Daga
Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani
Uwar gida ita ce matar farko a cikin gidan aure. Akan ɗauke ta a matsayin mace mai ƙima da daraja kasancewar ta mafi yawan shekaru da daɗewa tare da mai gida. Sannan a mafi yawan lokuta, manyan ‘ya’yan gidan sukan kasance ‘ya’yanta ne. Ga misalan karin magana da suka yi tsokaci game da uwar gida:
1. Uwar gida ran gida
Wannan fitaccen kirare ne da ake yi wa uwargida.
Wannan kirari yana nuna matsayi da muhimmancin da al’adar Bahaushe ta ba
mace, inda aka bayyana ta da cewa, ita ce rayuwar gida. Duk gidan da ba mace,
to wannan gidan matacce ne. Wannan magana kuwa tabbas haka take, duk wanda ke
musu ya shiga gidan gwauro ya gani. Saboda haka ake cewa, mata in ba ku, ba
gida, in kuma kun yi yawa gida ya ɓaci. Haka kuma, ta fuskar
jagoranci a mahangar zamantakewa, al’ada ta kalli uwargida a matsayin wata mace
mai matuƙar
muhimmanci wajen tafiyar da lamuran gida da kuma samar da kyakkyawar mu’amala tsakanin maigida da abokan zamanta da ita kanta da ma dangin miji da sauran mutanen
da ke da alaƙa da
gidan. Wanan ne ya sa ake kwatanta ta da rayuwar gidan domin
duk wata zamantakewa wadda babu jagoranci tare da ita yana da wahala a cimma
nasara da za ta haifar da ɗa mai ido.
2. Uwargida sarautar mata
Wannan karin magana (kirari) ne wanda Hausawa suke amfani da shi
domin su nuna wata mace ita ce shugaba, kuma mai isa, mai faɗa a ji a wurin mijinta. Wato karin magana ne da ke yi wa
macen da miji ya fara aurenta kirari da cewa ita ce shugaba a wajensa kuma ko
da ya auri wata amarya, to wannan dai matar tasa ta farko ita ce jagorar duk
matan nasa, kuma ita ce ta zama mai kula da komai nasa wajen tursasa shi ya yi
abin da take so.
Ana amfani da wannan karin magana ana nuna uwargida (matar
mutum ta farko) ita ce take da isa a wajensa, ita kuma ke juya shi da faɗa masa ya ji. (Gwammaja, 2010: Vol. III: 26).
Manazarta
Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.