Ticker

6/recent/ticker-posts

Hoton Kishi Da Uwar Kishiya a Karin Magana

Daga

Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani

Aure a Kunshiyar Karin Magana

A ganina, babban dalilin da ya sa uwar kishiya take da baƙin jini ga abokiyar kishi a zamantakewar Hausawa shi ne, a mahangar alada, ita uwar kishiya tsaye take tsayin - daka wajen kare yarta, kuma koyaushe cikin fafutukar nemar wa yar kayan faɗan da za ta yaƙi abokiyar kishin ta take domin su ga bayanta ko kuma su hana ta yin kowane irin tasiri a gidan miji, sai fa kaɗan daga cikinsu.

Kishi bai taƙaita a tsakanin kishiyoyi ba, a’a har sai da ya yi naso zuwa ga iyayensu mata, ko mene ne laifin uwar kishiya? Mai yiwuwa amsar tambayar na iya kasancewa saboda amincewar da ta yi na ɗiyarta da ta auri mijin abokiyar zama (kishiya) ko kuma domin ita uwar kishiyar a wasu lokutan takan taya ɗiyarta kishi, da dai sauran gudunmuwar da takan bayar a fagen kishi. Duk dai yadda lamarin ya kasance, karin maganar Hausa ya taskace wasu halaye da yanayin irin wannan nau’in kishi a ƙunshiyar kare-karen magana kamar haka:

1. Rabiɗin leɓo, shawara da uwar kishiya

A ƙamusun Hausa (CNHN, 2006 sh. 370), an bayyana ma’anar ‘ribiɗi’ da cewa; dakan farko da aka yi wa hatsi na fura don mayar da shi gari. Sannan aka bayyana ma’anar ‘shawara’ da ‘tattaunawa a kan wasu matsaloli tsakanin mutum biyu ko fiye. Idan aka tattara waɗannan ma’anoni za a samu sakamakon cewa, tattaunawa tsakanin kishiya da uwar kishiya domin samar mata mafita ga matsalolin da suka dabaibaye ta, wahalar da baki ne kawai da yawan magana domin ba za ta nuna mata mafitar ba, kasancewar ga al’ada, akwai tuhumar ƙiyayya a tsakaninsu.

2. Salula, shawara da uwar kishiya

Wannan karin magana ta fara ne da wata kalma (Salula) wadda sautinta yake alamta sakarci da wauta da fallasa asiri. Karin maganar tana bayyana sakarci da wautar kishiyar da ta yi shawara da uwar kishiyarta, domin kuwa ba za ta nuna mata mafitar ƙwarai ba, kuma ba za ta rufa mata asiri ba, saboda tuhumar ƙiyayya da ke tsakaninsu da kuma gudummuwar da take ba ɗiyarta a mahangar al’ada.

3. Ɓatan kai, shawara da uwar kishiya

Ɓatan kai na nufin rasa hanya daidai da ɗimuwa (CNHN, 2006 sh. 64). Wannan karin maganar tana nuna cewa shawara da uwar kishiya kauce wa hanya madaidaiciya ne tare da rashin tunani ko rashin hankali. Kasancewar an ɗauki kishiya a matsayin abokiyar gaba da ƙiyayya, haka nan duk danginta ake ganin su. Ga al’ada ba yarda tsakanin kishiya da uwar kishiyarta bare neman shawara.

Ana amfani da wannan karin magana ne, idan mutum ya yi wani abu wanda ya saɓa wa al’ada kamar yadda Usman (2005 sh. 125) ya bayyana.

4. Ba kukana ba, an ce uwar kishiya ta mutu

Kasancewar rashin kyakkyawar dangantaka tsakanin kishiyoyi, duk abin da ya faru ga wata, ba ruwan wata. Saboda haka, abu ne mai sauƙi kishiya ta ce wa kishiyarta; “Uwarta ce ta mutu ba tawa ba, mata suna amfani da wannan karin maganar su yi nuni ga wani abu wanda bai dame su ba (Usman, 2005 sh. 123).

Ita wannan karin magana, tana fayyace cewa, ita fa kishiya duk abin da ya shafe ta na alkhairi ne, ko akasin haka, to fa kishiyarta ba abin da ya shafe ta, ba ta ma sanya kanta a ciki, don ko ta yi wani abun alkhairi to za a zarge ta ne da cewa munafunci ne, don haka, bata ma cika sa kanta cikin lamarin kishiyarta ba. A zamantakewa, kamata ya yi a ce abin da ya shafi kishiyarka to ya shafe ka, amma ina, wannan ba ya yiyuwa saboda irin fassarar da aka yi wa kishiyar, don haka tun wuri take ba kanta lafiya kan duk wani abin da kishiyar ke ciki ba abin da ya sha mata kai ko ya dame ta.

Manazarta

Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449 

Post a Comment

0 Comments