Daga
Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani
A ma’ana ta ƙamusu, gwauro yana nufin “mutumin da ba shi da aure bayan ya taɓa yi,” (CNHN, 2006 sh. 184). Shi kuwa Muhammad (2020 sh. 84) yana da ra’ayin cewa: “Gwauro na nufin babban mutum magidanci da ya taɓa yin aure, amma kuma ya rabu da ita. Wannan rabuwa zai iya kasancewa ta hanyoyi huɗu kamar haka: Saki, mutuwa, kashe aure a kotu ko yaji. Ana kiran namiji da gwauro, in mace ce a ce mata gwauruwa (Bazawara) jam’i kuwa gwagware. Ita rayuwar, ta tsawon lokacin da gwauro ya zama ba shi da matar shi ake kira gwauranci.”
Da haka, muna iya fahimtar cewa
gwauro yana nufin wanda ba shi da mata alhali yana cikin munzalin shekarun
aure. Gwauranci/gwauranta abu ne da yake kawo tsangwama da kushe ga gwauro.
Akwai waƙar
gwauro da ake yi musamman a watan azumi, kamar haka:
Jagora: Gwauro-gwauro,
‘Y/Amshi: Gwauro.
Jagora: Mai sahur da ƙarago,
‘Y/Amshi: Gwauro.
Jagora: Buɗa baki da ƙanzo,
‘Y/Amshi: Gwauro.
Jagora: Mai filo da katifa,
‘Y/Amshi: Gwauro.
Jagora: Babu mata ɗaki,
‘Y/Amshi: Gwauro.
Bayarwa: Babu butar salla,
Amshi: Gwauro.
Jagora: Mai jiƙonsa a
leda,
‘Y/Amshi: Gwauro.
Jagora: Gwauro-gwauro,
‘Y/Amshi: Gwauro.
(Sani da Gobir, 2021 sh. 417)
Karin magana da aka gina game da
gwauro sun haɗa da:
1. Da wannan don wannan, an sa
gwauro biko.
2. Duniya da daɗi, gwauro ya samu mata.
3. Gwauro ya sha fura bale mai
mata.
4. Ikon Allah, mai gari gwauro.
5. Ina mata ga miji? In ji
shekararren gwauro.
6. Kalen magana an ce da gwauro
ina iyali.
7. Madalla, an ba gwauro ajiyar
mata.
8. Neman zance, an ce wa gwauro
ya iyali.
9. Niƙa, daka mafalkin gwauro.
10. Shiga uku, gwauro da yaye.
11. Sukunin banza, gwauro da
baraya.
12. Tuzuru, wanda ya fi gwauro ɓarna.
13. Ungwazoma maƙi zuwa
gidan gwauro.
14. Wadata shifci, gwauro da
turaka.
15. Rashin sani, karen gwauro ya
kori bazawara
A ƙasa an kawo taƙaitaccen tsokaci game da
wasu daga cikin fitattun karin magana da suka shafi gwauro:
1. Wadata shifci, gwauro da
turaka
Turaka tana nufin ɗakin da maigida ya ware don
kwanciya da ajiyar kayansa. Shifci kuma yana nufin ɗaurin yankakkiyar ciyawa wadda ake yi, don
yinta/yanta (wato, abin rufin ɗaki).
Wannan karin magana tana nuna
cewa wadatar kayan aiki ce ke sa wa gwauro ya gina wani ɗaki don amfanin kansa daban, idan ba haka ba a
mahangar al’ada ina ruwansa da yin wani ɗaki
da ya danganci maza masu aure? Don haka, wannan karin magana shaguɓe ce ga gwauro. Kuma ana
amfani da ita wurin nuna wa wani abin da ya yi bai kai ga wanan matsayin ba,
wato, ya zartar da wani hukunci ko yin wani abu wanda ba shi da hurumi a
cikinsa.
2. Sukunin banza, gwauro da
baraya
Baraya yana nufin wurin hutawar
maigida. Yana ɗaukar
ma’ana ɗaya da turaka.
Wato ɗaki ne da ake
warewa a gida inda zai kasance wurin hutu ga mai gidan.
Wannan karin maganar tana nuna
cewa wadatar arziki na dukiya ya zama marar amfani ga gwauro, don ya tanadi
irin wurin hutawar magidanta tun da shi ba mai aure ba ne. Ita ma wannan karin
maganar shaguɓe ce ga
gwauro a kan cewa, ya yi aikin banza don ya gina baraya (turaka), amma ba shi
da mata.
3. Ina mata ga miji, in ji
shekararren gwauro
Wannan karin magana tana nuna
shaguɓe ne sosai ga
gwauro ta yadda take bayyana halayya da yanayin da gwauro yake shiga ciki idan
ya daɗe bai sake wani
aure ba, da cewa har shela da cigiya da sanarwa yake yi a cikin al’umma yana
neman wata matar da zai sake aure.
4. Neman zance, an ce wa gwauro
ya iyali?
Wannan karin magana shaguɓe ne ga gwauro, domin kuwa
tun da har an san cewa ba shi da aure, bai kamata a tambaye shi yanayin iyali
ba kasancewar ba ya tare da su, sai fa idan ana so a tsokane shi ne. Wannan
karin magana tunatarwa ce, faɗakarwa
ce, haka kuma zaburarwa ce ga wani abu da ake son a tunawa mutum, wanda ya
kamata a ce ya yi amma bai ɗauke
shi da muhimmanci ba, don ya ƙi aiwatar da shi. Ana amfani da wannan
karin magana domin a nusar da mutum kan wani abu da ya kamata a ce ya gudanar
da shi, amma sai ya yi biris da shi, kuma abun nan mai matuƙar
muhimmanci ne ga rayuwarsa.
5. Ikon Allah, maigari gwauro
Ga al’adar Hausawa, Maigari kamar
Sarki ko Hakimi ko Dagaci yakan kasance mai aure, a mafi yawan lokuta ma sukan
auri mata ne fiye da ɗaya.
Don haka, abin mamaki ne ƙwarai maigari da zaman gwauranci. Ana amfani da wannan karin
magana idan wani abin mamaki ya faru inda wanda ake tsammani ya mallaki wani
abu ya kasa mallakarsa, sai wanda ba a tsammani ya mallaki wannan abun ya
mallake sa, kamar yadda aikin Koko (2011 sh. 79) ya bayyana.
6. Ba lafiya, sarkin gari babu
mata
Ga al’ada, rashin mata, ko ga
talaka, faɗuwar daraja
ne ko girma, balle sarkin gari. Ga al’adar Hausawa al’amari ne mai sosa rai da
tayar da hankali idan sarkin gari ya kasance babu mata. Ana amfani da wannan
karin magana domin a nuna damuwa ko kaɗuwa
game da wani mutum mai muhimmanci da ya rasa wani muhimmin abu na zamantakewa
da mu’amalar rayuwa.
7. Niƙa, daka, mafarkin gwauro
Niƙa da daka ayyuka ne na sarrafa ƙwayar
hatsi ko wani abinci domin samar da gari. A ƙamusun Hausa (CNHN, 2006 sh. 88) an
bayyana daka da cewa “dukan
abu da taɓarya ta daka
a cikin turmi har ya zama gari ko ya yi laushi.”
Wannan karin maganar tana nuna
cewa, gwauro koyaushe tunaninsa shi ne hanyoyin da zai bi wajen sarrafa abinci
da zai ci da kuma zullumin wahalhalun da zai fuskanta, kasancewar ya rasa matar
da take yi masa wannan hidima. Ana amfani da wannan karin magana a nuna yanayi
da ƙuncin
da mutum yakan shiga idan ya rasa wadda take gudanar masa da wani aiki wanda
shi ba zai iya yi ba, ko bai saba yi ba.
8. Shiga uku, gwauro da yaye
Yaye na nufin barin shayar da ɗa ko ‘ya nono (mama) da
mata ke yi bayan da yaro kai kimanin wata goma sha takwas ko fiye da haka. Ita
kuwa kalmar ‘shiga-uku’ tana ɗaukar
ma’anar samun kai cikin masifa da uƙuba. Wannan karin magana tana nuna irin
matsanancin halin da gwauro zai shiga idan har aka bar shi da ɗawainiyar kula da yaro
lokacin yaye, lokacin da yaro ya fi tsananta fitina saboda raba shi da abincin
da ya saba da shi. Ana amfani da karin maganar a nuna cewa mutum ya shiga
mawuyacin hali da bai saba ba.
9. Madalla, an ba gwauro ajiyar
mata
A wannan muhalli, madalla kalmar
godiya ce wadda ake amfani da ita don nuna jin daɗin
wani alheri. Wannan karin maganar tana
nuna cikakken farin cikin da gwauro yake nunawa da aka ba shi ajiyar mata. Ba
shakka, karin maganar shaguɓe
ce ga gwauro ta hanyar jingina masa abin da yake tsananin buƙata
ruwa- jallo.
Ana amfani da wannan karin magana
a yi nuni ga wani mutum wanda ya samu wani abu da yake tsananin buƙata da
kuma irin murnar da yake nunawa lokacin da ya samu wannan abu.
10. Duniya da daɗi, in ji gwauro da ya samu
mata
Shi ma wannan karin maganar shaguɓe ne ga gwauro da yake nuna
cewa gwauro zai yi matuƙar nuna farin cikinsa a lokacin da ya samu mata, har ma ya ce
duniya ta yi masa daɗi.
Ana amfani da wannan karin magana idan mutum ya sami wani abin jin daɗi, wanda yake nuna farin
cikinsa ƙarara,
wani lokaci ma har arerewa ya ke yi haɗi
da kuwa da nishaɗi,
wanda yake nuna abin nan fa bai yi zaton zai same shi ba.
11. Gwauro ya sha fura balle mai
mata
Ga al’adar Bahaushe ‘fura’ wani
abin sha ne mashahuri kuma mai muhimmanci da ake amfani da shi a kodayaushe.
Shi kuwa karin maganar tsokana ne ga gwauro, ta hanyar nuna cewa idan har shi
zai sha fura, duk da yake ba shi da mata, to ai wanda yake da mata ya fi shi
cancanta. Duk da yake yana iya sayowa, yana iya damawa domin samun sauƙi
sarrafawa a maimakon ya dafa abinci, amma ba ya samun yadda yake so, saboda ba
matarsa ta daka masa ita ba, ya dai sha yadda aka dama.
Ana amfani da wannan karin magana
a nuna cewa, idan har wani mai ƙaramar daraja zai iya samun abu, balle
mai darajar da tafi tasa, ai ba ma wani abin mamaki ba ne.
Manazarta
Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.