𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum. malam Allah ya saka maka da mafificin alkairi, malam kawatace take cikin damuwa, damuwarta ta itace, ta kasan mace ce mai kamun Kai ga ilimi da tarbiyya, Amma Babu saurayin da yake zuwa gurinta gashi shekarunta sun Kai 25 shi ne abin yake damunta. kuma tana matukar San tayi aure, Sai Kuma take tunanin ko Don tayi digree ne shi yasa mazan suke Jin tsoron zuwa gurinta, Don Allah a tayata da addu'a.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuhu
Tabbas Akwai irin
Wannan Tunanin Na ta, Sabida da yawa Maza ba Sa Auren Macen da tayi Zurfin
Karatun zamani. musamman Ma wadda take da Matsayin Karatu na degree. Dalilin su
shi ne. Duk wadda Aka Ce tana da degree, Lalle Zaka Samu Tana da wayewar da ta
fi Karfin Tunaninsu.
Wannan lamari na
damun mutane da yawa a cikin al'umma. Kuskure ne babba don mace ta yi tunanin
cewa karatunta (Degree) ko kamun kanta ne ke hana maza zuwa wurinta. A gaskiya,
Ilimi da tarbiya ado ne ga mace, kuma a addinance, su ne manyan abubuwan da ake
duba wa mace.
Wasu mazan suna da
ra'ayin cewa mace mai ilimi ba ta cika hakuri ko saukin sha'ani a gida ba,
musamman idan mijin bai kai ta matakin ilimi ko karfin arziki ba.
Wasu samari na ganin
cewa tunda mace ta yi degree, sai wanda ya kai matsayinta ko ya fi ta zai iya
fahimtarta da kuma kula da ita yadda ya kamata.
Sannan Wasu Mazan
Suna ganin Kamar idan mace ta yi Zurfi a Karatun zamani Kamar ba zata Yiwa
Mijinta biyayya ba, Sabida zata na Kallon Sa a Rene Kamar ma Wanda bai Waye ba.
Zata dinga ganin kamar Ita kaɗai ce wayayyiya. Shi bai Waye ba.
Sannan Wasu Mazan
suna Ganin kamar wadda ta yi Zurfi a Karatun Zamani Dole Zaka Samu tayi gogayya
da Maza Kuma ba bu Ranar da zata taɓa dena gogayya da Maza. Sabida Nan Gaba ma
Aikin Gwamnati zata Nema. Wanda kuma Kamar gogaggeniyar 'ya Mace Budurwa ko mai
Aure tare da Maza, ya saɓawa Tarbiyyar
Musulunci.
Sannan wani Lokacin
Zaka Samu Akasarin Matan da sukayi Zurfi a Karatun Zamani, Zaka Samu idan Suna Ɗaukar Albashi. To fa
Mijinta Ma bai isa ya gaya mata Magana ta ɗauka ba. Sabida Tana Samun kuɗi.
Sai dai Kuma duk Waɗannan abubuwan da na
zayyano Ba Lalle ba ne ka Samu Kowacce mace ce take da irin wannan Tunanin ba.
Amma dai Maza sukan Gujewa Mace ne Sabida Tunanin Faruwar ɗaya daga Cikin Waɗannan Abubuwan da na
Lissafo Miki.
Abubuwan da kawarki
za ta iya yi don magance wannan damuwa sun hada da: Addu'a da dogaro ga Allah:
Ta ci gaba da rokon Allah Ya kawo mata miji nagari mai tsoron Allah wanda zai
fahimci darajarta. In'sha Allahu. Allah zai Kawo Mata Miji Kuma na Gari, Domin
yanzu haka wannan zancen da Nake Yi miki. Zaki Samu wani Namijin Shi Kuma irin
Waɗannan Matan ya ke So Ma'ana
wadda tayi Zurfi a Karatun Zamani, Amma dai Akasarin Maza ba su fiya son Irin
Waɗannan Matan.
A duk lokacin da
namiji ya zo, ta nuna masa cewa ita mace ce 'yar gida mai saukin kai da
biyayya, domin auren mace mai kamun kai da tarbiya burin kowane namiji ne.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.