𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalam Alaikum Malam Dan Allah ina so a taimakamin da yadda zan Fidda kaina a cikin mugun halin da nake ciki, ni macece ban yi aure ba Amma nashiga tarkon soyayya hartakai an sadu dani, wanne irin Magani zan yi amfani da shi wajan tsuke gabana kada wanda ya aureni yagane cewar an yi jima'i Dani. nagode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuh
Toh, yar uwa a
kimiyance da ta fuskar likitanci, babu wani magani na musamman da zai mayar da
budurci ko kuma tsuke gaba ta yadda za ta koma kamar ba a taɓa saduwa ba.
Abubuwan da ake
amfani da su wajen tsuke gaba (Matsi) ba sa maido da fatar da ta warware, kuma
yin hakan na iya janyo wa mace cututtuka a mahaifa.
Gaba (farji) tsoka ce
mai shimfiɗa da kuma komawa
yanayinta na asali (Elastic). Bayan saduwa ta farko, gabar za ta iya komawa
yadda take ba tare da wani ya gane cewa mace ta taɓa saduwa ba, har sai
idan an yi ta saduwar akai-akai ko kuma ta haihu. Don haka, babu buƙatar shiga damuwa ko
neman magungunan tsuke gaba.
Idan wanda ya aureki
ba saurayi bane, to ki sani lalle zai iya gane cewar ke ba budurwa bace. Amma
idan wanda zai aureki saurayi ne wanda bai taɓa saduwa da mace ba, to abin da sauki,
ba lailai ba ne ya gane sabida shi baisan komai ba.
Amma duk da haka,
akwai magunan da zasu matseki kuma na hausa, ko wanene ma da kyar zai shigeki.
sadai wannan jinin na budurci bazaizo ba, sabida wanda ya sadu dake ya gama
fasashi. daman idan ya fashe ne jini yake zubowa.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.