HAƊUWAR IBNU BAƊUƊA DA IBNU TAIMIYYA

A ƙarni na takwas, an yi wani mutum ɗan yawon duniya, mai suna Ibnu Baɗuɗa (703 - 779h). Asalinsa ɗan ƙasar Moroco ne, daga garin Ɗanja (Tangier).

Wannan mutumi ya yi yawace-yawace da yawa, ya zagaya sassan Duniya. Ya shiga ƙasashe da yawa a Arewacin Afirka, da kudancin Europe, da Gabas ta tsakiya, da Asia ta tsakiya, da kudancinta. Ya taso daga garinsu, yana kan hanya har ya isa Birnin Dimashq, garin su Ibnu Taimiyya.

Shi wannan mutumi, ya rubuta a cikin littafinsa cewa:

"وكان بدمشق من كبار الفقهاء الحنابلة تقي الدين ابن تيمية كبير الشام، يتكلم في الفنون، إلا أن في عقله شيئًا، وكان أهل دمشق يعظمونه أشد التعظيم، ويعظهم على المنبر...

إلى أن قال: "...وكنت إذ ذاك بدمشق، فحضرته يوم الجمعة، وهو يعظ الناس على منبر الجامع ويذكرهم، فكان من جملة كلامه أن قال: إن الله ينزل إلى سماء الدنيا كنزولي هذا. ونزل درجة من درج المنبر".

رحلة ابن بطوطة "تحفة النظار" (ص: ١١١ - ١١٢)

"Akwai wani Malami cikin manyan Malaman Fiƙhun Hanbaliyya a Birnin Dimashq, mai suna Taƙiyyuddeen Ibnu Taimiyya, babban Malamin Sham, yana da ilimin fannoni da yawa, sai dai akwai motsi a ƙwaƙwalwarsa. Mutanen Dimashq suna girmama shi matuƙa, yana yi musu wa'azi a kan minbari...

... A lokacin ina Dimashq, sai na same shi ranar Juma'a, yana wa'azi wa mutane a kan minbarin Masallacin Juma'a. Daga cikin abin da na ji ya faɗa; Lallai Allah yana sauƙowa zuwa sama ta Duniya, kamar wannan sauƙowa tawa. Sai ya sauƙo hawa ɗaya, daga kan matakan minbarin".

Wannan shi ne abin da ya faɗa.

A ciki ya bayyana Ibnu Taimiyya a matsayin mutumin da kansa da motsi.

Kuma ya siffanta shi da cewa; yana kamanta sauƙowar Allah daga sama da sauƙowarsa shi Ibnu Taimiyya daga kan minbari. Ma'ana; Ibnu Taimiyya "Mushabbihi" ne, mai kamanta siffofin Allah da siffofin halitta.

To amma wannan labari na Ibnu Baɗuɗa ya ɗaure kai wa mutane masu san sanin gaskiyar labarin, saboda dalilai kamar haka.

1) Shi Ibnu Baɗuɗa ya faɗi ranar da ya isa birnin Dimashq, inda a maganarsa a kan "بعلبك" ya ce:

"وكان دخولي لبعلبك عشية النهار، وخرجت منها بالغد، ولفرط اشتياقي إلى دمشق، وصلت يوم الخميس، التاسع من شهر رمضان المعظم، عام ستة وعشرين إلى مدينة دمشق الشام".

رحلة ابن بطوطة "تحفة النظار" (ص: ١٠٠)

"Shigata garin Ba'alabakka da yammaci ne, da safe kuma na fita daga cikinta, amma saboda tsananin shauƙina ga Dimashq, na isa birnin Dimashq a ranar Alamis, 9 ga watan Ramadhan abin girmamawa, a shekarar 726H".

Ga shi dai a fili ya faɗi ranar da ya isa birnin Dimashq, wato 9 /9/ 726H.

To abin da ya ja hankulan mutane shi ne; a wannar rana, Ibnu Taimiyya yana cikin kurkuku. Tunda an shigar da shi kurkuku ne tun ranar Litinin, 6 /8/ 726H.

Wato an shigar da shi kurkuku wata ɗaya, har da kwana 3, kafin isowar Ibnu Baɗuɗa birnin Dimashq.

Malaman da suka ruwaito Tarihin Ibnu Taimiyya ne suka tabbatar da haka, irin su Ibnu Abdilhadiy, Ibnu Kasir da sauransu. Ga abin da Ibnu Kasir ya ce:

"قال الْبِرْزَالِيُّ: وَفِي يَوْمِ الِاثْنَيْنِ بَعْدَ الْعَصْرِ السَّادِسِ مِنْ شَعْبَانَ اعْتُقِلَ الشَّيْخُ الْإِمَامُ الْعَالِمُ الْعَلَّامَةُ تَقِيُّ الدِّينِ ابْنُ تَيْمِيَّةَ بِقَلْعَةِ دِمَشْقَ".

البداية والنهاية ط هجر (١٨/ ٢٦٧)

"Al-Birzaliy ya ce: a ranar Litinin, bayan La'asar, 6 ga Sha'aban, aka ɗaure babban Malami Shaikh Imam Taƙiyyuddeen Ibnu Taimiyya, a kurkukun Dimashq".

To wannan ya sa aka samu shakku a kan maganar Ibnu Baɗuɗa, aka ce: tunda tabbas, a ranar da ya iso Dimashq, Ibnu Taimiyya yana cikin kurkuku, to ta yaya har ya gan shi a kan minbari, a ranar Juma'a?!

2) Duk da rashin tabbacin wannan labari, amma masu sukar Ibnu Taimiyya sun riƙe wannan labari na Ibnu Baɗuɗa suna jingina wa Ibnu Taimiyya Aƙidar "Tashbihi" (kamanta siffofin Allah da na halitta), alhali a bisa ƙa'ida ana tabbatar da Aƙidar mutum ne daga littatafansa, ko daga maganganunsa da amintattun maruwaita suka naƙalto daga gare shi, waɗanda ake da tabbacin sun haɗu da mutumin.

To saboda an saba jingina wa Ibnu Taimiyya irin waɗannan tuhumomi marasa tabbaci, sai Ibnu Hajar ya ce:

"فالواجب على من تلبس بالعلم وكان له عقل أن يتأمل كلام الرجل من تصانيفه المشهورة، أو من ألسنة من يوثق به من أهل النقل، فيرد من ذلك ما ينكر، فيحذر منه على قصد النصح".

الشهادة الزكية في ثناء الأئمة على ابن تيمية، مرعي الكرمي (ص: ٧٤)

"Abin da yake wajibi a kan duk wanda ya saka rigar ilimi, kuma yana da hankali, to ya nazarci maganar mutumin (Ibnu Taimiyya) daga littatafansa shahararru, ko daga bakin waɗanda aka aminta da su cikin masu naƙalto magana, sai ya yi raddin mummuna a ciki, kuma ya tsoratar a kansa, da nufin nasiha".

To wannar magana ta Ibnu Hajar, ita za ta kai mu ga nema da lalube cikin littatafan Ibnu Taimiyya, ko za mu samu wannar Aƙida, ta kamanta siffofin Allah da siffofin halitta?

3) Ibnu Taimiyya yana da littafi da ya wallafa, ya yi sharhin Hadisin sauƙowar Allah (شرح حديث النزول), amma duk cikin littafin ba za ka samu magana mai kusa da abin da Ibnu Baɗuɗa ya ba da labari ba.

4) Aƙidar Ibnu Taimiyya da take cikin littatafansa ita ce: ana tabbatar wa Allah siffofinsa na aiki, kamar zuwa, sauƙowa daga sama, ba tare da bayanin "kaifiyya" (kamannin siffar) ba, ba kuma tare da kamanta siffar Allah da ta halitta ba. Ya tabbatar da haka a wurare masu yawa. Daga ciki, yana raddi ga Mu'utazilawa, masu kamanta aiyukan Allah da na mutum sai ya ce:

"وَهُمْ مُشَبِّهَةُ الْأَفْعَالِ يُشَبِّهُونَ الْخَالِقَ بِالْمَخْلُوقِ وَالْمَخْلُوقَ بِالْخَالِقِ فِي الْأَفْعَالِ وَهَذَا قَوْلٌ بَاطِلٌ كَمَا أَنَّ تَمْثِيلَ الْخَالِقِ بِالْمَخْلُوقِ وَالْمَخْلُوقِ بِالْخَالِقِ فِي الصِّفَاتِ بَاطِلٌ. فَالْيَهُودُ وَصَفُوا اللَّهَ بِالنَّقَائِصِ الَّتِي يَتَنَزَّهُ عَنْهَا فَشَبَّهُوهُ بِالْمَخْلُوقِ: كَمَا وَصَفُوهُ بِالْفَقْرِ وَالْبُخْلِ وَاللُّغُوبِ. وَهَذَا بَاطِلٌ؛ فَإِنَّ الرَّبَّ تَعَالَى مُنَزَّهٌ عَنْ كُلِّ نَقْصٍ وَمَوْصُوفٌ بِالْكَمَالِ الَّذِي لَا نَقْصَ فِيهِ وَهُوَ مُنَزَّهٌ فِي صِفَاتِ الْكَمَالِ أَنْ يُمَاثِلَ شَيْءٌ مِنْ صِفَاتِهِ شَيْئًا مِنْ صِفَاتِ الْمَخْلُوقِينَ فَلَيْسَ لَهُ كُفُؤًا أَحَدٌ فِي شَيْءٍ مِنْ صِفَاتِهِ لَا فِي عِلْمِهِ وَلَا قُدْرَتِهِ وَلَا إرَادَتِهِ وَلَا رِضَاهُ وَلَا غَضَبِهِ وَلَا خَلْقِهِ وَلَا اسْتِوَائِهِ وَلَا إتْيَانِهِ وَلَا نُزُولِهِ وَلَا غَيْرِ ذَلِكَ مِمَّا وَصَفَ بِهِ نَفْسَهُ أَوْ وَصَفَهُ بِهِ رَسُولُهُ. بَلْ مَذْهَبُ السَّلَفِ أَنَّهُمْ يَصِفُونَ اللَّهَ بِمَا وَصَفَ بِهِ نَفْسَهُ. وَمَا وَصَفَهُ بِهِ رَسُولُهُ مِنْ غَيْرِ تَحْرِيفٍ وَلَا تَعْطِيلٍ وَمِنْ غَيْرِ تَكْيِيفٍ وَلَا تَمْثِيلٍ. فَلَا يَنْفُونَ عَنْهُ مَا أَثْبَتَهُ لِنَفْسِهِ مِنْ الصِّفَاتِ وَلَا يُمَثِّلُونَ صِفَاتِهِ بِصِفَاتِ الْمَخْلُوقِينَ؛ فَالنَّافِي مُعَطِّلٌ وَالْمُعَطِّلُ يَعْبُدُ عَدَمًا. وَالْمُشَبِّهُ مُمَثِّلٌ وَالْمُمَثِّلُ يَعْبُدُ صَنَمًا. وَمَذْهَبُ السَّلَفِ إثْبَاتٌ بِلَا تَمْثِيلٍ وَتَنْزِيهٌ بِلَا تَعْطِيل".

مجموع الفتاوى (٨/ ٤٣١ - ٤٣٢)

A wannar magana ta Ibnu Taimiyya, za mu ga inda yake raddi ga Mu'utazilawa, har ya kira su da sunan "مُشَبِّهَةُ الْأَفْعَالِ", saboda suna kamanta Allah da halitta a cikin aiyuka.

Kuma sai ya yi musu raddi da cewa; Allah ya tsarkaka da a ce wata siffa tasa tana kama da siffar halitta. Allah ba shi da makamanci, ko madaidaici a cikin dukkan siffofinsa; iliminsa ne, ko ikonsa, ko nufinsa, ko yardarsa, ko fushinsa, ko halittarsa, ko "istiwa'insa" (ɗaukakarsa a kan al-Arshi), ko zuwansa, ko SAUKOWANSA zuwa saman Duniya, ko wata siffar daban...

Kuma ya nuna cewa; Mazhabar Salaf (Magabata) ita ce: suna tabbatar ma Allah dukkan siffar da Allah ya tabbatar ma kansa, ko Manzonsa ya tabbatar masa. Ba sa korewa, ba sa kuma kamanta Allah da halitta. Don mai korewa yana bauta wa babu ne. Mai kamantawa kuma yana bauta wa gunki ne. Mazhabar Salaf, tabbatar da siffofin Allah ne ba tare da kamantawa ba. Da tsarkake Allah ba tare da kore siffofin ba.

To wannan shi ne Aƙidar Ibnu Taimiyya. Ka ga a fili ta rushe labarin Ibnu Baɗuɗa.

* A tattaunawarsa da Ibnu Taimiyya, Prof. Rashid Al-Abdulkareem (مع ابن تيمية... حوارات فكرية) ya hakaito mana amsar da Ibnu Taimiyya zai bayar wa Ibnu Baɗuɗa kamar haka:

Da ya ce masa: Ibnu Baɗuɗa ya ce kanka da motsi.

Sai Ibnu Taimiyya ya ce: "Ai faɗa min wannan kam nomal ne".

Wannan gaskiya ne, ai Annabi (saw) ma, da wasu Annabawan kafinsa, an soke su da hauka. Don haka in dai Annabawa ma ba su tsira ba, har Annabi (saw), waye kuma Ibnu Taimiyya, da har zai tsira?!

Da ya ambata masa batun ya gan shi yana kamanta sauƙowar Allah da sauƙowarsa daga kan minbari, sai Ibnu Taimiyyan ya ce:

"AstagfirulLah, SubhanalLah, Ta'alalLah"!

Sai Ibnu Taimiyyan ya yi uzuri wa Ibnu Baɗuɗa, ya ce:

"Ina ganin wannar magana cushe aka yi masa, ko wani cikin abokan husumata ne ya ƙirƙiri maganar, sai ya ji daga gare shi, amma sai ya yi tadlisi, ya raya cewa; shi da kansa ne ya ganni".

Ma'ana, duk wanda ya san halin Ibnu Taimiyya, zai kyautata zaton lallai uzuri zai yi wa Ibnu Baɗuɗa, ya bar shi da Allah.

~ Dr. Aliyu Muh'd Sani (H) 

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani