Ticker

6/recent/ticker-posts

Rena Malamai

Kowa ya san irin rawar a zo a gani da Malaman al'umma suke takawa don ganin al'umma ta tsira a Duniyanta da Lahiranta. A kullum su suke koya wa al'umma Addini, suke koya musu Mu'amalar harkokin Duniya gaba daya, tare da koya mata kyawawan dabi'u. Su suke tsoratar da al'umma game da fitunu, musamman wadanda suke da nasaba da siyasa, wadanda tun tuni Annabi (saw) ya yi bayani a kansu kuma ya tsoratar. Su suke zamowa fitila ga al'umma a lokacin da ta dimauce take neman mafita.

To, a game da Malaman Al'umma irin wadannan, wadanda suka zama madubi ga Al'umma, an samu wasu bangarori biyu masu hamayya da juna, wadanda su kuma babu wadanda suka rena kamarsu.

Wadannan bangarori kuwa su ne Kungiyar Salafiyyun "Madakhilah" da kuma Kungiyar Ikhwan da rassanta da 'ya'yanta..

Kungiyar Ikhwan ta rena Malaman Al'umma, suna sukarsu, suna cewa; ba su da "Fiqhun Waki'i", suna nufin ba su san harkokin siyasa da jihadi ba, ba su san siyasar Duniya ba. Don haka ba za a karbi Fatawa ko wani ilimi game da harkokin siyasar Duniya da jihadi da abin da ya shafi matsalolin Al'umma, kamar ta Falasdinawa da ire - irensu daga gare su ba, saboda -wai- su jahilai ne a wannan fanni. Su kawai sai dai a karbi fatawan tsarki da Sallah daga gare su, shi ya sa ma suke kiransu da Malaman jinin haila da nifasi, don batanci da suka. Kai, akwai lokacin da har suke sukarsu da sunan Malaman fada "علماء السلاطين", kai, har lamarin ya kai ga kiransu da sunan Munafukai, sai su yi ta janyo Ayoyin Munafukai suna dorawa a kansu. Saboda kawai su wadannan Malaman ba sa goyon bayan tafo-mu-gama da gomnatoci da masu mulki, saboda guje wa fitintunun siyasar da Annabi (saw) ya tsoratar da Al'ummarsa game da su.

To a daya bangaren kuma, akwai wata kungiyar da take yi wa Kungiyar ta Ikhwan inkari a kan wannan mummunan tafarki, wato su ne Kungiyar Salafiyyun, wadanda suka shahara da sunan "Madakhilah".

To amma kash! Ita ma wannar kungiya tana da nata salo na rena wadancan Malamai, inda take kiransu da Malaman da ba su san "Manhaji" ba. Sun yarda wadancan Malaman masana ne a Shari'a, sun san Fiqhu da Aqida, amma sun jahilci "Manhaji". Saboda suna ganin babu wanda ya san "Manhajin" sai Shugaban kungiyar tasu da wasu 'yan tsirarun Na'ibansa. Kuma wannan "Manhaji" ya fi komai a wajensu, don shi wata kololuwar martaba ce da sai mutum ya zama Musulmi Ahlus Sunna mai ingantacciyar akida kafin ya isa inda zai zama mai "Manhaji" mai kyau. Wato idan ya shiga kungiyar tasu. Don haka su a wajensu, kasancewarka mai bin Akidar Salaf bai wadatar ba, har sai ka hada da bin "Manhaji", wanda hakikaninsa shi ne shiga kungiyarsu da bin shugabanninta sau da kafa.

Wannan ya sa sai ka ji suna sukar manyan Malamai, suna cewa ba su san "Manhaji" ba, don haka a yi hattara da su. Duk da kasancewarsu jagororin Al'umma a ilimin Shari'a da akidar Sunna.

To in an lura, duka wadannan bangarorin biyu sun yi tarayya cikin sukar manyan Malaman Sunna da aibanta su, da nuna cewa su kungiyoyin biyu suna da wasu mahanga game da siyasa (a wajen Kungiyar Ikhwan), da "Manhaji" (a wajen Kungiyar Salafiyyun) sabanin abin da Malaman Shari'a suka sani.

A takaice, ya kai dan uwa Ahlus Sunna, kar ka rudu da wadanda kungiyoyi guda biyu. Ka yi riko da Malaman Al'umma, wadanda suka shahara da karantar da kai Addini, ka sani Shari'ar Muslunci ta kunshi komai, ka sani cewa, Malaman Al'umma su ne masana siyasa da matsalolin Al'umma da abin da ya shafi siyasar Duniya, fadakarwarsu da nasihunsu da fatawowinsu su ne abin dauka ba maganganun Yan taratsi ba, masu yi wa Al'umma turin-jeka-ka-mutu. Kowa ya shaida abin da ya faru a zanga-zangan kasashen Larabawa.

Haka kuma a Addini babu wani abu -wai- shi "Manhaji" da wadancan Malamai jagororin Al'umma da ba su sani ba. In kuwa akwai to kirkirarre ne, ba a cikin Addini yake ba. Ma'ana; ba shi da asali a cikin abin da Annabi (saw) ya zo da shi, kuma ya bar Sahabbansa a kansa.

Don haka ya kamata ka san cewa; a kullum gaskiya tana tsakanin karya guda biyu ne, shiriya tana tsakanin bata guda biyu. Hanya madaidaiciya tana tsakanin kungiyoyi guda biyu.

✍️ Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments