𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-salamu Alai-kum. MLM Dan Allah Ina da tambaya. masu ilimin taurari da suke fadawa mutane cewa taurarinsu sun disashe ko suna haskawa ko Wani Al-khairi zai sami mutum kokuma mutane sunawa Wani Hassada, ko akwai ido ma'ana kambin ido Akan mutum Kuma ma Hassadan suyimasa yawa nakusa dananesa, gaskiya suke fada Kuma taurarin sunayin haka Dan Allah malam ayimana bayani yadda zamu fahimta Kuma ataimaka mana da Addu'ar dazatayi maganin wannan matsalar.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuhu
A cikin Shari'ar
Musulunci, hukuncin ilimin taurari ya kasu kashi biyu, ya danganta da yadda
mutum ya yi amfani da shi. Akwai sashe da yake Haramun ne (Bokanci da duba),
sannan akwai sashe da yake Halal ne (Kimiyya da lissafi).
1. ILIMIN TAURARI DA
YAKE HALAL (علم الفلك - ASTRONOMY):
Wannan shi ne nazarin
taurari da duniyoyi a matsayin cikakken ilimin kimiyya, kamar lissafin
tafiyarsu, kusancinsu, da yadda canjinsu yake shafar lokuta. Wannan fanni Ya
halatta (Halal), kuma yana iya zama faralul-kifaya (wajibi akan al'umma) don
amfanin addini da rayuwa.
2. ILIMIN TAURARI DA
YAKE HARAMUN (التنجيم - ASTROLOGY).
Wannan shi ne neman
sanin gaibu ko hango abubuwan da za su faru a nan gaba ta hanyar tafiyar
taurari, motsinsu, ko rarrabuwar gidajensu (kamar duba, shiga shafukan Zodiac
Signs, ko karanta tauraron ɗan adam na ranar haihuwa). Wannan fanni Haramun ne kuma
yana kasancewa babban zunubi (ko shirka).
Shari'a ta bayyana
cewa Allah ne kaɗai masanin gaibu.
Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: "Wanda duk ya debo wani ɓangare na ilimin
taurari (don sanin gaibu), to ya debo wani ɓangare ne na sihiri..." (Abu Dawud).
Yin amfani da taurari
don gano kaddara, sa'ar aure, arziki, ko masifa dabi'a ce ta bokaye da 'yan
tsubbu.
A koyarwar Musulunci,
taurari ba su da ikon juya rayuwar dan adam, ba su san gaibu ba, kuma ba sa
kawo alkhairi ko sharri. Allah kadai ya san abin da zai faru nan gaba. Masu
fadin tauraron mutum ya disashe ko yana haskawa ba gaskiya suke fada ba,
hasashe ne da yaudara. Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya hana zuwa wajen
masu duba ko masu duba na taurari. Duk wanda ya yarda da abin da suke fada, to
ya kusa fita daga koyarwar addini.
Malamai kamar su
Imamu Ƙatadah sun takaita amfanin taurari da Allah ya ambata a
Alkur'ani zuwa abubuwa guda uku:
1. ADO GA SARARIN
SAMANIYA: Kamar yadda yake a Suratul Mulk, aya ta 5:
وَلَقَدْ
زَيَّنَّا السَّمَاءَ الدُّنْيَا بِمَصَابِيحَ وَجَعَلْنَاهَا رُجُومًا
لِلشَّيَاطِينِ ۖ وَأَعْتَدْنَا لَهُمْ عَذَابَ السَّعِيرِ
Kuma lalle Mun ƙawãta
samar farko da fitillu, kuma Muka sanya su abin jifa ga shaiɗanu, kuma Muka yi
musu tattalin azãbar Sa'ĩr. (Suratul Mulk, aya ta 5)
2. KARIYAR SAMANIYA:
Jifan shaidanu kangararru da suke son satar jiyya daga sama.
3. ALAMOMIN GANE
HANYA: Kamar yadda Allah ya ce a Suratu An-Nahl aya ta 16:
وَعَلَامَاتٍ
ۚ وَبِالنَّجْمِ هُمْ يَهْتَدُونَ
Kuma da waɗansu alãmõmi, kuma da
taurãri sunã mãsu nẽman shiryuwa (ga tafiyarsu ta fatauci) (Suratul An-Nahl
Aya ta 16).
A musulunci, Hassada
da Kambin Baka (ko Kambun Ido) abubuwa ne guda biyu da suke da tabbas kuma
addini ya tabbatar da akwai su da kuma cutarwarsu ga rayuwar ɗan Adam. Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi kashedi mai tsanani game da su tare da koyar
da hanyoyin kariya.
HASSADA: Ita ce mutum
ya ji zafin wata ni'ima (kamar dukiya, ilimi, ko lafiya) da Allah ya yi wa wani
bawanSa, tare da burin daddale ko gushewar wannan ni'imar daga gare shi.
Hassada dabi'a ce ta zunubi da ke cinye kyawawan ayyukan mutum.
KAMBIN IDO (Al-Ayn):
Wannan shi ne cutarwa da ke samun mutum, dabba, ko dukiya sanadiyyar sha'awa,
mamaki, ko kallon keta da wani ya yi masa. Kambin Ido (Al-Ayn): Annabi
(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: "Kambin ido gaskiya ne." Yana iya
fado da mutum daga matsayinsa ko ma ya kai shi ga halaka.
Maimakon zuwa wajen
masu taurari, ga addu'o'i da matakan da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi
Wasallam) ya koyar da suke maganin HASSADA da KAMBIN IDO:
1. Karanta Surori Uku
Na Karshe (Al-Mu'awwidhatayn) wato Suratul Ikhlas (Ƙul Huwallahu Ahad)
Suratul Falaƙ (Ƙul A'uzu bi Rabbil Falaƙ) Suratun Nas (Ƙul A'uzu bi Rabbin
Nas). Wannan tana maganin hassada. Ka rinka karanta wadannan surori sau uku
safe da yamma da lokacin kwanciyar bacci kuma ka shafa a daukacin jikinka.
2. Karanta Ayatal
Kursiyyu. Ka karanta ta duk bayan sallah, kafin ka kwanta barci, da kuma safe
da yamma. Tana tsare mutum daga dukkan sharri.
3. Karshen Suratul Baƙarah: (Ayar karshe
guda biyu) wato Amana Rasulu, ka karanta daddare.
4. Addu'ar Kariya
Daga Kambin Ido Zaka iya fadin wannan addu'ar sau da dama:
أَعُوذُ
بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّةِ، مِنْ كُلِّ شَيْطَانٍ وَهَامَّةٍ، وَمِنْ كُلِّ
عَيْنٍ لَامَّةٍ.
Ma'ana: Na nemi tsari
da kalmomin Allah cikakku, daga dukkan shaidan da dabba mai dafi, da kuma
kowane ido mai cutarwa.
Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kasance yana neman wa jikokinsa (Hasan da
Husaini) tsari da wannan addu'ar:
MATAKAN KARIYA NA
RAYUWA:
1. BOYE SIRRI: Kar ka
rinka tallata dukkan alkhairinka ko nasarorinka ga kowa, musamman a kafafen
sada zumunta (social media). Yana da kyau mutum ya fadi ni'imar Allah gare shi,
amma musulunci ya halatta mutum ya boye wasu sirrika ko nasarori na rayuwarsa
ga mutanen da yake zargin suna da hassada ko kishinsa, har sai abin ya tabbata
(Kamar yadda Annabi Ya'ƙub ya shaidawa Annabi Yusuf a cikin Alƙur'ani).
2. AMBATON ALLAH: Duk
lokacin da kaga wani abu ya burge ka na kanka ko na wani, fadi
"MASHA'AALLAH, TABARAKALLAH" don kar ka kwashe da ido. Idan ka ga
wani abu mai kyau a gurin dan'uwanka, ko jikinka, kada ka tsaya murna kawai.
Fada: "MASHA'ALLAH, TABARAKALLAH" ko "ALLAHUMMA BARIK".
Wannan yana kore tasirin kambin ido nan take.
Idan an tabbatar
mutum ya kamu da kambin ido, akwai hanyoyi guda biyu na magani
1. Idan an san wanda
ya yi kambin, za a umarce shi ya yi alwala ko ya wanke hannunsa da fuskarsa a
cikin kwanon ruwa. Sai a dauki wannan ruwan a zuba shi a bayan wanda aka yi wa
kambin daga bayansa. Da izinin Allah zai warke nan take.
2. Yin Ruƙyah: Karanta ayoyin
Alƙur'ani
(kamar Fatiha, Ayatul Kursiyyu, da Kulhuwa da Falaki da Nasi) a cikin ruwa a ba
wanda yake da cutar ya sha kuma ya yi wanka da shi.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.