Ticker

6/recent/ticker-posts

Alhaji Shehu Mohammed Kangiwa Turakin Kabi, Gwamnan Farar Hula na Farko a Tsohuwar Jihar Sakkwato

Jagora:

Ran nan kwanan da kayyi Yauri tun Yelwa has Sakkwato

Y/Amshi :

Dud inda mun kazo mun iske dubun mutane,

Murna sukai ka taho

Bajini na Sarkin kudu

Gwamnan jahas Sakkwato,

Shehu Kangiwa mai niyyar riƙon gaskiya

Jagora :

Kowa addu’a ɗai yakai

Y/Amshi :

Allah ya taimakeka riƙon duniya Alhaji,

Yayi ma tsari swahe dut

Jagora :

Wada kas samu duniya,

Allah baka lahira

Y/Amshi :

Ya zamo lahira tahi nan,

Bajini na Sarkin kudu

Gwamnan jahas Sakkwato,

Shehu Kangiwa mai niyyar riƙon gaskiya

Jagora :

Baba kowa Allah yab ba mutane,

Komi akai yayi mai

Y/Amshi:

Ka ƙara hamdala don komi akai yayi ma,

Bajini na Sarkin kudu

Gwamnan jahas Sakkwato,

Shehu Kangiwa mai niyyar riƙon gaskiya.

☝️☝️Suna cikin kalmomin Makaɗa Alh. Sani Aliyu Ɗandawo Yauri dake cikin waƙar da ya rerawa marigayi mai girma Alhaji Shehu Mohammed Kangiwa Turakin Kabi, Gwamnan farar hula na farko a Tsohuwar Jihar Sakkwato (Sakkwato da Kabi da Zanhwara, SOKEZA na yau) daga 1/10/1979 zuwa wafatinsa ranar 17/11/1981, a waƙar da yayi masa mai turke "Gwamnan jihar Sakkwato, Shehu Kangiwa mai niyyar riƙon gaskiya, bajini na Sarkin Kudu a farko farkon shekarar 1980.

Haƙiƙa waɗannan kalmomi sun dace da wanda aka yiwa su saboda mutum ne na mutane mai ƙwazo da jajircewa da karimci da kwatanta gaskiya da adalci kamar yadda rayuwarsa kafin da bayan zamansa gwamna ta bayyana.

Ɗan Malam Muhammad Maijimada(Malam Inuwa) ɗan Malam Yakubu ɗan Malam Muhammad Mansur Muƙaddas, an haifi Alh. Shehu Mohammed Kangiwa a garin Kangiwa hedikwatar Ƙaramar Hukumar Mulkin Arewa a Masarautar Argungu, Jihar Kebbi ta yau a ranar 13/11/1939.

Mahaifinsa Malam Muhammad Maijimada (Mal. Inuwa) mutumen garin Godiya ne dake Ƙaramar Hukumar Mulkin Gwarzo, Jihar Kano. Ya ziyarci Sakkwato a lokacin mulkin mai alfarma Sarkin Musulmi Malam Hassan ɗan Mu'azu inda ya zarce zuwa Jega daga nan kuma ya zo Kangiwa ya kafa makarantarsa ta Allo.

A Kangiwa ne ya auri mahaifiyar Alh. Shehu Mohammed Kangiwa, wato Hajiya Fatima yar Malam Ahmadu wani malamin addinin musulunci da ya taho Kangiwa  daga Ƙofar Yanɗaka Katsina.

Mahaifin Alh. Shehu Mohammed Kangiwa ya rasu a shekarar 1941 wannan shi ne dalilin tashinsa a hannun yayansa, Alh. Adamu Ɗanbaba mahaifin marigayi Ambasada Sani Kangiwa.

Yayi makarantar Allo da mahaifinsa ya bari, a tsakanin 1946  zuwa 1967, Alh. Shehu Mohammed Kangiwa yayi karatunsa na zamani na Firamare da Elimentary da Midil da Jami'a a Kangiwa da Argungu da Sakkwato da ABU Zaria da Lincoln Inn ta Ingila inda ya kammala digiri a fannin shari'a (Law).

Ya riƙe muƙamin Sakatare na musamman na marigayi mai girma Firaministan Nijeriya, Alh. Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa, ya kuma yi aiki a hukumar jiragen ƙasa ta Nijeriya da Kwalejin fasaha da ƙere-ƙere ta Kaduna(Kaduna Polytechnic) kafin daga bisani ya zama babban sakatare a gwamnatin tsohuwar jihar Sakkwato inda daga nan ne gwamnatin mulkin soja ta Nijeriya a ƙarƙashin jagorancin Janar Olusegun Obasanjo ta naɗa shi a matsayin Kwamishinan kula da ma'adinai da lantarki na Tarayyar Nijeriya a shekarar 1978.

Marigayi mai martaba Sarkin Kabin Argungu, Alhaji Muhammadu Mera ya naɗa shi Turakin Kabi (Turakin Argungu) a shekarar 1977.

Saboda kiraye - kirayen al'ummar tsohuwar jihar Sakkwato a shekarar 1978/79, Alh. Shehu Mohammed Kangiwa ya tsunduma a fagen siyasa, aka tsayar dashi takarar kujerar gwamna tare da marigayi magajin garin Gusau, Dr. Garba Nadama a matsayin mataimaki a ƙarƙashin tutar Jam'iyyar NPN, an zaɓe su a watan Yuli na shekarar 1979 aka rantsar dasu ranar 1/10/1979.

Sun fara sanin juna shi da Makaɗa Sani Aliyu Ɗandawo Yauri tun suna yan matasansu a garin Argungu domin anan Argungu ne aka haifi Alhaji Sani Aliyu Ɗandawo a shekarar 1943, suna zaune a Argungu har zuwa shekarar 1959 lokacin da mahaifin Sani Aliyu Ɗandawo wato Aliyu Ɗandawo Shuni ya tashi daga Argungu ya koma Yauri.

Wannan tare bata yanke ba har ya zuwa wafatin Alh. Shehu Mohammed Kangiwa a ranar 17/11 /1981 a Kaduna sanadiyar hatsari/haɗari da ya samu akan doki da yake ƙwallon dawaki akai.

Taren ta amfane su domin kuwa Makaɗa Alh Sani Aliyu Ɗandawo Yauri ya zama hamshaƙin ɗan kwangila kuma ɗan kasuwa baya ga kiɗa da waƙa sanadiyar Alhaji Shehu Mohammed Kangiwa. Shi kuma Gwamna Alh. Shehu Mohammed Kangiwa sunansa yayi amo ta hanyar yayata shi da Makaɗa Sani Aliyu Ɗandawo Yauri yayi a waƙoƙin da ya yi masa. Allah SWT ya jaddada masu rahama su da sauran dukan magabatanmu ya sa mu wanye lafiya mu cika da kyau da imani Alfarmar Fiyayyen Halitta Rasulallahi Sallallahu Alaihim Wasallam, amin ya rabbal alamin.

A wannan hoto marigayi mai girma Gwamna Alh. Shehu Mohammed Kangiwa ne (a tsakiya) tare da mataimakinsa marigayi Dr. Garba Namada na farko daga gefen hagu da kuma marigayi Makaɗa Sani Aliyu Ɗandawo Yauri na farko daga gefen dama.

Daga Alƙalamin:
Hon. Ibrahim Muhammad (Ɗanmadamin Birnin Magaji) Jihar Zamfara, Nijeriya.
23/07/2026.

Post a Comment

0 Comments