Taken gasar a wannan shekara shi ne: "Kalubale da Matsalolin Yawaitar Barace-Barace Musamman na Ƙanana Yara a Ƙasar Hausa."
📌Arc. Ahmed Musa Dangiwa, FNIA, FCIB, Jarman Kankia
Sunansa Arc. Ahmed Musa Dangiwa,
FNIA, FCIB, Jarman Kankia shi ne Shugaba kuma Jagoran Gidauniyar Adabi ta Arc.
Ahmed Musa Dangiwa (Arc. Ahmed Musa Dangiwa Literary Foundation), wadda ke ɗaukar nauyin shirya Gasar
Gajerun Labarai ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa, domin bunƙasa adabin Hausa da ƙarfafa
matasa masu baiwar rubutu.
Haifaffen Ƙaramar Hukumar Kankiya ne
a Jihar Katsina, Arc. Ahmed Musa Dangiwa ƙwararren masani ne a fannin Tsara da
Zanen Gine-gine (Architecture). Ya samu digirin farko da na biyu a wannan fanni
daga Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya yi fice wajen neman ilimi da ƙwarewa.
Ya fara aikinsa ne a matsayin
malami a Hassan Usman Katsina Polytechnic, kafin daga bisani ya tsunduma cikin
harkokin kasuwanci, inda ya yi aiki da kamfanoni daban-daban, har ya kafa nasa
kamfani wanda ya samu nasarori masu yawa.
A fagen shugabanci da hidimar
jama'a, Arc. Ahmed Musa Dangiwa ya riƙe manyan mukamai a matakan jiha da
tarayya. Daga cikin mukaman da ya riƙa akwai Shugaban farko na Jam'iyyar APC a
Jihar Katsina, Manajan Darakta na Bankin Bayar da Lamunin Gina Gidaje na Ƙasa
(Federal Mortgage Bank of Nigeria), Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, sannan
kuma ya rike matsayin Ministan Gidaje da Raya Birane na Tarayyar Najeriya.
Arc. Ahmed Musa Dangiwa mutum ne
mai matuƙar
kishin ilimi da bunƙasa matasa. Daga cikin manyan gudummawar da ya bayar akwai
jagorantar kafa makarantar sakandaren al'umma ta farko a garin Kankiya, domin
faɗaɗa damar samun ilimi ga
matasa.
Ta fuskar tallafa wa ilimi da ci
gaban al'umma, a halin yanzu yana ɗaukar
nauyin karatun ɗalibai
102 a matakin digiri a Jami'ar Tarayya da ke Dutsinma, da kuma ɗalibai 50 masu karatun
aikin jinya da unguwar zoma a Kwalejin Horar da Ma'aikatan Jinya ta Dan Sharif
da ke Kano. Haka kuma, ya ɗauki
nauyin horas da matasa maza da mata sama da 500 sana'o'i daban-daban, tare da
ba su kayan aikin fara sana'a da jari domin su dogara da kansu.
Ta hanyar Gidauniyar Adabinsa,
Arc. Ahmed Musa Dangiwa ya nuna irin ƙudirinsa na bunƙasa adabin Hausa da ƙarfafa
matasa marubuta ta hanyar gasar rubuce-rubuce, tallafawa masu basira, da samar
da damarmakin da za su taimaka wajen haɓaka
ilimi da al'adun Hausawa.
Arc. Ahmed Musa Dangiwa jagora ne
mai hangen nesa, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimar jama'a, inganta
ilimi, ƙarfafa
matasa, da samar da ingantacciyar makoma ga al'umma.
📌Dr. Abdulrahman Aliyu
Sunansa Dr. Abdulrahman
Aliyu, manazarci ne, marubuci, kuma mai
bincike a fannin Nazarin Hausa. Ya kammala digirin PhD a Adabin Hausa daga
Jami'ar Umaru Musa Yar'adua, Katsina.
Ya wallafa muƙalu da
dama a mujallu na ilimi na cikin gida da na ƙasashen waje, tare da gabatar da takardun
bincike a tarurrukan ilimi na ƙasa da na ƙasa da ƙasa. A halin yanzu, bincikensa ya fi
mayar da hankali kan alaƙar Fasahar Ƙirƙirar Basira (Artificial Intelligence – AI) da Harshe, musamman
yadda AI ke tasiri wajen koyarwa da bincike da fassara, da bunƙasa
harshen Hausa a duniyar zamani.
Baya ga ayyukansa na bincike, Dr.
Abdulrahman Aliyu yana ba da gudummawa wajen gyarawa da tace littattafai da muƙalu na
ilimi, tare da jagorantar matasa masu tasowa a fannin bincike da rubuce-rubuce.
Har ila yau, shi ne Sakataren
Kwamitin Shirya Gasar Gajerun Labarai ta Arc. Ahmad Musa Dangiwa, inda yake
taka muhimmiyar rawa wajen tsarawa da gudanar da wannan gasa domin haɓaka rubuce-rubucen Hausa da
ƙarfafa
matasan marubuta.
Yana da burin ganin harshen Hausa
ya ci gaba da bunƙasa ta hanyar bincike, fasahar zamani, da amfani da AI wajen
samar da ingantattun hanyoyin koyarwa da adanawa, da yaɗa ilimi.
A halin yanzu, yana aiki a
National Assembly Service Commission, Abuja, inda yake ba da gudummawa a fannin
gudanar da ayyukan gwamnati. Duk da haka, ya ci gaba da gudanar da bincike da
wallafe-wallafe a fannin Hausa.
Shi ne zai jagoranci bitar
labarai 13 daga cikin wadanda suka tsallako wannan mataki
📌Malam Aliyu Abubakar Sadiq
Sunansa Aliyu Abubakar Sadiq
malami ne, mai bincike (Researcher), ɗan
kasuwa, kuma shugaban Almufid Islamic Foundation. Ya sadaukar da rayuwarsa
wajen yaɗa
ingantacciyar fahimtar Musulunci da gina tarbiyya, da bunƙasa
al'umma ta hanyar ilimi, wa'azi, da ayyukan jin ƙai.
Yana da sha'awa ta musamman a
fannonin Tauhidi da Da'awa da Islamic
Finance daa Zakat da Waqf, da ci gaban matasa. A matsayinsa na mai bincike,
yana gudanar da bincike kan batutuwan da suka shafi tattalin arziƙin
Musulunci da hanyoyin inganta rayuwar al'umma bisa koyarwar Shari'a.
A matsayin Shugaban Almufid
Islamic Foundation, ya jagoranci shirye-shiryen ilimantarwa da tarukan wa'azi da horaswa, da ayyukan
taimakon al'umma, tare da amfani da kafafen sada zumunta da shirye-shiryen
podcast domin isar da saƙon Musulunci cikin hikima da fahimta.
Baya ga harkokin addini da
bincike, Aliyu ɗan
kasuwa ne mai fahimtar muhimmancin haɗa
kasuwanci da ɗabi'a,
yana kuma ƙarfafa
matasa su rungumi kasuwanci na halal da dogaro da kai.
Manufarsa ita ce gina al'umma mai
ƙarfi
wadda ta ginu kan ingantaccen Tauhidi da ilimi mai amfani da kyawawan ɗabi'u, da ci gaba mai
dorewa.
Shi ne zai gabatar da bita a kan
"Barace-barce a Mahangar Addini da Zamantakewar Al'umma
📌Dr. Mujaheed Abdullahi
Sunansa Dr. Mujaheed Abdullahi
fitaccen malami ne kuma masani a fannin Harshen Hausa da Adabin Hausa. Malami
ne a Sashen Harsunan Nijeriya da Ilimin Harshe na Jami'ar Jihar Kaduna (Kaduna
State University – KASU), inda yake koyarwa tare da gudanar da bincike da kuma
bayar da gudunmawa wajen bunƙasa ilimi.
Ya shahara wajen gudanar da
bincike da wallafa muƙalu a fannonin adabin Hausa da ƙa'idojin rubutun Hausa da sauran
batutuwan da suka shafi ci gaban harshe da adabin Hausa. Ayyukansa sun samu karɓuwa a mujallu na ilimi da
kuma tarukan ƙasa da na ƙasa da ƙasa.
Dr. Abdullahi Mujaheed na daga
cikin matasan masana da suka himmatu wajen bunƙasa ilimin Hausa, tare da horas da ɗalibai da masu bincike
domin su zama ƙwararru masu ba da gudunmawa ga al'umma. Ta hanyar koyarwa da
bincike da wallafe-wallafensa, ya ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen adanawa
da haɓaka al'adu da
harshe da adabin Hausawa.
Yana da ƙwarewa sosai kan abinda
ya shafi nazarin gajerun labarai da yadda suka wanzu.
Shi ne zai bayar da bita kan
"Bara da Roƙo A Adabance"
📌Dr. Abu-Ubaida Sani
Sunansa Dr. Abu-Ubaida Sani manazarci
ne kuma marubuci. Ya rubuta littattafai kimanin goma sha biyar (15) da maƙalu
sama da ɗari (100) waɗanda aka wallafa a mujallu
daban-daban a cikin gida Nijeriya da ƙasashen waje. Yakan kuma gabatar da maƙalu a
tarukan ƙara
wa juna sani.
Yana da muradin ganin
rubuce-rubucen Hausa sun mamaye duniya. Yana bakin ƙoƙari wajen gwagwarmayar
cimma wannan mafarki ta hanyar rajin ganin Hausawa suna ɗora rubuce-rubuce masu ma’ana a kan intanet.
Shi ne ya assasa kafar intanet ta Hausa da take kan gaba a duniya wajen tattara
rubuce-rubucen ilimi cikin harshen Hausa (wato amsoshi.com). A bisa wannan yunƙuren
ne kuma ya samar da labarai.amsoshi.com, kafar da ta shawara wajen kawo labarai
cikin harshen Hausa.
Ya kasance edita a mujallu
daban-daban a cikin gida Nijeriya da ƙasashen waje. A cikinsu har da Tasambo
Journal of Language, Literature, and Culture (Nijeria) da da International
Academic Journal of Education & Literature, International Academic &
Research Consortium (Kenya) da Global Academic Journal of Linguistics and
Literature (Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa) da
Sarcouncil Journal of Arts, Humanities and Social Sciences (India) da The
Afrikanist (Amurka), da sauransu. Bugu da ƙari, shi ne ya samar sannan yake kula da
kafafen intanet na mujallu kimanin goma (10).
Wani fanni da ya saka gaba shi ne
aikin fassara. Ya samar kamfani mai suna Amsoshi Language Services
(amlas.amsoshi.com) inda yake amfani da wannan dama domin koya wa zaƙaƙuran ɗalibai ayyukan da suka
shafi kimiyyar harshe a kan intanet.
A yanzu haka yana koyarwa a
Sashen Haruna da Al’adu na Jami’ar Tarayya Gusau, a Nijeriya.
Abin da ya fi burge shi, shi ne
ganin al’umma suna farin ciki a dalilinsa. Mutanen da suka fi burge shi su ne
waɗanda suke aikata
daidai tare da rayuwa bisa gaskiya da riƙon amana, da kuma aiki tuƙuru
cikin zaƙaƙuranci
da buɗaɗɗiyar zuciyar karɓar gyara da datattun
sauye-sauyen zamani.
Shi ne zai jagoranci bitar
labarai goma daga cikin wadanda suka tsallako wannan matakin.
📌Malama Hadiza Idris
Sunanta Hadiza Idris. Malama ce a
Sashen Harsunan Nijeriya na Jami'ar Umaru Musa Yar'adua, Katsina. Haka kuma, ɗaliba ce mai neman digirin
na uku PhD a fannin Adabin Hausa.
Fannonin binciken da tafi mayar
da hankali a kai sun haɗa
da wasan kwaikwayo da nazarin fina-finan Hausa (Drama and Film Studies). A
tsawon shekaru, ta gudanar da bincike tare da wallafa muƙalu da suka shafi
rubutattun wasannin kwaikwayon Hausa, da kuma nazarin yadda ake aiwatar da
baddala a cikin Adabin Hausa.
Ta kuma wallafa littafi mai taken
Baddalawa a Wasan Kwaikwayon Hausa, wanda TETFund ta ɗauki nauyin wallafawa a shekarar 2024.
A halin yanzu, tana gudanar da
bincike kan rayuwar mace a ƙarni na ashirin da ɗaya,
inda take nazarin yadda ake gina hoton mace a cikin fina-finan Hausa masu dogon
zango.
Sannan tana maraba da duk wata
dama ta haɗin gwiwa a
fannin bincike, da wallafa muƙalu, da gudanar da sharhi kan batutuwan
da suka shafi rayuwar mata, Adabin Hausa da wasan kwaikwayo, da nazarin
fina-finai.
Za ta jagoranci bitar labarai goma
daga cikin wadanda suka tsallako wannan mataki.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.