𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum barka da safiya Mal Allah yakara ma Mal lpy da Nisan kwana Mal ban taba yin aureba Amma duk lokacinda nake soyayya da Wani duk yanda nakeson shi daga zaran yasa maganar aure to wlh Mal kamar anciremin kaya zanji kota kota bana sonshi ko kadan Kuma bazan Kara sonshiba gaskiya Mal yanzun abin yafara damuna sosae gashi iyayena nason inyi aure wslm

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuhu

Na fahimci halin da kike ciki, kuma gaskiya abin akwai damuwa da kuma rudani, musamman ma da yake iyayenki suna son ganin kinyi aure. Wannan matsalar da kike fuskanta ta zama ruwan dare kuma ana danganta ta da Jinnul Ashiq (Aljanin soyayya) ko wani nau'i na sihiri da ke hana aure. Yakan sa mutum ya tsani duk wanda zai zo maganar aure saboda aikin aljanin kenan na hana mace yin aure.

Aljanin da ke shiga jikin mutum don hana shi aure ko kuma ya dauke kansa tamkar matar ko mijin sa, yana amfani da sihirinsa ne wajen canza miki tunani da sanya miki kyamar duk wanda zai zo da maganar aure saboda tsananin kishinsa a kanki. Abin da kike ji na tsanar wanda kike so da zaran an ambaci aure tsantsar aikin Aljanin ne domin yaga ya mallake ki.

Don magance wannan matsalar da kuma samun sauki, ga wasu matakai da ya kamata ki dauka:

1. RUKYAH: ki nemi amintattun Malamai na Sunnah wadanda suka kware wajen yi wa mutane addu'o'i (Rukyah) domin karanta miki Alqur'ani. Za ki iya neman wanda aka karanta wa ayoyin Alqur'ani (Ruqyah), kina yin Wanka da Shafa Man Zaitun a jikinki.

2. ZIKIRIN SAFIYA DA YAMMA: Kada ki kuskura ki bar yin addu'o'in kariya na safe da yamma kafin rana ta fito da kuma kafin ta fadi da kuma lokacin kwanciyar bacci.

3. YAWAITA KARATUN ALQUR'ANI: Musamman Suratul Baqarah. Zaki iya sanya ta a waya ko na'ura tana yin ruruwa a cikin daki ko a gida, domin Aljanu suna gudu daga gidan da ake karanta ta.

4. TSARKI DA ADDU'A: Koyaushe ki kasance cikin tsarki (Alwala), kuma ki yawaita addu'ar neman tsari daga sharrin duk wani abu da Allah ya halitta.

5. ADDU'AR ISTIKHARA: Duk lokacin da wani yazo neman aure, ki yawaita yin addu'ar neman zabi (Istikhara) don Allah Ya nuna miki alkhairi.

6. KAURACE WA SHIGA ƊAKI KE KAƊAI: Ki daina kwana ke kaɗai adaki, Ki rage yawan zama ke kaɗai a wuri mai duhu ko shiru, domin hakan yana kara musu damar shiga jikinki da kwakwalwarki.

Ana iya samun kwararrun malaman addini wadanda za su iya duba yanayinki su ba ki hadaddun magunguna na sunnah da kuma addu'o'in da za ki rika wanka ko shafawa.

Ki yi kokarin yi wa iyayenki bayani a fili game da yadda kike ji (cewa kina da sha'awar yin auren amma wani abu na daban na hana ki) don su fahimce ki kuma su taimaka miki da addu'a da neman magani.

A halin yanzu, yayin da kike neman magani, ki rage yawan shiga zurfin zance da saurayi na soyayya na tsawon lokaci, musamman wanda zai kai ga shirin aure, har sai kin sami sauki. Ki cire tsoro da damuwa a zuciyar ki. Kada ki yanke kauna, kuma kada ki bari tsoro ya hana ki neman magani a wajen Malamai na kwarai masu bin Sunnah. Wannan jarabawa ce kuma da yardar Allah za a dace.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam