𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum malam KHAMIS. Barka da sallah. da fatan an dawo idi lafiya. Dan Allah ya sunan shedan kafin Allah ya la'ance shi? shin Shaiɗan yana cikin jinsin aljanu ne Ko Mala'iku kuma Da me Allah zai yiwa shaidan azaba a ranar alkiyama?
SUNAN SHAIƊAN KAFIN ALLAH YA LA'ANCE SHI
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuhu
Malaman tafsiri sun
bayyana cewa Sunan Shaiɗan (Iblis) na asali
kafin Allah Ya la'ance shi, shi ne: AZAZIL ko AZAZILU wanda ke nufin
"Bawan da Allah ya daukaka" ko kuma "Mafi kusa da mala'iku a
bauta da ilimi".
Malaman addinin
Musulunci sun bayyana cewa shaiɗan yayi girman kai, ya ƙi yi wa Annabi Adamu
sujada, Bayan Allah Ya halicci Annabi Adam, Ya umurci Mala'iku su yi masa
sujada don girmamawa. Mala'iku duka sun yi biyayya, amma Iblis ya ki, yana mai
ganin kansa a matsayin wanda ya fi Adam saboda shi an halicce shi daga wuta,
yayin da aka halicci Adam daga ɓako (danko/ƙasa).
Wannan rashin biyayya
da girman kai sun sa Allah Ya kore shi daga rahamarSa, Ya la'ane shi, kuma Ya
sanya shi cikin tsinannu har zuwa Ranar Kiyama.
A cikin Alƙur'ani mai girma,
Allah SWT Ya yi bayanin wannan lamari dalla-dalla, musamman a cikin Suratul
A'raf (aya ta 11 zuwa 18).
Sunan shaidan ya koma
Iblis ne bayan da Allah Ya kore shi daga rahamar Sa sakamakon rashin biyayya.
Allah Ya kore shi daga Aljanna Ya la'ance shi. Daga nan ne aka sauya sunansa
zuwa Iblis, wanda ma'anarsa a harshen Larabci ke nufin yanke kauna (daga rahamar
Allah), wato wanda aka kora, aka kuma hana shi duk wata alheri. A kan kira shi
da suna Shaidan, ma'anar kuma ita ce mai nesa da gaskiya, mai tawaye, ko dukkan
wani abu da ya kauce wa tafarkin Allah.
Malaman tafsiri sun
yi saɓani game da cewa Shaiɗan yana cikin jinsin
aljanu ne Ko Mala'iku zuwa maganganu guda biyu:
1. Shaiɗan yana daga cikin
mala'iku, saboda faɗin Allah a cikin
suratul Bakara aya ta 34:
وَإِذْ
قُلْنَا لِلْمَلَائِكَةِ اسْجُدُوا لِآدَمَ فَسَجَدُوا إِلَّا إِبْلِيسَ أَبَىٰ
وَاسْتَكْبَرَ وَكَانَ مِنَ الْكَافِرِينَ
Kuma a lõkacin da
Muka ce ga malã'iku: ''Ku yi sujada ga Ãdam,'' Sai suka yi sujada, fãce Ibilĩsa
ya ƙi,
kuma ya yi girman kai, kuma ya kasance daga kãfirai. (suratul
Bakara aya ta 34).
Wannan ya nuna shaiɗan yana daga cikin
mala'iku ne.
2. Shaiɗan Aljani ne, saboda
faɗin Allah maɗaukakin sarki:
وَإِذْ
قُلْنَا لِلْمَلَائِكَةِ اسْجُدُوا لِآدَمَ فَسَجَدُوا إِلَّا إِبْلِيسَ كَانَ
مِنَ الْجِنِّ فَفَسَقَ عَنْ أَمْرِ رَبِّهِ أَفَتَتَّخِذُونَهُ وَذُرِّيَّتَهُ
أَوْلِيَاءَ مِن دُونِي وَهُمْ لَكُمْ عَدُوٌّ بِئْسَ لِلظَّالِمِينَ بَدَلًا
Kuma a lõkacin da
Muka ce wa malãiku, ''Ku yi sujada ga Ãdamu.'' Sai suka yi sujada fãce Iblĩsa,
yã kasance daga aljannu sai ya yi fãsiƙanci ga barin umurnin
Ubangijinsa, To fa, ashe, kunã riƙon sa, shi da zũriyarsa,
su zama majiɓinta baicin Ni,
alhãli kuwa su maƙiya ne a gare ku? Tir da ya zama musanya ga azzãlumai.
(Suratul Kahf Aya ta 50).
Wannan ayar ta
bayyana cewa shaiɗan daga aljanu yake.
Zance mafi inganci
shi ne Shaiɗan aljani ne, saboda
an halicce shi ne daga wuta, su kuwa mala'iku an halicce su ne daga haske,
kamar yadda hadisin Muslim mai lamba ta: (2996) yake nuni zuwa hakan.
Sannan Shaiɗan yana da zuriyya,
wacce take hayayyafa, mala'iku kuma ba sa haihuwa, wannan sai ya nuna ba daga
cikinsu yake ba, Wannan yasa za'a ɗauki ayar suratul Bakara a matsayin tana
nufin yana daga cikinsu ta fuskar zaman tare, amma ba ta fuskar halitta ba,
sannan mala'iku ba sa saɓawa Allah, shi kuma
shaidan (Iblis) yana saɓawa Allah.
Don neman Karin
bayani duba: Tafsirin Ibnu-jarir 1/507 da Jami'u lada'if attafsir 1/278.
Dalilin da yasa wasu
ke tunanin shaidan (Iblis) Mala'ika ne saboda ya kasance mai yawan bauta wa
Allah sosai tun yana ƙarami, wanda hakan ya sa aka ɗaukaka shi har ya
dinga zama da Mala'iku. Lokacin da Allah Ya umarci Mala'iku da su yi sujjada ga
Annabi Adamu, an shigar da shi cikin umarnin ne saboda yana cikin su, amma
lokacin da ya ƙi yin sujjadar saboda girman kai, sai asalin halittarsa
ta Aljani ta fito fili.
A ranar alkiyama
babban hukunci da Allah Ya tanadarwa Shaidan shi ne jefa shi cikin wuta
madawwamiya. A cikin Suratu Sad (Aya ta 84 zuwa 85), Allah Maɗaukakin Sarki Ya yi
rantsuwa da cewa:
لَأَمْلَأَنَّ
جَهَنَّمَ مِنْكَ وَمِمَّنْ تَبِعَكَ مِنْهُمْ أَجْمَعِينَ
"Lalle ne zan
cika Jahannama da kai (Iblis) da wanda ya bi ka daga cikinsu gaba ɗaya."
Ya Allah muna neman
tsarinka daga sharrin shaidan da tarkonsa.🤲
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.