Daga
Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani
Wannan gaɓa tana ɗauke ne da shimfiɗar zaman aure tsakanin ma’aurata a gidan aure, domin kuwa zaman yakan fara ne da angwanci da amarci, ko dai a tsakanin saurayi da budurawa ko bazawari da bazawara da dai sauransu. A ƙamusun Hausa (CNHN 2006 sh. 17) an bayyana ma’anar angwanci da cewa: ‘Bikin Sabon aure da Ango ke yi” shi kuwa amarci yana nufin ‘zaman aure da amarya ke yi a gidan mijinta; idan muka dunƙule waɗannan ma’anoni na kalmomin nan guda biyu a wuri ɗaya, za su ba da ma’anar cewa: Angwanci da amarci wata rayuwar zaman aure ce ta farko wadda ango da amarya suke yi, daga bayan bikin aurensu zuwa wani ɗan lokaci kafin haihuwar fari(farko).
A wannan ɓangaren, aikin ya taskace hoton
rayuwar ango da amarya daga ƙunshiyar
wasu kare-karen maganan Hausa, kamar haka:
1. Tilas, a gyara wa amarya ɗaki
Wannan karin magana tana bayyana muna al’adar Hausawa ta
kimtsa ɗakin amarya wadda ango ke yi na
gyara ɗakin da kuma kyautata shi, kamar
yin shafe (fenti kenan) da daɓe (siminti) ko ma na zamani wato
tiles domin kyautata daƙinta,
sannan kuma da al’adar nan ta jere wadda dangin
amarya suke yi na shirya ɗakin amarya da kuma ƙawata shi da kayayyaki
daban-daban kamar; jeran tasa, daro, kwanoni, tamgaram, sa kayan katako
domin inganta ɗakin da ƙawata shi, waɗanda al’ada take gudana a kansu.
Ana amfani da wannan karin magana idan ana son a nuna cewa
samar da wani abu dole ne saboda faruwar wani abu.
2. Amarya in ba ta hau doki ba, ba za a ɗora mata kaya ba
Wannan karin magana ta taskace al’adar Hausawa ta ɗaukar amarya bisa doki da sauran abubuwan hawa idan za a kai
ta gidan aure, da kuma nuna cewa ita amarya ‘yarlele ce, wadda ba a son ta
wahala. Saboda haka, ga al’ada, ba a bari ta ɗauki
wani abu da kanta zuwa gidan aurenta. Ana amfani da wannan karin magana a nuna
cewa, idan har ba a wa mutum karimcin da ya cancanta da shi ba, to bai kamata a
ɗora masa wani nauyi wanda bai
dace da shi ba.
3. Amarya ba ki laifi, ko kin karya ɗan masu gida
Wannan karin maganar ta taskace yadda al’adar nuna ƙauna ga amarya take da shi a ƙasar Hausa, wanda har ta kai ga
cewa duk abin da amarya ta aikata a lokacin amarcinta, ba kasafai ake ganin
laifinta ba ko da kuwa ta karya ɗan masu gida. A wani lafazin
karin magana cewa aka yi ko da ta kashe ɗan masu gida.
Ana amfani da wannan karin maganar a yi nuni ga duk wani
mutum wanda ba a faye ganin laifinsa ba, saboda yana cikin wani lokaci ko kuma
bisa wani matsayi.
4. Tun ana Marmari, Amarya Kan yi Goshi
Wannan karin maganar na bayyana cewa, idan har amarya za ta
yi farin jini a gidan miji to, tun a farkon zamantakewa farin jinin zai
bayyana. Kula, ɗawainiya abinci isasshe, kayan
marmari da na kwaɗayi duk lokacin amarci ake iya
samun su ba tare da gardama ba. Idan ba ta same su a wannan lokacin ba an yi ba a yi ba ke nan.
Ana amfani da wannan karin magana wajen nuna cewa wani abu
wanda ba a same shi a farkon lamari ba, to da wuya a same shi daga baya.
5. Samun wuri, amarya da aron ‘yan kunnen uwar miji
Wannan karin magana tana bayyana irin kyakkyawar zamantakewa
tare da fahimtar juna da ake samu tsakanin matar ɗa
da uwar miji a wasu lokuta. ‘Yan Kunne nau’in kayan ƙawa ne da mata suke yin ƙawa ko ado da shi a kunnuwansu,
idan ko har amarya za ta iya aron ‘yan
kunnen uwar mijinta ta yi ado da shi, lalle amarya ta samu karɓuwa sosai ga surukanta, wannan kuwa ita ce irin rayuwar da
zamantakewar aure take buƙata.
Ana amfani da wannan karin magana a bayyana cewa wani ya
samu dama ga wani na samansa ko wanda ake tsammani su sami saɓani da shi, amma sai aka ga alaƙarsu ta kyautatu.
Manazarta
Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.