𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Aslm Mllm Tambayana shine mene ne ma'anar sunan Maimunat da Kuma Ahyan
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuhu
Sunan Maimuna (ميمونة) yana nufin
mace mai albarka, sa'a, farin ciki, da arziki. Suna ne mai kyau da daraja wanda
ya fito daga harshen Larabci.
A tarihin Musulunci,
akwai MAIMUNA BINT AL-HARITH (RA), ɗaya daga cikin matan Annabi Muhammad
(Sallallahu Alaihi Wasallam) ta ƙarshe. Sunanta na
asali "BARRAH", amma Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya canza
mata shi zuwa Maimuna don yana nufin alheri da albarka.
Sun yi aure a shekara
ta 7 bayan Hijira (bayan Umarar Ramuwa), a wani wuri da ake kira Sarif, da ke
da nisan mil 10 daga Makka.
Ta kasance tana da
matsayi babba a addini, kuma ta ruwaito Hadisai da dama daga Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi Wasallam) musamman akan ibadu da kuma rayuwar gida.
Ta rasu a shekara ta
51 bayan Hijira (ko 61 A.H a wani ruwayar) kuma dan uwanta Abdullah ibn Abbas
(R.A) ne ya jagoranci sallar jana'izarta. An binne ta a garin Sarif inda aka
daura aurenta da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) kamar yadda ta bukata.
Ta kasance mace mai
tsantseni, ilimi, da sadaukarwa. Wannan ya sa sunan ya shahara a tsakanin
Musulmai tun karni na farko.
Ana kallon mai sunan
Maimuna a matsayin mace mai albarka da arziki ga al’umma. Mai taimako, nagarta,
da tausayi. Wacce ke kawo alheri da kwanciyar hankali a cikin rayuwa.
MA'ANAR SUNAN AHYAN:
Sunan AHYAN ko AYAAN
suna ne mai kyau da asali daga Larabci da Musulunci, wanda ake amfani da shi ga
samari (namiji). Sunan na zamani ne kuma ya shahara a kasashen musulmi da dama
saboda kyakykyawar ma'anarsa. Babban ma'anarsa ita ce "Kyautar rayuwa"
(gift of life) ko "kyauta daga Allah" (Gift from God) ko "Cike
da rayuwa". ko "falala da albarka". Haka kuma, kalmar tana nufin
"lokaci," "zamani," ko "tarihi".
Sunan ya samo asali
ne daga kalmar nan ta Larabci HAYY (wato 'Rayayye'). Ana danganta shi da daya
daga cikin kyawawan sunayen Allah, wato AL-HAYY (Madawwamin Mai Rai), wanda ke
ba shi kima da albarka a cikin al'adun musulmi. Wasu na amfani da shi da ma'anar
"Lokuta" (Jam'in kalmar Wa'qti) ko "Zamani" ko
"tarihi." Wannan kalmar tana nan a cikin Alkur'ani mai girma.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.