𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamualaikum malam
barka da warhaka ina da tambayoyi kamar haka:
1. Shin idan mutum ya
yanka rago ɗaya shi da iyalansa
ya isar masa layya?
2. Shin mutum nawa za
su iya yanka rago ɗaya?
3. Shin mutum nawa za su iya tarayya akan saniya ɗaya ko rakumi ɗaya?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam
Warahmatullahi Wabarkatuhu.
Rago ɗaya ta wadatar a
matsayin udiya ga mutum ɗaya da iyalansa da
wanda yake so a cikin musulmi. “Nana A’isha (RA) ta ce, Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi umurni da a kawo masa rago mai baƙin ƙafafu, baƙin ciki da bakin
baya, da bakin (digo digo) a idonsa, a zo masa da shi, don ya yi layya da
shi. Sai ya ce wa Aisha: “Ba ni wukar,”
sai ta yi haka ta miko masa. Ya karɓa, sannan ya ɗauki ragon, ya kwantar da shi a kasa,
sannan ya yanka (wato ya shirya yanka), yana mai cewa: “Da sunan Allah, Ya
Allah ka karɓa (wannan hadaya) a
madadin Muhammadu da iyalan Muhammadu da al’ummar Muhammadu”. Sannan ya yanka dabbar.” (Muslim ne ya
ruwaito).
Abu Ayyub al-Ansariy
(Allah Ya yarda da shi) ya ce: “A lokacin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam)
mutum ya kan yanka ragonsa don kansa da kuma iyalan gidansa, sun kasance suna
yanka tunkiya su na cin wani su bada wani.” (Ibn Majah da Tirmizi suka ruwaito
shi, wanda ya sanya shi a matsayin sahih. Albani kuma ya sanya shi a matsayin
sahih a cikin Sahihul Tirmizi, 1216).
Idan mutum ya yi
hadaya da tunkiya ɗaya ko akuya a
madadin kansa da iyalinsa, wannan ya wadatar masa da duk wanda ya nufa cikin iyalinsa, rayayye ko
matacce. Idan kuwa bai yi niyya takamammiya ba to ya haɗa da duk waɗanda suke cikin
wannan kalmar ta (iyali ko gida) na al'ada ko na harshe.
A al'adance, yana
nufin duk wanda yake tallafawa, wato wa'inda suke kasansa, daga mata, 'ya'ya da
dangi ko ma wanda bai da alaƙa da su. A fannin harshe, kuma ya haɗa da duk waɗanda suke da alaƙa da shi na ’ya’yansa
da zuriyar mahaifinsa da kakansa da kakansa.
Kashi ɗaya cikin bakwai na
raƙumi
ko saniya yana daidai da tunkiya ɗaya ne. Idan mutum ya yanka kashi ɗaya bisa bakwai na
rakumi ko saniya a madadin kansa da iyalansa,
hakan ya wadatar. Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam ya ce kashi
ɗaya bisa bakwai na
rakumi ko saniya yana maye gurbin tunkiya a wajen hadaya da ake yi a lokacin
Hajji. Don haka wannan ma ya shafi uduyya ne domin babu wani bambanci tsakanin
udiyya da hady a cikin wannan mas’ala.
Idan mutum biyu ko
fiye suka sayi tunkiya suka yanka, wannan bai wadatar musu ba, domin ba a
ruwaito irin wannan abu ba a cikin Alƙur'ani da Sunna ba.
Haka nan idan mutum
takwas ko fiye da haka suka raba rakumi ɗaya ko saniya, hakan bai wadatar musu ba su
ma (amma ya halatta mutum bakwai su raba rakumi ko saniya). Domin kuwa ayyukan
ibada sun kasance kamar yadda Alƙur'ani da Sunna suka
shar'anta ne kuma ba ra'ayin mutum ake bi ba.
Ba ya halatta a ketare iyakokin da aka gindaya dangane da nawa ne za a
yi ko kuma yadda za a yi. Wannan ba ya rasa nasaba da shigar da wasu cikin ladan,
domin an ruwaito cewa babu iyaka ga adadin mutanen da za a yi layya a
madadinsu.
Kuma Allah ne Mafi
sani.
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.