Daga
Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng
Da
Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
Asalin Fulani, mutanen Fula ne. A ƙasar Mali da Senegal suke zaune. Akwai Fulanin daji waɗanda ake kira Bararoji, da Fulanin Soro. Fulalanin Soro sun fi yin tasiri ga rayuwar Hausawa, saboda suna zaune a cikin garuruwa ne. Suna karatu da karantarwa. Daga cikin irin waɗannan Fulanin ne aka samu Malam Musa Jakollo kakan Shehu Usmanu Ɗafodiyo, wanda ya zo ƙasar Hausa a cikin ƙarni na 15.
Muhimmiyar cuɗanya
a tsakanin al’ummar Hausawa da Fulani ta wanzu ne bayan Shehu
Usman Ɗafodiyo ya jagoranci Jahadin ƙasashen
Hausa. Wanda jahadin ya kasance sanadin ƙwace mulki daga hannun sarakunan Hausawa ya koma na Fulani. Suka kasance su ne shugabanni a ƙasar Hausa har zuwa farkon ƙarni na
20 (Ibrahim, 1978 p. 104). Irin wannan cuɗanyar
ta wanzar da samuwar wasu sababbin sunaye
a tsakanin al’ummar Hausawa. Misalai daga cikin irin waɗannan sunaye sun haɗa
da:
a. Baffa:
Wan uba ko ƙanin uba ko wani da yake da dangantaka ta jini da shi.
b. Dattijo: Mai mutunci da sanin ya kamata da kuma uwa uba yawan shekarun rayuwar duniya.
c. Goggo:
Yar uba ko ƙanwar uba ko wadda yake da alaƙar jini da mahaifin.
d. Kawu: Wan
uwa ko ƙanin uwa
ko wanda yake
da dangantaka ta jini da mahaifiyar.
e. Nagge:
Saniya (Ibrahim, 1978 p. 105).
Haka kuma, sakamakon auratayya
da ta auku a tsakanin Hausawa
da Fulani an sami sunayen Fulatanci
da suke ishara da jerin haihuwa.
Misalansu su ne:
Jad. na 44: Ararrun Sunayen Hausawa Daga Fulani
|
|
Sunayen Filatanci |
Ma’anarsu
da Larabci |
|
1. |
Dikko |
Auwalu
(Lawali) |
|
2. |
Sambo |
Sani |
|
3. |
Yaro |
Salisu |
|
4. |
Fate |
Rabi’u |
|
5. |
Dabo |
Hamisu |
|
6. |
Jamo |
Sadisu |
|
7. |
Gabindi |
Al-a’limu |
|
8. |
Giɗaɗo |
Al’Habibu |
|
9. |
Gyano |
Al-hayat |
|
10. |
Keranga |
Miyassir |
|
11. |
Jalli |
Maifara’a |
Naɗewa
Duk da bambance-bambance da ake samu tsakanin sunaye al’ummomi daban-daban, akan samu kamance wajen matakan samar da sunayen. Irin wannan misali ya fito a cikin abin da aka nazarta na daga matakan samar da sunayen Barebari da na Fulani kamar yadda aka tattauna a babi na huɗu da na biyar. Kamancen ya shafi samuwar sunaye a gargajiyance da kuma yadda addinin Musulunci ya yi tasiri kan lamarin raɗa su.
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.