𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum malam. Barka da wuni. da fatan kana lafiya. Malam dan Allah a ba ni shawara. Ƙanwata ce a gidan mijinta. Amma zaman babu daɗi sakamakon Yana yi mata wulaƙanci. Kalakala. Amma dai mijin cewa akayi yazo ya nemeta. sabida yabawa da hankalinsa da akayi, dama makobtan juna ne. Kuma yace Yana sonta. Harma sun haifi Yaya. To Amma wulaƙancin yayi yawa. Ahalin yanzu ita matar ta haɗe kayanta awaje ɗaya. Har tana maganar wai ta haƙura. Gidansu zata. To don Allah malam atemaka mana da Shawara..
SHAWARAR ZAMA DA MIJI
MAI WULAƘANTA MATARSA
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikis salam wa
rahmatulLahi wa barakatuhu.
Abu na farko dai
amatsayinki na yayarta, ki yi mata nasiha tare da jan hankalinta game da
muhimmancin hakuri da juriya, da kuma girman ladan da Allah yake bayarwa ga
masu hakuri. Misali kamar ayoyin da Allah yake cewa : "HAKIKA LALLAI
ALLAH YANA TARE DA MASU HAKURI".
Sannan ki nusar da
ita game da girman hakkin mijinta dake kanta ta ɓangaren ladabi, biyayya da kyautata ta
kowacce fuska. Ki gaya mata kuma yin hakuri da yanayin halayensa gwargwadon iko
yana daga cikin kyautatawar da Allah yake so mace ta yiwa mijinta. Kamar yadda
suma mazajen Allah ya umurcesu da yin hakuri da kyautata zama tare da iyalansu
cikin adalci.
Domin hakika bayan
ayyukan farillai irin su sallah, zakkah da azumi da aikin hajji, babu wata
hanya mafi saurin shigar da mace zuwa ga samun rahamar Allah fiye da kyautata
zamantakewa da miji..
Kada ki goya mata
baya wajen kokarin kashe aurenta. Domin hakika akwai bala'o'i da jarrabobi masu
yawa acikin mutuwar aure. Musamman idan kika dubi cewa za ta fita ne ta bar
'ya'yanta har guda biyu.
Kiyi bakin kokarinki
wajen fahimtar da ita, sannan ki tuntubi mijin nata amatsayinki na yayar
matarsa, ku zauna ki saurari nashi bayanin. Watakil itama akwai laifin da take
yi masa. Sai ki bashi hakuri ki tarasu su biyun ki basu shawarwari da nasihohi.
Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam acikin wani hadisin da Bukhariy da Muslim suka
riwaito ta hanyar Sayyiduna Abu Hurairah (radhiyalLahu anhu) Da yake bayanin
kofofin samun lada, yace "Yin sulhu atsakanin mutum biyu shima sadaƙah ne".
Acikin irin wannan
aikin na sulhu atsakanin Ma'aurata, ya halatta gareki ki fadi duk abinda zaki
fada wanda zai kawo gyara atsakaninsu. Koda ta hanyar fadar abinda za'a iya
cewa 'Karya' ne. Domin hakika manyan Malaman Musulunci da dama sun nassanta
cewa yin karya yakan halatta ga mai yin sulhu tsakanin Mutum biyu.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.