Shimfiɗa
Yadda lokuta kan juya, haka nan akan sami canjin alkunyar sunayen shugabanni a tsakanin al’ummar Hausawa. Irin wannan canjin shi ya wanzar da samuwar girkakkiyar alkunya da ta keɓanta ga wasu sunayen yanka a ƙasar Hausa. A wannan fagen za a taƙaita bayayani ne daga lokacin bayyanar masu jahadi zuwa ƙarni na ishirin. Misali kafin bayyanar Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, duk mai suna Usmanu akan kira shi da Usmanu ne a ƙasar Hausa. Idan kuma yana da wani matsayi a tsakanin al’umma ko laƙabi, sai a dinga kiransa da matsayin ko laƙakabin. Bayyanar Usmanu Ɗanfodiyo da jahadinsa ya wanzar da samuwar alkunya ga duk wanda ake kira da suna “Usmanu”. A wasu sassan ƙasar Hausa, musamman a Cibiyar Daular Usumaniyya.
Alkunya Bayan Tabbatuwar Jahadin Shehu
Bayan tabbatar da samuwar
Daular Usmaniyya, an sami wasu nau’o’in alkunya da akan yi wa wasu sunayen shugabannin
da suka riƙe madafun gudanar
da mulkin sassanta. A bisa al’adar Bahaushe da kusan dukkan al’ummar
da suke zaune a farfajiyar ƙasar
Hausa, ba a kiran sunan yanka na shugaba (sarki
ko malami). Wannan ne yawanzar da sunayen alkunya
da akan sa wa irin waɗannan shugabannin, har ta kai ana kiran duk wani mai suna takwaran nasu
da alkunyar tasu har zuwa wannan zamanin.
Usumanu: Bayyanar Usman Ɗafodiyo,
matsayin iliminsa mai zurfi a kan fannonin addinin Musulunci,
ya sanya aka dinga kiransa
Shehu, wanda a Turance yake da ma’anar Farfesa.
Daga nan ne Hausawa suka dinga yi wa mai suna Usumanu alkunya da Malami ko a ce Shehu. Sakamakon
kunyar faɗar sunan domin girmamawa ga Shehu Usmanu.
Abdullahi: Ana yi wa mai sunan alkunya da Maiboɗinga, a sakamakon zaman da Malam Abdullahi Ɗanfodiyo ya yi a garin Boɗinga na tsawon watanni takwas (8) yana jiran izini daga fadar Sidi Abdul-ƙadir (R. A) kamar yadda T/Mafara (2005 p. 97) ya zo da bayanin. Wannan ne ya sa ake yi masa alkunya da Maiboɗinga, saboda kunyar faɗar sunansa. Wannan ya haifar da ake yi wa mai takwaran sunansa da alkunyar. Yayin da ya koma Gwandu da zama har Allah Ya yi masa wafati (rasuwa) a can, aka kuma rufe shi a can, kamar yadda T/Mafara (2005 p. 103) ya nuna, sai aka dinga yi masa alkunya da Maigwandu. Hasali ma duk wanda ake kira da suna Abdullahi ana kiransa da Maigwandu.
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.