da matarsa take, zai ɗauki
kwari da baka domin idan ya iske kwarto a gidansa ya auka masa da yaƙi.
Manazarta
Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.