Daga
Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani
Wasu lokuta tsananin zafin kishin da yake gudana a tsakanin kishiya da kishiya yakan yi naso har zuwa ga ‘ya’yansu. Hakan ya haifar da samuwar wasu karin maganan Hausa waɗanda suke ƙunshe da bayanin yadda matsayin ɗan kishiya yake a mahangar wasu kishiyoyi. Ga wasu daga cikinsu kamar haka:
1. Ɗan kishiya, riƙon mai haƙuri
Kalmar ‘riƙo’ na nufin kula ko ɗaukar nauyin yin wani abu (CNHN
2006 sh. 372). Wannan karin magana tana bayanin cewa ba kowace mace take iya ɗaukar ɗawainiya da ɗan kishiyarta ba, sai wadda take da haƙuri da kuma sassauƙan kishi, kasancewarsa aiki ne
mai wuya da ya ƙunshi
tarbiyya da kulawa irin yadda za ta iya yi wa ‘ya’yan da ta haifa.
2. Babu dole, ga goyon ɗan
kishiya
Kalmar ‘goyo’ na nufin ɗaukar yaro ko mutum ko wani abu
a baya. Wannan karin maganar ya nuna muna ƙarara
cewa kulawa ko ɗawainiya da ɗan kishiya ba dole ba ne, sai rai ya so kawai za a iya yin
haka. Ana amfani da wannan karin maganar a wurin da mutum yake son ya yi
bayanin wani abu wanda ba dole ne ya aikata shi ba, kawai zai yi ne don ganin
damarsa.
3. Wayayyen hauka, goyon ɗan kishiya ga naki
Wannan karin magana tana ƙara rura wutar kishi ne a tsakanin kishiyoyi, inda take
bayyana wa kishiya cewa rashin hankali ne da kuma nuna halin ko in kula ga
kishiya ta himmantu (shagaltu) da goyon ɗan kishiya, maimakon ta mayar da
hankalinta wajen kulawa da ɗanta. Karin magana mai zuwa tana
nuni ne da cewa akwai ƙamshin
tuhuma ga kishiya a kan yi wa ɗan kishiyarta horo, ko da kuwa
domin gyaran halinsa ne da tarbiya.
4. Ban gane ba, an daki ɗan kishiya
Wannan karin magana tana bayyana muna cewa matsala ba mai ƙarewa ba ce tun da dai har
kishiya ba za ta yi kyakkyawan zato ba, bale har ta yarda da horon da
kishiyarta za ta yi wa ɗanta don gyaran hali. Mata suna
amfani da wannan karin magana gabanin fara cacar baki ko faɗa da nuna cewar ita waccan kishiyar ce ta fara tsokana
(Usman, 2006 sh. 123).
Karin magana ta gaba tana nuna shaguɓe daga kishiyar da take ganin an ci mata wani haƙƙi ko an yi mata ba daidai ba
zuwa ga kishiyar da ta yi abin da ya wuce wuri.
5. Isa da mallaka, biyan bashi da ɗan kishiya
Ga al’ada, ana ɗaukar kishiya wani abu maras
muhimmanci kuma duk wani abu da ta mallaka ana ganin sa maras muhimmanci.
Saboda haka ne karin maganar take ƙunshe
da cewa, kishiya ta ɗauki ɗan kishiya ta biya bashi da shi. Wannan karin magana shaguɓe ne
ko zolaya ga wanda ya wuce iyaka wajen amfani da abin da ba mallakarsa ba. Ana
amfani da ita ne domin fusata wanda aka yi wa karin maganar (Usman, 2005: 123).
Manazarta
Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.